





























Hadeeth Cards
Da'wa cards that highlight great meanings from the noble prophetic hadiths in a simple style and attractive display that helps the Muslim to have a deeper understanding of his religion in an easy way
All
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce : Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Sallar mutum a jama'a tana karuwa akan sallarsa agidansa a kasuwarsa da daraja ashirin da wani abu, hakan cewa dayansu idan ya yi alwala ya kyautata alwalar, sannan ya tafi masallaci babu abinda ya zaburo da shi sai sallah, ba ya nufin komai sai sallah, ba zai yi wani taku ba sai an daukaka darajarsa da shi, an kankare masa kuskurensa da shi, har ya shiga masallaci. Idan ya shiga masallaci ya kasance a cikin sallah muddin dai sallah ce ta tsare shi , Mala'iku suna addu'a ga dayanku muddin dai yana mazauninsa wanda ya yi sallah a cikinsa, suna cewa: Ya Allah ka jikansa, ya Allah ka gafarta masa, ya Allah ka karbi tubansa, muddin dai bai cutar ba a cikinsa, muddin dai bai yi (hadasi) kari ba a cikinsa ba".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa idan musulmi ya yi sallah a cikin jama'a, sallarsa ta kasance tafi sallarsa a gidansa ko kasuwarsa sau ashirin da wani abu. Sannan ya ambaci dalili a hakan: Shi ne cewa mutum idan ya yi alwala sai ya cika alwala ya kyautatata, sannan ya tafi masallaci babu abinda ya fitar da shi sai nufin sallah, ba zai yi wani taku ba sai an daukaka matsayinsa da darajarsa da shi, kuma an shafe masa kuskure da shi, idan ya shiga masallaci ya zauna yana sauraron sallah, to shi yana samun ladan sallah da sakamakonta muddin dai ya jira sallah, Mala'iku suna masa addu'a muddin dai yana mazauninsa wanda ya yi sallah a cikinsa, suna cewa: "Ya Allah Ka gafarta masa, Ya Allah Ka karbi tubansa" muddin dai bai bata alwalarsa ba, ko ya aikata abinda mutane zasu cutu da shi ko Mala'iku ba.
Daga Ibnu Mas'ud - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Jinin mutum musulmi ba ya halatta sai da ɗaya daga cikin abubuwa uku, bazawarin da ya yi zina, da ran (da ya kashe) rai, da wanda ya bar addininsa wanda ya bar jama'a».
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa jinin musulmi haramun ne, sai dai idan ya aikata ɗaya daga cikin ɗabi'un nan uku: Na farko: Wanda ya faɗa cikin alfashar zina, alhali ya riga ya yi aure da ƙulla ingantaccen ɗaurin aure, to sai kashe shi ta hanyar jifa ya halatta. Na biyu: Wanda ya kashe tsararren rai da aka hana kashewa ba tare da wani haƙƙi ba, to sai a kashe shi da sharuɗɗansa. Na uku: Wanda ya fita daga cikin jama'ar muslmai; ko dai ta hanyar barin addininsa gabaɗayansa ta hanyar yin ridda, ko wanda ya bari ba tare da ridda ba ta hanyar barin sashinsa kamar 'yan tawaye, da 'yan fashi, da mayaƙa cikin Khwarij da wasunsu.
Daga Ɗan Abbas - Allah Ya yarda da su - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Da a ce ana bawa mutane abu saboda ikirarin cewa nasu ne, da da yawa daga cikin mutane sun yi da'awar dukiyoyin wasu mutane da jinanansu, sai dai wanda duk ya yi da'awa to shi zai zo da shaidu, kuma rantsuwa tana kan wanda ya musanta".
Baihaki ne Ya Rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa da ace ana bawa mutane saboda kawai mujarradin da'awarsu ba tare da wasu dalilai ba ba kuma tare da wasu alamomi ba to da wasu mutane sun yi da'awar dukiyoyin wasu mutane da jinanensu, sai dai gabatar da shaida da dalili ya wajaba akan mai da'awa da abinda yake nema, idan ba shi da shaidu to sai a gabatar da da'awar akan wanda aka kawo karar, idan ya yi inkarinta to ya wajaba ya yi rantsuwa sai ya kubuta.
A kan A’isha, yardar Allah ta tabbata a gare ta, ta ce: Idan Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya rasa salla daga jin zafi ko wani abu da daddare, zai yi raka’a goma sha biyu da rana.
