Hadeeth Cards
Da'wa cards that highlight great meanings from the noble prophetic hadiths in a simple style and attractive display that helps the Muslim to have a deeper understanding of his religion in an easy way






























Da'wa cards that highlight great meanings from the noble prophetic hadiths in a simple style and attractive display that helps the Muslim to have a deeper understanding of his religion in an easy way
Annabi tsira da amincin Allah yana tsoratar da al'umma game da yin wasa da lamarin alwala da kuma gaza yin ta cikakkiya, ya kuma kwadaitar da a irika yinta cikakkiya, kasncewar an fi samun lam'a a duga - dugai, ruwa baya mamaye su sosai, wanda hakan ka iya jawo matsala ga tsarki da salla, sai Annabi ya bamu labarin azaba mai tsanani ga duga - dugai da kuma mai duga- dugan mai yin wasa da alwala
Annabi ya jinkirta fitowa zuwa ga sallar issha'i har dare yayi ,mata da yara sun kwanta bacci,wanda basu da jumurin jira mai tsawo,sai Umar Dan Khaddab ya zo wajensa yace: sallah,mata da yara sun yi bacci. sai Manzo tsira da aminci ya fito daga gidansa zuwa masallaci kansa yana digar da ruwan wanka yana bayyana cewa mafi kyawun liokacin sallar issha'i shine a jinkirta ta.ba don gudun wahalar jiran lokacin ba:ba don kan in matsawa al'umma ta ba da na umarce su da wannan sallar a irin wannan lokacin
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa Allah - Maɗaukakin sarki - Yana faɗa a cikin Hadisi Ƙudsi: Dukkan aikin Ɗan Adam ana ninka kyakkyawa da kwatankwacinsa goma zuwa ninki ɗari bakwai, sai azimi; shi nawa ne riya ba ta shiga cikinsa, kuma nine zan yi sakayya da shi, sai in kaɗaita da sanin gwargwadan ladansa da kuma ninka kyawawan (ladansa). Sannan Ya ce: (Azimi garkuwa ne) kuma kariya ne kuma sitira ne kuma katanga ne mai katangewa daga wuta; domin cewa shi kamewa ne daga sha'awowi da afkawa cikin zunubai, wuta kuma abar kewayewa ce da sha'awowi. (Idan yinin azimin ɗayanku ya kasance to kada ya yi kwarkwasa) da yin jima'i da abubuwan gabatarwarsa, ko mummunan zance kai tsaye. (Kada ya yi zancen banza) da yin husuma da kuma kururuwa. (Idan wani ya zage shi ko ya yi faɗa da shi) a cikin Ramadan to ya ce: Lallai ni mai azimi ne; wataƙila ya ƙyale shi, idan ya nace sai dai faɗa to a haƙiƙa to sai ya tunkuɗe shi da mafi sauƙi, sai mafi sauƙi kamar wanda ya shigo maka gida. Sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya yi rantsuwa da wanda ransa yake a hannunSa cewa canzawar bashin bakin mai azimi saboda azimin ya fi daɗi a wurin Allah ranar alƙiyama daga ƙanshin almiski a wurinku, kuma ya fi yawan lada daga almiski abin so gare shi a ranakun juma'a da kuma majalisan zikiri. Mai azimi yana da farin ciki biyu da zai yi farin ciki da su: Idan zai yi buɗa baki zai yi farin ciki da gushewar yunwarsa da kuma ƙishirwarsa saboda yadda aka halatta masa buda baki. Kuma zai yi farin ciki da cikar aziminsa da kuma kammala bautarsa, da kuma sauƙi daga Ubangijinsa, da taimako akan aziminsa na gaba. (Idan ya gamu da Ubangijinsa zai yi farin ciki da aziminsa) da sakamakonsa da kuma ladansa.
Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Na kasance ina barci a gefen Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai na rasashi da daddare, sai na laluba da hannayena gurin da ya kasance yake sallah a cikinsa a cikin ɗaki; sai gashi yana sujjada alhali diga-digansa suna a tsaye, sai gashi shi yana cewa: (Ina neman tsari) ina kamun ƙafa (da yardarKa daga fushinKa) akaina ko akan al'ummata, (kuma) ina neman tsari (da rangwaminKa) afuwarKa mai yawa (daga uƙubarKa), (Ina neman tsari daga gareKa) da siffofin kyawunKa daga siffofin ɗaukakarKa, inda ba mai fakewa daga gare Ka sai Kai, babu matserata kuma babu mafaka daga Allah sai dai zuwa gareShi, (Ba zan iya ƙididdige yabo a gareKa ba) ba zan iya kuma bazan kai ƙololuwa a lissafewa ba da kuma ƙirgawa ba saboda gajiyawata ba, ƙididdige ni'imarKa da kyautatawarKa kamar yadda Kake cancantarsa ba koda na yi ƙoƙari a hakan. (Kai kamar yadda Ka yabi kanKa) Kaine wanda Ka yi yabo akan zatinKa yabon da ya dace da Kai, waye yake da iko akan bada haƙƙin yabonKa?!
Ya kasance daga shiriyar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - shi ne yana farawa da asuwaki idan ya shiga gidansa a kowane lokaci da daddare ko da rana.
An anbaci wani mutumin da ya yi bacci har gari ya waye rana ta ɓullo bai tashi ya yi sallar farilla ba a wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Lallai shi wani mutum ne wanda Shaiɗan ya yi fitsari a cikin kunnansa.
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin halin Shaiɗan da kuma yakinsa ga mutumin da yake nufin tsayuwa dan sallar dare ko Asuba. domin mumini idan ya tafi yin bacci shaiɗan yana ƙulli uku akan ƙyaraysa - yana nufin: Ƙarshen kansa -. Idan mumini ya farka kuma ya ambaci Allah - Maɗaukakin sarki - bai amsa waswasin shaiɗan ba; sai ƙulli (ɗaya) ya warware. Idan ya yi alwala sai ya warware. Idan ya tashi ya yi sallah sai ƙulli na uku ya warware, sai ya wayi gari mai yawan nishaɗi mai daɗin rai; dan farin cikinsa da abinda Allah Ya datar da shi na aikin ɗa'a, yana mai bushara da abinda Allah Ya yi masa alƙawari na lada da gafara, tare da abinda ya gushe daga gare shi na ƙulle-ƙullen Shaiɗan da nauyayawarsa, in ba haka ba zai wayi gari mai mummunan rai, mai baƙin ciki a zuciya, mai kasala daga ayyukan alheri da biyayya; domin cewa shi abin ɗaurewa ne da marin Shaiɗan, kuma abin nisanta daga kusancin Al-Rahman.