





























Hadeeth Cards
Da'wa cards that highlight great meanings from the noble prophetic hadiths in a simple style and attractive display that helps the Muslim to have a deeper understanding of his religion in an easy way
All
Daga Husayn bn Abd al-Rahman, ya ce: Na kasance tare da Sa'eed bin Jubair sai ya ce: Wanene a cikinku ya ga duniyar da ta share jiya? Na ce: Ni ne, sai na ce: Amma ni ba na cikin sallah, amma an yi min duri, ya ce: Me ka yi? Na ce: Na tashi, ya ce: Me ya sanya ka jure a kan haka? Na ce: Hadisi ne da muka ba da labari ga al-Sha`bi. Na ce: Ka fada mana a kan Buraydah bin Al-Husayb cewa ya ce: “Babu ruqyah sai daga ido ko suruka.” Ya ce: Wanda ya gama ya yi kyau ga abin da ya ji. Annabi yana tare da shi da annabi, kuma tare da shi mutum da mutanen biyu, da annabi kuma babu wani a tare da shi, yayin da aka kawo min bakar fata mai girma, kuma na zaci cewa su al'ummata ne, sai aka ce min: wannan shi ne musa da mutanensa. Sannan ya tashi ya shiga gidansa, kuma mutane suka yi fada a cikin wadancan. Don haka sai suka gaya masa, sannan ya ce: Su ne wadanda ba sa bautar, ba sa buya, kuma su tashi, kuma Ubangijinsu ya dogara gare su, don haka Okasha bin Mohsen ya tashi ya ce: Ina rokon Allah ya sanya ni a cikinsu, sai ya ce: Kai kana cikinsu, sai wani zamani ya tashi ya ce: Ina rokon Allah ya sanya ni daga cikinsu. Okasha sun riga ka. "
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDaga Sahlu ɗan Sa'ad - Allah Ya yarda da shi - lallai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce a ranar Khaibara: "Lallai zan bai wa wani mutum wannan tutar Allah Zai yi buɗi ta hannunsa, yana son Allah da manzaonSa kuma Allah da manzonSa suna son shi". Ya ce: Sai mutane suka kwana suna tattaunawa a daran waye a cikinsu za'a ba shi ita, lokacin da mutane suka wayi gari sai suka yi jijjifi ga manzon Allah - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - kowanne su yana ƙaunar a ba shi ita, sai ya ce: "Ina Aliyu ɗan Abi Dalib?" sai aka ce : Shi ya manzon Allah yana ciwon idanu, ya ce: "Ku aike masa", sai aka zo da shi sai manzon Allah - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - ya yi tofi a cikin (idanuwa) ya yi masa addu'a, sai ya warke kai kace babu wani ciwo a tare da shi, sai ya ba shi tuta, sai (Sayyidina) Aliyu ya ce: Ya manzon Allah, shin zan yake su ne har sai sun zama irinmu? sai ya ce: "Ka zarce a hankali har sai ka sauka a farfajiyarsu, sannan ka kira su zuwa ga musulunci, ka ba su labari da abinda yake wajaba akansu na hakkin Allah a cikinsa, na rantse da Allah, Allah ya shiryar da mutum daya da kai shi ne mafi alheri daga jajayen ni'imomi (rakuma)".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiAnnabi - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - ya bai wa sahabbai labari da samun nasarar musulmai akan Yahudawan Khaibara a wayewar gari, hakan ta hannun wani mutum da zai ba shi tuta ne alamar da runduna take rikewa alama a gare ta. Wannan mutumin daga siffofinsa cewa shi yana son Allah da manzonSa, kuma Allah da manzonSa suna sonsa. Sai sahabbai suka kwana suna tunani suna tattaunawa ga wanda za'a bai wa tutar? dan kwaɗayin wannan matsayi mai girma, Lokacin da gari ya waye sai suka tafi zuwa wurin manzon Allah - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - kowannensu yana kwaɗayin ya rabauta da wannan matsayin, sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya yi tambaya game da Aliyu ɗan Abu Dalib - Allah Ya yarda da shi -? sai aka ce : Lallai ba shi da lafiya, yana fama da ciwon idanunsa. Sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya aika a zo masa da shi, sai ya yi tofi a idon (sayyidina) Aliyu daga yawansu mai daraja, kuma ya yi masa Addu’a, sai ya warke daga cutar kai kace babu wani ciwo a tare da shi, sai ya ba shi tuta, kuma ya umarce shi da zarcewa cikin sauƙi har sai ya yi kusa daga ganuwar maƙiya sai ya bijiro musu da shiga musulunci, idan sun amsa masa; sai ya ba su labari da abinda yake wajaba akansu na farillai. Sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya bayyanawa Aliyu falalar kira zuwa ga Allah, kuma mai Da'awah idan ya zama sababi a cikin shiriyar wani mutum ɗaya to hakan shi ne mafi alheri a gare shi da ya samu jajayen raƙuman da su ne mafi tsadar dukiyoyin Larabawa, sai ya mallakesu ko ya yi sadaka da su.
