





























Hadeeth Cards
Da'wa cards that highlight great meanings from the noble prophetic hadiths in a simple style and attractive display that helps the Muslim to have a deeper understanding of his religion in an easy way
All
An rawaito daga Salman Al-farisi -Allah ya yarda da shi- daga Manzon Allah: "Kwanan dakon Rana da yini yafi Al-khairi daga Azumin wata da kuma tsayuwar Sallarsa, kuma idan Mutum ya Mutu (yanayi) za'a rika rubuta masa lada kamar yana yi, kuma ana bashi Arzikinsa, kuma za'a tsareshi ga barin fitina"
Muslim ne ya rawaito shiGadin Wuni da dare saboda Allah don kare Musulmai, yafi Al-khairi kan azumin wata, da tsayuwar darensa, kuma idan Mai Jahadi ya Mutu aikin ladansa yana wanzuwa yana ci gaba baya yankwa, kuma za’a rika bashi Arzikin Al-janna, saboda yana raye a wajen Ubangijinsa a Al-janna, kuma yana samun Karama ta yadda Mala’iku biyu basa su masa ba don tamabaya (a Kabari) kuma wancananka saboda ya Mutu ne yana mai dakon kare Addinin Allah Madaukakin Sarki, tare da sanin cewa Mai zaman dako a tafarkin Allah; saboda shi ya lazamci wuraren Iyakoki don kariyar ga Musulmai daga Kafirai
Daga Dan Abbas - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce wa wata mata daga mutanen Madina, Ibnu Abbas ya ambaceta sai na manta sunanta: "Meya hanaki ki yi Hajji tare da mu?" Ta ce: Ba mu da komai sai raƙuma biyu, sai baban ɗanta da ɗanta suka yi Hajji akan raƙumi ɗaya, kuma ya bar mana ɗayan muna ban ruwa da shi, ya ce: "Idan Ramadan ya zo to ki yi umara, domin umara a cikinsa yana daidai da Hajji".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiLokacin da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya dawo daga Hajjin ban kwana, sai ya cewa wata mata daga mutanen Madina wacce bata yi Hajji ba: Me yahanaki yin Hajji tare da mu? Sai ta kawo hanzarin cewa suna da raƙuma biyu ne, sai mijinta da ɗanta suka yi Hajji akan ɗayan su, kuma ya bar ɗayan dan su yi ban ruwa da shi daga rijiya. Sai Annabi - tsira da aminci su tabbata agare shi - ya bata labarin cewa yin Umura a watan Ramadan ladansa ya yi daidai da ladan Hajji.
Ukkaz da Mijna da Thul-Majaz a lokacin Jahil;iyya Kasuwanni ne sai kuke ganin laifi ne kuyi kasuwanci a cikinsu lokacin aikin Hajji, Sai Allah ya saukar da: Babu laifi akan ku ku nemi Falala daga Ubangijinku" Bakara:198 a cikin lokacin Hajji...
Al-Tirmithi Ya Rawaito shi - Abu Daud Ya Rawaito shi - Ahmad ne ya rawaito shiKowane Mamaci ladan aikinsa yana tsayawa da Mutuwarsa, ba’a rubuta masa komai sabo, sai mai aman dako a tafarkin Allah,shi ne wanda yakr gadin Iyakokin Musulmai saboda Allah saboda haka Allah ya Aurtashi da wanzuwar ladan aikinsa, kuma za’a amuntar das hi daga fitinar Kabari kuma Mala’iku biyu ba asu tambayar shi ba
Daga Nana Aisha Uwar Muminai - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Ya manzon Allah, muna ganin yaƙi shi ne mafificin aiki, shin ba ma yi yaƙi ba? ya ce: "A'a, sai dai mafificin yaƙi: Shi ne kubutaccen aikin Hajji".
Bukhari ne ya rawaito shiSahabbai - Allah Ya yarda da su - sun kasance suna ganin yaƙi a tafarkin Allah da yakar maƙiya yana daga mafifitan ayyuka, sai Nana A'isah - Allah Ya yarda da ita - ta tambayi annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - cewa zasu iya yin yaƙi? Sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya nuna musu mafificin yaƙi a cikin haƙƙinsu shi ne kubutaccen aikin Hajji wanda ya dace da AlKur'ani da Sunnah, wanda ya kubuta daga zunubi da kuma riya.
