Hadeeth Cards
Da'wa cards that highlight great meanings from the noble prophetic hadiths in a simple style and attractive display that helps the Muslim to have a deeper understanding of his religion in an easy way






























Da'wa cards that highlight great meanings from the noble prophetic hadiths in a simple style and attractive display that helps the Muslim to have a deeper understanding of his religion in an easy way
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kwaɗaitar da wanda yake da iko akan jima'i da ɗawainiyar aure da ya yi aure; domin cewa shi yafi kiyaye gani daga haram, kuma ya fi tsananin katange farjinsa, da kuma hana afkawa cikin alfasha, wanda ba zai iya ɗaukar ɗawainiyar aure ba alhali shi yana mai iko akan jima'i to ya yin azimi domin cewa shi yana yanke sha'awar farji da sharrin maniyyi.
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya tsoratar daga cakuɗuwa da mata ajanibai (waɗanda ba muharramai ba), ya ce: Ku kiyaye kawunanku da ku shiga gurin mata, mata kuma su shiga gurinku. Sai wani mutum daga mutanen Madina ya ce: Shin kana ganin makusantan miji fa; kamar ɗan uwan miji da ɗan ɗan uwansa, da baffansa da ɗan baffansa, da ɗan 'yar uwarsa, da makamancinsu daga waɗanda aure da su yake halatta gare shi da a ce ba mai aure ba ce? Sai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Ku kiyaye shi kamar yadda kuke kiyayar mutuwa! domin kaɗaitaka da 'yan uwan miji mai kaiwa ne zuwa ga fitina da halaka a cikin Addini, makusantan miji banda iyayensa da 'ya'yansa sune mafi cancanta da hani cikin ajnabi; domin kaɗaitaka da makusancin miji tafi yawa daga kaɗaitaka da waninsa, kuma sharri ana tinanin afkuwarsa ne daga gare shi sama da waninsa ba tare da wani inakri akansa ba, kuma domin cewa shi babu makawa daga gare shi , kuma tsare shi ba ya yiwuwa daga gareta, yayin da al'ada ta gudana da sassauci a cikinsa sai namiji ya keɓanta da matar dan uwansa; to shi yana kama da mutuwa a muni da barna, sabanin namiji ajnabi cewa shi ana kulawa daga gare shi.
Tabi'i Malik ɗan Aus yana bada labari cewa shi ya kasance a wurinsa akwai zinarai, kuma yana son ya canja su da azirfofi, sai Ɗalha ɗan Ubaidullahi - Allah Ya yarda da shi - ya ce masa: Ka bamu zinarenka dan na gansu! sannan ya ce da shi bayan ya yanke zai saya: Ka je Ka dawo, idan ɗan aikinmu ya zo bayannan dan mu baka dirhamomin, Umar ɗan Khaɗɗab - Allah Ya yarda da shi - ya kasance yana halarce a wurin, sai ya yi inkarin wannan nau'in na mu'amala, kuma ya yi wa Ɗalha rantsuwa akan cewa ya bada azirfar a take, ko ya dawo masa da zinarensa wanda ya karba daga gare shi, kuma ya bayyana masa sababin hakan cewa Manzon Allah - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - ya ambaci cewa saida zinari da azirfa ko akasin hakan ya wajaba ya zama hannu da hannu nan take, inba haka bafa to wannan cinikin zai zama riba abin haramtawa, kuma bataccen ciniki, ba'a saida zinari da azirfa ko azirfa da zinari sai hanuu da hannu kuma karba ya tabbata, haka ba'a saida alkama da alkama ko wake da wake ko sha'ir da sha'ir ko dabino da dabino sai daidai wa daidaida awo da awo,
Shari'a tana kwadayin kautar da duk abinda zai jawo gaba ko kiyayya a tsakanin "ya'yan Musulmi, kuma wannan yana bayyane ta hanyar wannan Nassi kamar haka: Annabi ya hana kari akan kudin haja ba tare da niyyar saye ba, don kawai amfanin mai siyarwa ta hanyar kara kudin, ko don cutar da Mai saye da sanya kayan yayi tsada kuma an hana hakan, sabida abinda yake janyowa na karya da kuma rudi da mai saye, da kuma daga Darajar kayan ta hanyar Makirci da yaudara. kuma ya hana Mutumin Birni ya siyarwa da Mutumin kauye kayansa a kasuwa, don shi yasan kudin kayan; ta hanayar haka ya toshe duk kafar da Masu saye zasu ci riba, kuma Annabi yana cewa : "ku bar Mutane sashinsu su Azurta da sashi" kuma idan mai ita ya siyar da kansato mai saye zai samu wani rangwamen da shi ma zai ci riba, don haka aka hana Mutumin Birni ya yiwa mutumin kauye don akwai takurawa ga Mutanen birni, kuma harmta neman Aure akan neman Auren Dan uwansa, har sai yasan cewa Mai neman farko ya fita ko an hana sh, ko ba'a amsa masa ba don sabida neman Aure kan neman Aure abunda yake jawowa na gaba da kuma kiyayya, da kuma jefa kai ga Abinda zai hana Arziki, da kuma hanin Mace kan ta nemi Miji ya saki kishiyarta ko ta cusa masa kinta, ko kuma rigima a tsakaninsu, don ta sanya sharri a tsakaninsu, har yakai sun rabu, to wannan Haram ne, sabida abinda yake cikin ta na Barna mai girma, na gadar da gaba, da janyo fitintunu, da kuma yanke Arzikin wacce aka saka, wanda ya suturtashi da fadin abinda yake cikin kwaryarta na Alkairi wanda Aure ne yake jawo shi, kuma yake wajabta shi akan miji na ciyarwa da kuma tufatarwa, da sauran hakkokin Aure.
Wani ciwo ya kama Uman ɗan Abul Aas - Allah Ya yarda da shi - ya kusa ya halakar da shi, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya zo l ya duba shi, kuma ya sanar da shi wata addu'ar da Allah zai ɗauke masa abinda ya saukar masa na rashin lafiyar; shi ne ya ɗora hannunsa akan wurin da yake jin ciwon, kuma sai ya ce: Bismillah, (Da sunan Allah) sau uku, sannan ya ce sau bakwai: (Ina neman tsari) ina fakewa kuma ina katanguwa (Da Allah da ikonSa daga sharrin abinda nake ji)na raɗaɗi a wannan lokacin (kuma nake tsoro) nake jin tsoron faruwarsa a nan gaba na baƙin ciki da tsoro, ko ya wannan cutar ta ci gaba kuma radadinta ya yadu a jiki.