Hadeeth Cards
Da'wa cards that highlight great meanings from the noble prophetic hadiths in a simple style and attractive display that helps the Muslim to have a deeper understanding of his religion in an easy way






























Da'wa cards that highlight great meanings from the noble prophetic hadiths in a simple style and attractive display that helps the Muslim to have a deeper understanding of his religion in an easy way
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa wanda ya nemi shahada da mutuwa a tafarkin Allah, kuma ya kasance mai gaskiya mai tsarkake niyyarsa ga Allah - Mai girma da ɗaukaka -, Allah Zai ba shi darajojin shahidai saboda niyyarsa ta gaskiya koda ya mutu akan shinfiɗa ba a yaki ba.
Dakin Ka'aba yana da daraja da daukaka,kuma shi wata alama ce ta bautar Allah da kankan da kai da tsoron Allah,kuma yana da kwarjini a zukatan mutane,rayuka sun damfaru da shi,suna son shi.Don haka Annabi ya umarci mahajjaci daya sanya dawafi ga dakin Allah abu na karshe,ya zama ban kwana,sai dai anyi sauki ga mace mai haila don gudun kar ta bata masallacin.wannan kuma ya shafi Hajji ne kawai banda Umra.Duba littafin Taisiril Allam,Tanbihul Afham,Ta'asisil Ahkam.
Uwar muminai Nana Maimuna - Allah Ya yarda da ita - ta bada labari game da siffar wankan annabi - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - na tsarki, lokacin da ta ajiye masa ruwa dan ya yi wanka da shi, kuma ta kare shi da labule, sai annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya aikata abinda ke tafe: N farko: Ya zuba ruwa a hannayensa sai ya wanke su kafin ya shigar da su cikin abin wanka. Na biyu: Ya zuba ruwa da hannunsa na dama akan hannunsa na hagu sai ya wanke gabansa; dan tsarkake shi daga abinda ya maƙale na alamar janaba. Na uku: Ya bugi ƙasa da hannunsa sai ya shafe shi sannan ya wanke shi dan ya gusar da ƙazanta daga gare shi. Na huɗu: Ya kurkure baki; ta hanyar shigar da ruwa a cikin bakinsa ya motsa shi ya kuma kurkure shi sannan ya zubar da shi, sai ya shaƙi ruwa; ta hanyar da ya shigar da ruwa a cikin hancinsa da nunfashinsa, sannan ya fitar da shi dan ya tsarkake shi. Na biyar: Ya wanke fuskarsa da zira'insa biyu. Na shida: Ya zuba ruwa a kansa. Na bakwai: Ya zuba ruwa a sauran jikinsa. Na takwas: Ya juya daga gurinsa sai ya wanke diga-digansa a wani wurin daban ta inda bai wankesu ba kafin nan. Sannan ta kawo masa wani mayafi dan ya tsane da shi, bai karɓa ba, sai ya fara shafe ruwan jikinsa da hannunsa yana karkaɗe shi.
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan ya yi nufin wankan janaba sai ya fara wanke hannayensa, sannna ya yi alwala kamar yadda yake alwalar sallah, sannan ya zuba ruwa a jikinsa, sannan ya tsattsefe gashin kansa da hannayensa, har sai ya tabbar cewa ruwa yakai tushen gashin, ya jika fatar, sai ya zuba ruwa akansa sau uku sannan ya wanke ragowar jijkinsa. Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - ta ce : Na kasance ina wanka ni da Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a kwarya daya, muna kanfatowa daga gareta gaba daya.
Aliyu Dan Abu Dalib - Allah Ya yarda da shi - ya bada labarin cewa ya kasance da yawan maziyyi yana fita daga gare shi - shi wani ruwa ne fari siriri mai zuba yana fita daga gaba a yayin sha'awa ko kafin jima'ai -. Bai san me zai aikata ba idan ya fita ba, sai ya ji kunyar ya tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -; domin cewa shi mijin Fadimatu ne 'yar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, Sai ya bukaci Mikdad Dan Aswad ya tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - game da hakan, sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya amsa masa da ya wanke gabansa sannan ya yi alwala.
Hadisin Abu Hurairah - yardar Allah ta tabbata a gare shi - ya tabbatar da batun mustahabbancin lokaci a cikin lamuran girmamawa, kuma an danganta shi ne cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Idan kun sa," wato kuna son sawa kuma "idan kun yi alwala," ma'ana kuna son ayyukansa. "Don haka ku fara da rantsuwarku." Jam'in Ayman, wanda yake daban da hagu, don haka gefen dama ya shiga zuwa rigar, kafin hagu, kuma ya gabatar da gefen hannayensa da ƙafafunsa na dama a cikin alwala.Sannan kuma na san cewa a cikin membobin alwala akwai wani abu da ba a marmarin itacen oak, wanda shine kunnuwa, hannu da kumatu, amma yana tsarkake ɗaya lokaci ɗaya. Idan kuwa hakan ba zai yiwu ba, kamar yadda yake a yankan yanke da makamantansu, ana yin rantsuwa.
An tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: Wanne aiki ne mafi soyuwa agurin Allah? Sai ya ce: Sallar farilla a lokukacinta wanda mai shari'a ya iyakance shi, sannan biyayya ga mahaifa, da kyautata musu, da tsayuwa da hakkinsu, da barin saba musu, sannan yaki a tafarkin Allah, dan daukaka kalmar Allah - Mai girma da daukaka -, da kare addinin Allah ma'abotansa, da bayyanar da alamominsa, hakan yana kasancewa ne da rai da dukiya. Dan Mas'ud - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Ya bani labarin wadanan ayyukan; da na ce masa: Sannan wanne? da ya karamin.
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa a kowane yinin da rana zata ɓullo a cikinsa akwai wasu mala'ilku biyu zasu sauka suna masu kira, ɗayansu yana cewa: Ya Allah Ka baiwa mai ciyarwa a ayyukan ɗa'a da iyalai da baƙi da abubuwan alheri mayewa Ka canja masa mafi alheri a cikin abinda ya ciyar, kuma Ka yi masa albarka. Ɗayan kuma yana cewa: Ya Allah Ka bawa mai riƙewa (mai rowa) ɓaci ka halakar da dukiyarsa wacce ya hanata ga waɗanda suka cancanceta.