An rawaito daga Abu Huraira –Allah ya yarda das hi- y ace: “Anzowa da wani mutum daga cikin Musulmai ga Mazon Allah –tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- a cikin Masallaci sai ya kirawo shi: Ya Manzon Allah, ni nayi Zina, sai yak au da kai ga barinsa, sai yasake zagayowa ta daya fuskarsa sai y yace: ya mazon Allah ni nayi Zina sai yak au da kai, har ya maimaita masa sau Hudu, yayin da yayi wa kansa da kansa shaida har sau hudu sai Annabi ya kirawo shi sai y ace das hi: ko kana da hauka nr? Ya ce: aa sai y ace ko ka taba Aure? Sai ya ce: E sai Manon SAW y ace: ku tafi das hi ku jefe shi sai Ibn Shihab y ace: Abu Salama Bn abdul-Rahman ya bani labara cewa yaji Jabiri Bn Abdullahi yana cewa: “Na kasance cikin wadan ga muka
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiMa’iz Bn Malik Al-aslami –Allah ya yarda das hi ya zo wajen Manon Allah SAW yana cikin Masallaci, sai ya kirawo shi, kuma yayi ikirari akansa cewa yayi ina, sai Annabi ya kawar mada da kai ko zai dawo ya tuba a tsakaninsa da Allah, sai dai yazo cikin yana mai fuda kansafushi da kansa, yana mai yankewa cewa tsarkake shi kawai ayi masa Haddi, sai ya fyskance shit a wajen fuskarsa har wa lau, sai yayi Ikirarin Zina akansa kuma dai, sai Annabi SAW ya kawar da kai har said a yayi Shaida akansa da Zina sau Hudu, sannan ne ya tambaye shi: shi ko yana da hauka ne? y ace a’a kuma ya tambayi ‘Yan Uwansa ko yana da Aure ? kuma ya tambayeshi ko yayi abunda ba sai anyi masa Haddi ba, na tabawa ko kuma sunbanta, sai ya bayyana da zina karara, yayin da Annabi ya tabbatar daga dukkan wadan can, kuma ya tabbatar cewa Haddi ya kama shi, sai ya Umarci sahabbansa das u tafi da shi sai suka jefe shi, sai suka futo das hi zuwa Baki’a Al-garkad –Kuma shi ne wurin Sallar Jana’iza- sai suka jefe shi, yayin day a fara jin afin Duwastu sai ya nemi ya gudu daga Mutuwa, saboda Ran Dan Adam baya iya jure hakan, sai ya gudu, sai suka kamo shi a Harra, sai suka yi Masa rubdugu har ya Mutu –Allah yayi masa rahama kuma ya yarda das hi
Daga ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Idan Allah Ya tara mutanen farko da na ƙarshe ranar alƙiyama za'a ɗaga tuta ta dukkan wani mayaufdari, sai a ce: Wannan yaudarar wane ɗan wane ce".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa Allah - Maɗaukakin sarki - idan ya tara mutanen farko dana ƙarshe ranar alƙiyama saboda hisabi, za'a kafawa kowanne maha'incin da bai cika alƙawarin da ya dauka ba tare da Allah ko tare da mutane ba, wata alamar da za'a kunya shi da ita akan ha'incinsa, kuma za’a yi kira akan sa a wannan ranar: Wannan ha'incin wane ɗan wane ne; dan bayyanar da mummunan aikinsa a filin taron alƙiyama.
