





























Hadeeth Cards
Da'wa cards that highlight great meanings from the noble prophetic hadiths in a simple style and attractive display that helps the Muslim to have a deeper understanding of his religion in an easy way
All
Daga Amr Dan Shu'aib daga babansa daga kakansa ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "ku umarci 'ya'yanku da yin sallah alhali su suna 'yan shekara bakwai, kuma ku dake su akanta alhali su suna 'yan shekara goma, kuma ku raba tsakaninsu a wurin kwanciya".
Abu Dawud ne Ya Rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa ya wajaba akan uba ya umarci 'ya'yansa - maza da mata - da yin sallah alhali suna da shekara bakwai, kuma ya sanar dasu abinda suke bukata dan tsaida ita. Idan suka kai shekara goma sai ya yi kari akan umarnin, sai ya yi duka akan kasa yin Sallar, kuma ya raba a tsakaninsu a shinfida.
Daga Abdurrahman dan Abu Laila ya ce: Ka'abu dan Ujra ya hadu da ni, sai ya ce: Shin ba na baka wata kyauta ba? Lallai cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya futo wurinmu, sai muka ce: Ya Manzon Allah, hakika mun san ya zamu yi maka sallama, to yaya zamu yi maka salati? Ya ce: "Ku ce: Ya Allah ka yi salati ga (Annabi) Muhammad da alayen (Annabi) Muhammad, kamar yanda Ka yi salati ga (Annabi) Ibrahim da alayen (Annabi) Ibrahim, lallai cewa kai abin yabo ne kuma Mai girma. ya Allah Ka yi albarka ga (Annabi) Muhammad da alayen (Annabi) Muhammad, kamar yadda ka yi albarka ga (Annabi) Ibrahim da alayen (Annabi) Ibrahim, lallai kai abin yabo ne kuma Mai girma".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiSahabbai sun tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - game da siffar salati gare shi? bayan sun san siffar sallama gare shi a Tahiya: "Aminci ya tabbata agareka ya kai wannan Annabi da rahamar Allah da albarkarSa..."? Sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya sanar da su siffar salati gare shi, ma'anarsa: "Ya Allah ka yi salati ga (Annabi) Muhammad da alayen (Annabi) Muhammad" Wato: Ka yi yabo gare shi da ambato mai kyau a cikin jama'a madaukaka, da mabiyansa a cikin AddininSa, da muminai daga makusantansa. "kamar yadda Ka yi salati ga (Annabi) Ibrahim" Kamar yadda ka yi baiwa ga iyalan (Annabi) Ibrahim - aminci ya tabbata agare shi - su ne (Annabi) Ibrahim, da (Annabi) Isma'il, da (Annabi) Ishak, da zuriyarsu da mabiyansu muminai, to ka riskar da falalararKa ga (Annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -. "Lallai kai abin yabo ne kuma Mai girma" Wato: Abin yabo a zatinKa da siffofinKa da ayyukanKa, Mayalwaci a girmanKa da sarautarKa da baiwarKa. "Ya Allah Ka yi albarka ga (Annabi) Muhammad da alayen (Annabi) Muhammad kamar yanda ka yi albarka ga Ibrahim" Wato: Ka ba shi alheri da girmamawa mafi girmasa Ka kara masa Ka tabbatar masa.
Daga Ubadah dan Samit - Allah Ya yarda da shi - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Babu sallah ga wanda bai karanta Fatiha ba".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa sallah ba ta inganta sai da karanta suratul Fatiha, ita rukuni ce daga rukunan sallah a kowace raka'a.
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wanda ya yi wanka irin wankan janaba a ranar Juma`a, sannan ya tafi, kamar ya bayar da sadakar rakuma ne, wanda ya tafi a lokaci na biyu, kamar ya bayar da sadakar saniya ne. wanda ya tafi a lokaci na uku kamar ya bayar da sadakar rago ne mai ƙaho. wanda ya tafi a lokaci na huɗu kamar ya bayar da kaza ne, wanda kuma ya tafi a lokaci na biyar kamar ya bayar da ƙwai ne. Idan liman ya fito Mala`iku za su halarto suna sauraron zikiri (Huɗuba)".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labari game da falalar gaggawar tafiya zuwa sallar Juma'a. Gaggawa tana farawa ne daga bullowar rana zuwa lokacin zuwan liman; shi ne sa'o'i biyar, ana karkasasu kaso biyar gwargwadan lokaci tsakanin bullowar rana har zuwa shigowar liman da hawansa minbari dan huɗuba: Na farko: Wanda ya yi wanka cikakke kamar wankan janaba, sannan ya tafi masallacin Juma'a a lokaci na farko kamar ya yi sadaka da taguwa ne. Na biyu: Wanda ya tafi a lokaci na biyu kamar ya yi sadaka da saniya ne. Na uku; Wanda ya tafi a lokaci na uku kamar ya yi sadaka ne da rago - shi ne namijin tinkiya - mai ƙahuhhuna. Na huɗu: Wanda ya tafi a lokaci na huɗu kamar ya yi sadaka ne da kaza. Na biyar: Wanda ya tafi a lokaci na biyar kamar ya yi sadaka ne da ƙwai. Idan liman ya fito dan huɗuba; sai mala'ikun da suke zaune a ƙofofi dan rubuta masu shiga masallaci na farko da mai biye da shi sai su dakatar da rubutu, sai su zo suna jin zikiri da huɗuba.