Daga Zaid ɗan Khalid - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce: "Duk wanda ya shirya mayaki a tafarkin Allah to hakika ya yi yaki, wanda ya maye gurbin wani mayaki a tafarkin Allah (a gidansa) da alheri to hakika ya yi yaki".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa wanda ya tanadarwa wani mayaki a tafarkin Allah sabubban tafiyarsa da abinda yake bukatuwa gare shi daga abinda babu makawa gare shi na makami da abin hawa, da abinci, da ciyarwa da waninsu; to shi yana cikin hukuncin mai yin yaki, kuma ladan mayaki zai same shi . wanda ya jibinci al'amarin mayaki da alheri, kuma ya maye gurbinsa a cikin kula da iyalansa a lokacin da ba ya nan to shi yana cikin hukuncin mayaki yake.
Daga Yahaya dan Umara AlMazinu ya ce: Na halarci Amr dan Abu Hassan ya tambayi Abdullahi dan Zaid game da alwalar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ya ce a kawo masa kwarya ta ruwa, sai ya yi musu alwala irin alwalar Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ya sanya hannunsa akwaryar, sai ya wanke hannayensa sau uku, sannan ya shigar da hannunsa a cikin kwaryar, sai ya kuskure baki ya shaka ruwa ya face, kanfata uku, sannan ya shigar da hannunsa sai ya wanke fuskarsa sau uku, sannan ya wanke hannayensa sau biyu zuwa gwiwar hannu, sannan ya shigar da hannunsa sai ya shafi kansa, sai ya yi gaba da su ya yi baya sau daya, sannan ya wanke kafafuwansa zuwa idan sawu.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiAbdullahi Dan Zaid - Allah Ya yarda da shi - yana bayyana siffar alwalar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi a aikace, sai ya nemi karamar kwarya (buta) ta ruwa, a farko sai ya fara da wanke tafukansa, sannan ya karkatar da kwaryar ya zuba ruwa sai ya wankesu sau uku a wajen kwaryar, sannan ya shigar da hannunsa a cikin kwaryar ya kanfato daga gareta kanfata uku yana kuskurar baki a kowacce kanfata yana shaka ruwa yana facewa, sannan ya kanfato daga kwaryar (butar) sai ya wanke fuskarsa sau uku, sannan ya kanfato daga gareta sai ya wanke hannayensa zuwa gwiwoyin hannaye sau biyu-biyu, sannan ya shigar da hannayensa cikin kwaryar, ya shafi kansa da hannayensa ya fara da magabacin kansa har ya kai zuwa keyarsa saman wuya, sannan ya dawo da su har ya kai gurin da ya fara daga gare shi, sannan ya wanke kafafuwansa tare da idan sawu.
Daga Ibn Shamasa Al-Mahri, ya ce: Omar bin Al-Aas - Allah ya yarda da shi - ya halarci mu yayin da yake cikin mutuwa, sai ya yi kuka mai tsawo, kuma ya juyar da fuskarsa zuwa bango, sai ya sanya dansa ya yi masa salla, don haka ya sanya dansa ya yi masa salla. Shin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya yi bushara? Ya juya ga fuskarsa, ya ce: Mafi alherin alkawari ya shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma Muhammadu Manzon Allah ne, na kasance a kan abinci sau uku: Na gan ni kuma daya daga cikin mafiya tsana daga Manzon Allah, amincin Allah ya tabbata a gare shi daga gare ni, kuma ina son zama na iya Astmkint shi, ya kashe shi, Flo ya kasance a kan wannan lamarin ne daga mutanen Wuta, lokacin da Allah ya yi Musulunci a zuciyata ya zo ga Annabi mai tsira da amincin Allah, sai na ce: mafi sauki hannun dama Vlobaaek, ya miƙa hannayen Vqdt na dama, ya ce: «me ya same ka, ya Amr? Na ce: Ina so in gindaya wani sharadi, sai ya ce: “Kun gindaya menene?” Na ce: Don a gafarta masa, sai ya ce: Shin ba ku sani ba cewa Musulunci yana rusa abin da yake gabaninsa, kuma shige da fice yana rusa abin da yake gabaninsa da gabaninsa? Babu wanda ya fi soyuwa a gare ni kamar Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - kuma babu wani lokaci a idona daga gare shi, kuma ban sami damar cika idanuna da shi ba. Girmama shi, da an ce in bayyana shi, ba zan ba da shi ba; Saboda ban cika idanuna da shi ba, kuma idan na mutu a wannan lamarin, ina fatan kasancewa daya daga cikin 'yan Aljanna, to kuwa zan ga wani abu game da shi? Idan na mutu kada ku dauke ni kuma kada kuyi kukan bakin ciki, idan Dvintamona, wanda yake shimfida kasar Shanna, sannan kuma ya dage game da kabarina kamar yadda mata bayi suka samo asali, kuma suka raba naman, harma Stans dinku, kuma ga abinda na bita ta wurin Lord Russell.