Daga Abdullahi Dan Abbas -Allah ya yarda da shi- yace: Sa'ad Dan Ubada ya yi wa Manzon Allah fatawa game da alwashi da mahaifiyarsa tayi, wanda har ta mutu bata cika shi ba?, sai Manzon Allah -tsira da amincin Allah- yace: sai ka yi mata
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiUmmu Saad ta rasu bata cika wani alwashi da ke kanta ba, sai Annabi tsira da amincin Allah ya umarci Danta da ya yii mata
An rawaito daga Salamah Bn Al-akwa’a –Allah ya yarda da shi- “wani dan leken Asiri daga cikin Mushirikai Annabi -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi-, kuma yana cikin tafiya, sai ya zauna a wajan Sahabbansa ina zantawa das u, sannan sai ya bace, sai Annabi SAW y ace ku nemo shi ku kasha shi, sai na kasha shi, sai ya bani ganimar Kayansa” a cikin wata riwayar kuma sai y ace: waye ya kasha Mutumin ? sai suka ce: Ibn Al-akwa’a, sai y ace: yana ganimar kayansa baki daya”
Muslim ne ya rawaito shi - Bukhari da Muslim suka Rawaito shiWannan Hadisin ya na cikin bayani ne kan hukuncin Musulunci ga wanda yake liken Asiri cikin Musulmai daga cikin Kafirai; saboda Salama Bn Al-akwa’a ya bada labarin cewa: “Wani Dan liken Asiri ya zo wa Manzon Allah SAW daga cikin Mushirikai” ankirawo shi da idon Masu liken Asiri; saboda aikinsa da ido yake yi, kuma shi shi halin Manzon Allah SAW a cikin tafiyarsa sai Dan liken Asiri ya zauna a wajen Sahabbansa yana Magana, sai ya bace sai Manzon Allah y ace ku kasha shi sai aka kasha shi, sai na kasha shi, sai ya bani rabon ganimar da ake bayarwa rabon ganima, kuma a kara Masa akan rabonsa, “Ganimarsa” ai abunda ya kasance akansa na lada da kuma Takobi da aka ambace shi das hi, saboda zai rabashi das hi, kuma zai shiga cikin Ganima: dukkan abunda yake kai na Sirdi da kuma kaya, kuma da abunda yake tare da shi na Dabba da kuma Dukiya, kuma da abun yake daure das hi na Zinare da Azurfa.
Daga Bara’u ɗan Azib -Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya umarce mu da abubuwa guda bakawai, kuma ya hanemu da abubuwa bakwai: Ya umarcemu da duba mara lafiya, da raka jana’iza, da gaida mai atishawa, da kuma kuɓutar da rantsuwa, ko mai rantsuwa, da taimakon wanda aka zalunta, da kuma amsawa mai gayyata, da yaɗa sallama. Ya kuma hana mu yin zobe - ko sanya zoben zinare, da sha acikin abin sha na azurfa, da al-Mayathir, (Shi ne matakalar abunda ake sanyawa a shinfidar doki) da al-ƙissi (zabon Masar, nau’i ne na alhariri mai kauri) da kuma sanya alharini, da al-Istabraƙ (Alharini mai kauri) Dibaj (shi ma nau’i ne na alharini mai kauri).
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya umarci musulmai da ɗabi'u bakwai kuma ya hanesu ɗabi'u bakwai; waɗanda ya umarce su sune: Na farkonsu: Ziyarar mara lafiya. Na biyunsu: Raka jana'iza da tarayya ta hanyar yi mata sallah da kuma binneta, da yi mata addu'a. Na ukunsu: Yin addu'a ga wanda ya yi atishawa kuma ya godewa Allah, shi ne ace masa: Allah Ya yi maka rahama. Na huɗunsu: Kuɓutar da mai rantsuwa da kuma gasgata shi, ma'ana cewa da zai yi rantsuwa akan wani al'amari alhali kai kana da iko akan sanya shi kuɓutacce a cikinta to ka aikata; dan kada ka bar shi zuwa yin kaffara ta rantsuwar. Na biyarɗinsu: Taimakon wanda aka zalinta, ta hanyar taimaka masa da tunkuɗe abinda yake afka masa daga azzalimi gwargwadan iko. Na shidansu: Amsa gayyata zuwa walimar abin ci, kamar walimar angwanci, ko suna, ko waninsu. Na bakwansu: Yin sallama da yaɗata da kuma amsata. Waɗanda kuma ya hanasu su ne: Na farkonsu: Sanya zobunan zinare da kuma yin ado da su. Na biyunsu: Shan abu a ƙwaryar azirfa. Na ukunsu: Zama akan Mayasir, sune shimfiɗun da ake sawa akan sirdin doki da kuma sirdin raƙumi na alharaini. Na huɗunsu: Sanya tufafin da aka yi da kattanin da aka cakuɗa da alharini kuma ana ambatansa: (Alƙisiyyu). Na biyarɗinsu: Sanya alharaini. Na shidansu: Sanya Istabraƙ, shi ne: Alharini mai kauri. Na bakwansu: Sanya Dibaj, shi ne: Mafi kyan nau'ikan alharini kuma mafi tsadarsu.