Hadeeth Cards
Da'wa cards that highlight great meanings from the noble prophetic hadiths in a simple style and attractive display that helps the Muslim to have a deeper understanding of his religion in an easy way






























Da'wa cards that highlight great meanings from the noble prophetic hadiths in a simple style and attractive display that helps the Muslim to have a deeper understanding of his religion in an easy way
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya yi wa mutane huɗuba a ranar buɗe Makka sai ya ce: Ya ku mutane lallai cewa Allah haƙiƙa ya ɗauke kuma ya gusar muku da girman kan Jahiliyya, da jiji da kanta, da alfahari da iyaye, kawai dai mutane sun rabu gida biyu: Ko dai mumini mutumin kirki mai tsoron Allah mai biyayya ga Allah - Mai girma da ɗaukaka -, to, wannan mai girma ne a wajen Allah, ko da bai zama mai wani matsayi ko nasaba a wurin mutane ba. Ko kafiri fajiri taɓaɓɓe, to, wannan wulaƙantacce ne ƙasƙantacce a wurin Allah, kuma bai yi daidai da komai ba, ko da ya zama mai matsayi kuma yana da alfarma da mulki. Mutane dukkaninsu 'ya'yan Adam ne, kuma Allah Ya halicci Adam daga turɓaya, ba ya dacewa ga wanda asalinsa daga turɓaya ne ya yi girman kai ya yi jiji da kai, gasgata hakan shi ne faɗin Allah - Mai girma da ɗaukaka -: {Ya ku mutane lallai Mu Mun halicceku daga namiji da mace, kuma mun sanyaku jama'a da ƙabilu don ku san juna, lallai mafi girmanku a wajen Allah shi ne mafi tsoronku ga Allah, lallai Allah Masani ne Mai ba da labari} [Al-Hujurat: 13].
Lokacin da aya ta sauka: {Lallai wallahi za a tambayeku a wannan yinin game da ni'ima} wato: Za a tambayeku game da tsayuwa da godiyar abin da Allah Ya yi muku ni'ima da shi, sai Zubair ɗan Al-Awwam - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Ya Manzon Allah, shin wacce ni'ima ce za a tambayemu game da ita?! ni'imomi biyu ne kaɗai, da ba za su kai a tambaya ba, dabino ne da ruwa fa! Sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: Lallai tabbas za a tambayeku game da ni'ima tare da wannan yanayin da kuke ciki, ni'imomi ne guda biyu masu girma daga ni'imomin Allah - Maɗaukakin sarki -.
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya nemi Abdullahi Dan Mas'ud - Allah Ya yarda da shi - ya karanta masa wani abu na Alƙur'ani, sai ya ce; Ya Manzon Allah, ta yaya zan karanta maka alhali kai aka saukarwa?! sai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Lallai ni ina son in ji shi daga wanina, sai ya karanta masa Suratu al-Nisa'i yayin da ya kai ga faɗinSa Allah - Maɗaukakin sarki -:{To yaya al'amarin zai kasance idan Muka zo da kowace al'umma tare da mai yi mata shaida, kai kuma Muka zo da kai a matsayin mai shaida akan waɗannan al'ummar?} Wato yaya halinka da halin al'ummarka zasu kasance idan Muka zo da kai kana mai shaida ga al'ummarka cewa kai ka isar musu da saƙo, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: Ka tsaya da karatun a yanzu, Ibnu Mas'uda - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Sai na juya wajensa sai ga idanuwansa suna zubar da hawaye dan tsoron mauƙifin (alƙiyama), da kuma tausayin al'ummarsa.
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - a nan yana nuna cewa hassada nau'uka ne daban-daban, hadi da hassada abin zargi ne kuma haramtacce ne a shari'ance, wanda yake shi ne mutum ya yi fatan mutuwar dan uwansa, kuma hassada ta halatta, wacce ita ce ganin wata ni'imar duniya a gaban wasu, kuma yana yi wa kansa irin wannan, kuma hassadar Mahmud abin so ne bisa doka, wanda ake so. Albarkace ta addini yayin da wasu suke yiwa kanta fata. Wannan shi ne abin da Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yake nufi yayin da yake cewa: “Babu hassada sai a cikin biyu.” Ma’ana, hassada tana da nau’uka daban-daban da hukunce-hukunce gwargwadon nau’inta, kuma ba abin yabo ne ba kuma abin so ne a Sharia sai dai a cikin mas’aloli biyu: Na farko: akwai wani mai kudi kuma salihi wanda Allah ya ba shi kudi. Ya halatta, don haka ya ciyar da ita saboda Allah Ta'ala, kuma yana fatan hakan ta kasance, kuma ya sanya shi farin ciki da wannan ni'imar. Magana ta biyu: Ya kamata a sami wani mutum mai ilimi, kuma Allah ya ba shi ilimi mai amfani da zai yi aiki da shi, ya koyar da shi ga wasu, kuma ya yi hukunci da shi a tsakanin mutane, kuma yana fatan ya zama kamarsa.
Annabi -Tsira da aminci Allah su tabbata a gareshi- ya wakilata wasu daga Sahannabnsa a kan wata Rundunar yaki, don Jagorantar ta da kuma yin hukunci a tsakaninsu, kuma don kada abin ya zama babu tsari, kuma ya zabi wanda ya fi kowanne Addini da Ilimi da kuma iya tafi da yaki, shi yasa Shugabannin sune Limamai a cikin salloli, kuma su suke bada Fatawa sabida Iliminsu da Addininsu, to sai ya rika karanta musu Kulhuwa a kowace Rakao'i biyu na kowace Sallah; sabida sonsa da Allah da kuma sunayensa da sifofinsa, kuma duk wanda yaso Allah to zai yawaita ambatonsa, to yayin da suka dawo daga yakin nasu zuwa ga Annabi sai suka gaya masa abinda ya faru sai ya cce ku tambayae shi mai yasa yake yi sai suka tambayeshi mai yasa yake yin hakan haka kawai yake yi ko kuma sabida wani abu ne? sai Jagoran nasu ya ce: ina yin haka ne Sabida ta kunshi sifofin Allah don haka nake son Maimaita ta sai Annabi ya ce ku gaya masa kamar yadda ya ke maimaita wannan sura saboda soyayyarsa da ita; kuma sabida abinda ta kunsa na sifofin Allah masu girma wanda wannan Surata kunsa na Sunayensa da aka ambata, to shima Allah yana sonsa, kai wannan ta isa falala.