Muslim ne ya rawaito shiDaga Abu Musa Al-Ash'ari - yardar Allah ta tabbata a gare shi - ya ce: (((Na zo wa Annabi - Salatin Allah da amincin Allah su tabbata a gare shi - yayin da yake amfani da abin goge baki), sai ya ce: Karshen sawa yana kan harshensa, sai ya ce: Ya, ka taimaka, kuma tsabtar tana cikin ta, kamar yana cikinta).
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDaga Ammar dan Yasir - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya aikeni wata bukata, sai na samu janaba ban samu ruwa ba, sai na tumurmusa a bigire kamar yadda dabba take tumurmusa , sannan na zo wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai na ambata masa hakan sai ya ce: "Kadai ya isheka ka aikata kamar haka da hannayenka" sannan ya bugi kasa bugu daya da hannayensa, sannan ya shafi hagu akan dama, da bayan tafukansa da kuma fuskarsa.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya aiki Ammar Dan Yasir - Allah Ya yarda da shi - a wata tafiya dan wasu bukatunsa, sai janaba ta same shi ta hanyar jima'i ko zubar maniyyi da sha'awa, bai samu ruwa ba da zai yi wankan (janaba) ba., ya kasance bai san hukuncin taimama dan janaba ba, kadai yana da sanin hukuncinta ne dan karamin kari ne, sai ya yi ijtihadi ya yi zatan cewa kamar yadda zai shafi sashin gabban alwala daga karamin kari da turbayar dake doron kasa, to babu makawa taimama daga janaba ta kasance da game jiki da turbaya; dan kiyasi akan ruwa, sai ya jujjuya a cikin turbaya har ya game jiki ya yi sallah, lokacin da ya zo wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai ya ambata masa hakan; dan ya ga shin akan daidai yake ko a'a? sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana masa siffar tsarkaka daga karamin kari kamar fitsari, da babban kari kamar janaba: Shi ne ya bugi kasa bugu daya da hannayensa, sannan ya shafi hagu akan dama, da bayan tafukansa da kuma fuskarsa.
Daga Jariri Dan Abadullahi - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na yi wa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi caffa - akan shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma Annabi Muhammadu Manzon Allah ne, da tsaida sallah, da bada zakka, da ji da bi, da nasiha ga kowanne musulmi.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiSahabi Jariru Dan Abdullahi - Allah Ya yarda da shi - yana bada labarin cewa shi ya dorawa kansa ya yi wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - alkawari akan tauhidi, da yin salloli biyar a yini da dare, da sharuddansu da rukunansu da wajibansu da sunnoninsu, da kuma bada zakka ta dole, ita ce ibada ta dukiya wajiba, ana karba daga mawadata ana bada ita ga macancanta daga talakawa da wasunsu, da kuma biyayya ga shugabanni, da nasiha ga kowanne musulmi, hakan ta hanyar kwadayi akan amfanar da shi, da sadar da alheri gare shi, da tunkude sharri daga gare shi ta hanyar magana da aikatawa.
Daga Mu'az Bin Jabal -Allah Ya yarda da shi -: Cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya riƙe hannuna, sai ya ce: "Ya Mu'az, wallahi lallai ni ina sonka", sai ya ce: "Ina yi maka wasicci ya Mu'az bayan kowace sallah kada ka bar faɗin: Ya Allah Ka taimakeni akan ambatanKa da gode maKa da kyakkyawar ibadarKa".
Abu Dawud da Nasa'i haka Ahmad suka ruwaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya riƙe hannun Mu'aza - Allah Ya yarda da shi -, sai ya ce masa: Wallahi lallai ni ina sonka, kuma ina yi maka wasicci ya Mu'az a ƙarshen kowace sallah kada kabar faɗin: (Ya Allah Ka taimakeni akan ambatanKa) a kowace magana da aikin da zai kusanto da ni zuwa biyayya, (da godiyarKa) ta hanyar samun ni'imomi da tunkuɗe masifu, (da kyakkyawar bautarKa) ta hanyar yin ikhlasi ga Allah da bin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.