Hadeeth Cards
Da'wa cards that highlight great meanings from the noble prophetic hadiths in a simple style and attractive display that helps the Muslim to have a deeper understanding of his religion in an easy way






























Da'wa cards that highlight great meanings from the noble prophetic hadiths in a simple style and attractive display that helps the Muslim to have a deeper understanding of his religion in an easy way
Annabi tsira da aminci su tabbata agareshi yana yiwa Al'umarsa bushara da cewa hakika Allah maitsarki da daukaka yana kebantarsu da Alamar fifiko da daukaka ranar Alkiyama,a tsakanin Al'umai,ta yarda za'a kirawosu sai su zo agaban Halittu Fuskokinsu daHannayensu da Kafafuwansu suna kyalkyali na haske, wancananka gurbine daga guraben wannan Ibada maigirma,itace Alwala wacce suka dinga maimaitata abisa wannan Gabobi masu Alfarma don neman yardar Allah, da kuma neman ladansa, sai sakamakonsu ya kasance wannan girmamawar maigirma kebantacciya.Sannan Abu Huraira Allah ya yarda dashi yake cewa: "Wanda ya sami ikon tsawaita wannan Fari to ya aikata" domin cewashi duk sanda ya tsawaita bigiran wankewa daga Gaba Fari da kyalkyali zai karu, domin cewa adon Hasken yana kaiwa inda Ruwan Alwala ya kai, sai dai abin shar'antawa kawai wanke Hannaye biyu acikin Alwala ya zama zuwa gwiwar Hannaye biyu ya shigar da gwiwar da farawa da Dantse da wanke wani yanki daga gareshi, da kuma wanke Diga Digai biyu izuwa Idon sawaye biyu ya shigar da Idon sawayen biyu da farawa da kauri, kuma ba'a shara'anta wanke Dantse da kauri acikin Alwala ba
A`isha Allah ya kara yarda da ita tana ambatar: cewa maniyyin janaba ya kasance yana shafar tufafin manzon Allah mai tsira da aminci su kara tabbata a gareshi, wani lokacin yana kasancewa danye sai ta wankeshi daga tufafin da ruwa, sai ya fita zuwa salla, alhalin ruwan bai gama bushewa daga tufafin ba, wani lokacin daban kuma, maniyyin yana kasancewa busashshe, a wannan lokacin sai ta kankare shi daga tufafin nashi kankarewa, sai yayi salla a cikinsa.
Uwar muminai Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - ta bada labarin cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - bai kasance mafi tsananin lazimta da kuma kiyaye wa ba akan wani abu na nafiloli sama da raka'o'i biyu ratibai na kafin sallar Asuba ba.
Wannan hadisi yana bayani akan falalar sallar jam'i akan sallar mutum shi kadai,cewa abin da ke cikin fa'idojin sallar jam'i da maslahar jiki- ya wuce na mai yin salla shi kadai da lada ashirin da bakwai, ba makawa wanda ya yi asarar wannan riba mai girma ya yi babbar asara
Mu'azah al'adawiyya - ta tambayi uwar muminai Nana A'isha - Allah Yarda da ita -, sai ta ce: Me yasa mai al’ada take rama azimi, bata rama sallah? Sai ta ce mata: Shin ke daga Khawarijawa Hirarura’a kike ne ? waɗanda suke yawaita tambaya dan ta'annuti da kuma tsanantawa? Na ce: Ni ba baharuriyyababa ce, sai dai tambaya nake yi, ta ce: al’ada tana samunmu tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai a umarcemu da rama azimi, ba'a umartarmu da rama sallah.
Wannan hadisin ya tabbatar da tsarin musulunci na kyautatawa marassa karfi, kamar marayu da mata, kuma abin lura a cikin wannan hadisin cewa Annabi –sallal Lahu alaihi wa sallama- ya wuce gona da iri game da kula da hakkin maraya da mace. Saboda ba su da hakkin su juyo gare shi kuma su kare su, don haka ya sanya - don Allah ya yi salati da sallama a gare shi - jin kunya, taurin kai da wahala kan wadanda suka dauki hakkinsu.
Aisha-Allah ya yarda da ita- ta fadi cewar Annabi tsira da aminci ya kasance yana kishingida kan cinyarta ya karanta Alqur'ani alhali tana haila, wannan shi ke nuna cewa jikin mai haila tsarkakakke ne, ba ya zama najasa saboda haila.
Wannan hadisi yana nuni da lokacin da yafi a yi kowacce daga cikin salloli biyar,ka ga sallar Azahar:ana yin tane lokacin da rana ta karkata daga tsakkiya,shi ne lokacin zawali, shi ne farkon lokacinta.La'a sar kuma: ana yinta lokacin da rana take fara fat, ba wani fatsi-fatsi da ya gauraya da ita,yadda ake gane lokacinta shi ne tsawon komai ya lunka, Magariba kuma ana yinta ne lokacin faduwar rana da sanda ta buya. Issha'i kuma sai a kula da yanayin mutane in sun zo da wuri a farkon lokacinta,shi ne lokacin buyan jan shafaki to sai a yi ta, in kuma basu zo ba to sai a jinkirta ta har wajen tsakkiyar dare na farko, don shi ne lokacinta da ya fi ba don takurawa ba. amma Asuba shi ne farkon lokacin da haske ya fara dan bullowa