Daga Abdullahi ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana cewa: "Wanda zai je Juma'a a cikinku to ya yi wanka".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana ƙarfafa cewa wanda ya yi nufin zuwa sallar Juma'a to an so gareshi ya yi wanka, kamar irin wankansa na janaba.
an karbo daga Abi Huraira Allah ya yarda dashi an daga hadisin zuwa ga Annabi: "wanda ya halarci Gawa har akai mata salla yana da kiradi guda.wanda kuma ya halarce ta har aka binneta yana da kiradi biyu.sai aka ce: menene kiradi biyu? sai yace: kwatankwacin manyan dutsuna biyu" a wata ruwayar kuma: "mafi kankantarsu kwatankwacin dutsen Uhudu"
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiAllah mai madaukakin suna da albarka mai tausasawa ne ga bayinsa, sa`annan yana nufin da ya shimfida musu dalilan yin gafara a garesu, musamman ma lokacin da zasu bar duniya, wadda ta ke ita ce gidan aiki, izuwa gidan da za`a ninke takardun ayyukan su a cikin ta. don hakanan ne ya kwadaitar bisa yin sallar jana`iza da halartar ta, saboda ita sallar neman ceto ne ga mamaci kuma tana kasancewa dalilin samun rahamar Allah. sai ya sanya ladan qiradi ga wanda ya sallace ta, ya kuma sanya wani ladan qiradin ga wanda ya halarci binne ta. wannan wani gwargwado ne daga lada mai girma kuma matsayinsa sananne ne wurin Allah madaukakin saki. yayin da gwargwadon girman wannan lada ya buya ga sahabbai Allah ya kara yarda a gare su- sai Annabi mai tsira da aminci su kara tabbata a gareshi ya kusanto da shi ga kwakwalen su, ta yadda kowane qiradi ya kai girman babban dutse; saboda abinda ke ciki na girma tsayawa akan hakkin dan uwansa musulmi tare da yin addu`ah a gareshi da tunatarwa dangane da makoma da debewa mutanen gidan kewar mamacin su da wanin haka da maslahohi.
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wanda ya yi alwala sai ya kyautata alwala sannan ya zo Juma'a sai ya saurari huduba kuma ya yi shiru za'a gafarta masa abinda ke tsakaninsa da tsakanin Juma'a da ƙarin kwanaki uku, wanda ya taba tsakankwani to haƙiƙa ya yi yashasshiyar magana".
Muslim ne ya rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa wanda ya yi alwala sai ya kyautata alwalarsa da cikawa da zuwa da sunnoninta da ladubbanta, sannan ya zo sallar Juma'a kuma ya yi shiru ya karkata ga mai huɗuba, kuma ya yi shiru daga yashasshiyar magana; za'a gafarta masa ƙananan zunuban kwana goma, daga sallar Juma'a zuwa Juma'a ta biyu da ƙarin kwanuka uku; domin kyakkyawa da kwatankwacinta goma. Sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya gargaɗar daga rashin fuskantar zuciya ga abinda ake faɗa a cikin huɗuba na wa'azuzzuka, da kuma wasa da gabbai na shafar tsakwankwani da waninsu na nau’ukan wasa da shagaltuwa, cewa wanda ya aikata hakan to haƙiƙa ya yi yashasshiyar magana, wanda ya yi yashasshiyar magana to ba shi da rabo a cikin ladan Juma'a cikakkiya.
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: "Wanda ya yi sammako zuwa masallaci ko ya maraita, Allah zai tanadar masa wani masauki a cikin aljanna duk lokacin da ya yi sammako ko ya maraita".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi wa wanda ya zo masallaci dan yin ibada ko ilimi ko wanin hakan daga manufofin alheri a kowanne lokaci albishir; a farkon yini ko ƙarshensa da cewa Allah haƙiƙa ya tanadar masa da wani wuri da garar baƙi a cikin aljanna, duk lokacin da ya zo masallaci a dare ko yini.
Daga Abu Musa al-Ash'ari - yardar Allah ta tabbata a gare shi - ya ce: Manzon Allah - Salati da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Duk wanda ya ratsa wani abu daga cikin masallatanmu ko kasuwanninmu da mai martaba, to ya taba ku, ko kuma ya mallake shi da hannunsa. Cewa ya cutar da wani daga cikin musulmai da wani abu ».
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDuk wanda ya ratsa masallatai, kasuwanni, da wuraren taron musulmai tare da makamin mutunci da sauransu, zai rike shi kuma ya kara riko shi da kyau. Don kar ta shafi wani daga cikin musulmai.