Muslim ne ya rawaito shiDaga Jabir ɗan Abdullahi - Allah Ya yarda da su - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wanda ya ci tafarnuwa ko albasa, to ya yi nesa damu - ko cewa ya yi: Ya yi nesa da - masallacinmu, ya zauna a gidansa", kuma cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - an zo masa da wata tukunya a cikinta akwai korren abubuwa daga maɓungura ƙasa, sai ya ji wari daga gareta, sai ya yi tambaya sai aka ba shi labarin abinda ke cikinta na maɓungura ƙasa, sai ya ce ku kusantar da ita ga wani daga sahabbaina wanda ke tare da shi, lokacin da ya ganta sai ya ƙyamaci cinta, ya ce: "Ka ci domin cewa ni ina ganawa da wanda ba ka ganawa (da shi)". A riyawayar Muslim daga Jabir ɗan Abdullahi, daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wanda ya ci daga waɗannan maɓungura ƙasan, tafarnuwa - wani lokacin kuma ya ce: Wanda ya ci albasa da tafarnuwa da algarif to kada ya kusanci masallacinmu, domin mala'iku suna cutuwa da abinda 'ya'yan Adam suke cutuwa da shi".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya hana wanda ya ci tafarnuwa ko albasa zuwa masallaci, dan kada ya cutar da 'yan uwansa daga waɗanda suka halarci sallar jam’i da warinsu, shi hanine na tsarkakewa daga zuwa masallaci, ba dan an hana cinsu ba: domin cewa su suna daga abubuwan da aka halatta, haƙiƙa an zo wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da wata tukunya a cikinta akwai korren abubuwa, lokacin da ya shaƙi wari a cikinta kuma aka ba shi labarin abinda ke cikinta sai ya hanu daga cinta ya kuma kusantar da ita ga wani daga sahabbansa dan ya ci daga gareta, sai ya kyamaci ci dan koyi da shi, lokacin da tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya gan shi ya ce: Ka ci; domin cewa ni ina ganawa da Mala’iku idan sun zo da wahayi. kuma Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa mala'iku suna cutuwa daga warin da ake ƙi, kamar yadda mutane suke cutuwa daga gare shi.
Daga Abu Huraira Allah ya yarda da shi daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: "Shin kuna ganin cewa da ace akwai wata korama a kofar dayanku yana wanka a cikinta kowacce rana sau biyar, shin kuna zatan wani abu na dattinsa zai rage ?" Suka ce: Ba abin da zai rage dattinsa, ya ce: "To hakan tamkar salloli biyar ne, Allah Yana shafe kurakurai da su".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kamanta salloli biyar a kowanne yini da dare a kawarwa da kankarewarsu ga kananan zunubai da kurakurai da korama a kofar mutum da yake wanka a cikinta kowacce rana sau biyar, babu wani abu da zai ragu daga dattinsa.
Daga Zaid bin Arqam, yardar Allah ta tabbata a gare shi, ya ce: “Mun kasance muna magana a cikin salla, mutumin ya yi magana da abokinsa, alhali yana gefensa yana salla, har sai na sauko ((kuma in tsaya ga Allah sau biyu)). Don haka aka umurce mu da yin shiru, kuma aka hana mu magana. ”
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiAddu’a mahada ce tsakanin mutum da Ubangijinsa. Bai kamata mai bauta ya shagaltu ba tare da ya yi magana da Allah ba, don haka Zaid bin Arqam, Allah ya yarda da shi, ya ruwaito cewa Musulmai a farkon umarninsu sun yi magana a cikin addu’a gwargwadon yadda suke bukatar magana. Musun su. Kuma tunda sallah ta shagaltu da magana da Allah game da magana da halittu, sai Allah mai girma da daukaka ya umarce su da tsayar da salla kuma ya umarce su da yin shiru kuma ya hana su magana, don haka Allah Madaukakin Sarki ya saukar da cewa: {Kiyaye salla da tsakiyar salla, kuma ku tsayu zuwa ga Allah, shari'arku.} Sahabbai sun san daga gare ta cewa sun hana su yin magana a cikin addu’a, sai suka gama, Allah Ya yarda da su.
A kan hadisin A’isha - Allah Ya yarda da ita - “Rana ta yi bacci a lokacin Manzon Allah - Salatin Allah da amincin Allah su tabbata a gare shi - don haka sai ya aika mai kira yana cewa:“ Sallah rukuni ce, don haka suka taru, kuma ya ci gaba ”.
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiRana ta dushe a lokacin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - don haka sai ya aika mai kira a cikin tituna da kasuwanni yana kiran mutane (Addu'a ita ce Duka) don yin addu'a da rokon Allah - Mai Albarka da Madaukaki - ya gafarta musu da rahama a gare su, kuma ya dawwamar da ni'imominsa na zahiri da na badini. Sun taru a masallacinsa - Allah ya kara masa yarda - ya tafi wurin da zai yi salla tare da su, kuma ya yi musu salla tare da wata addu’ar da ba ta misaltuwa kamar yadda mutane suka saba yi. Ga wata aya ta sararin samaniya wacce bata daga al’ada, batare da iqamah ba, don haka ya yawaita yayi sallah raka’a biyu a sujuda biyu, da raka’ah biyu a sujuda biyu, ma’ana a kowace raka’ah biyu da sujada biyu.
Daga Nana Aisha ya ce: "A kowane dare Annabi yana wutiri ko afarkon dare ko tsakiyarsa, ko karshensa, Kuma yakan tsaida Wutirinsa da Asuba"
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiNana Aisha tana bada labari game da lokacin da Annabi ya kasance yake sallatar Wuturi a cikin Dare, kuma cewa bai takaita a wani lokaci daya ba a kowane lokaci na dare yana yin Wuturi, wani lokacin ma a farkonsa lokacin da zai Sallaci Isha da kuma ya sawwaka bayant, kuma wani lokacin a tsakiyar daren bayan wucewar daya bisa ukunsa na farko, wani lokacin kuma daga karshensa lokacin da biyu bisa ukunsa suka shude, har ya kasance karshen lokacin Dare.