





























Hadeeth Cards
Da'wa cards that highlight great meanings from the noble prophetic hadiths in a simple style and attractive display that helps the Muslim to have a deeper understanding of his religion in an easy way
All
Daga Ummu Aɗiyya - Allah Ya yarda da ita - ta ce: An hanamu bin jana'iza, amma ba'a ƙarfafa hanin a kanmu ba.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiUmmu Aɗiyya al-Ansariyya - Allah Ya yarda da ita - tana bada labarin cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya hana mata bin jana'iza; hakan saboda abinda ake jin tsoro a cikin hakan na fitina garesu da kuma fitinuwa da su, da kuma ƙarancin haƙurinsu, sannan Allah Ya yarda da ita ta bada labarin cewa bai ƙarfafa hanin ba kamar yadda yake aikatawa a sauran abubuwan da ya hana.
Daga Abu huraira -Allah ya yarda da shi- ya ce: An zuwarwa Manzon Allah SAW da wani Mutum ya Sha Giya, sai ya ce: "Ku masa Duka" sai Abu huraira ya ke cewa: daga cikin mu akwai mai dukansa da hannu da Mai dukansa da Takalmi, da mai dukansa da tufarsa, yayin da ya juya sai wasu daga cikin Mutane suka ce: Allah ya Qasqantaka, sai ya ce: "Kada ku ce haka, kada ku taimakawa shixan a kansa"
Buhari ne ya rawaito shiDaga Anas Allah ya yarda da shi - zuwa ga Annabi: "Ya umarci Bilal da ya maimaita lafazin kiran salla sau bibbiyu, kiran salla kuma sau daida
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiAnnabi tsira da amincin Allah ya umarci ladaninsa' Bilal da ya maimaita lafazin kiran salla sau bibbiyu don shi kairan salla sanarwace ga wanda ba su nan,amma banda kabbara a farkonta,hakanan kuma yinsa sau hurhudu ya tabbata,hakanan kuma yin kalmar tauhidi sau daya akarshe,haka nan ya tabbata yinta sau daidai,kamar yadda ya umarci Bilal ya yi ikama sau daidai, domin ita tunatar da wanda suke gurin ne,amma banda(takbir),da lafazin kad kamatissalatu"don maimaita su sau bibbiyu ya tabbata
An karbo daga Anas Dan Malik Allah ya yarda dashi"Cewa Kakarsa Mulaika ta gaiyaci Manzan Allah tsira da amincin Allah su tabbata agareshi saboda wani Abinci da ta shirya masa,sai yaci daga gareshi.sannan yace:ku tashi nai muku Salla?sai Anas yace:Sai na tashi zuwa wata Tabarmarmu wace tayi Kura saboda an dade da shinfida ta,sai na yayyafa mata Ruwa,sai Manzan Allah tsira da amincin Allah su tabbata agareshi ya tsaya akanta ni da Marayan sai muka yi sahu a bayansa,Tsohuwar kuma tana daga bayanmu, sai yayi mana Salla raka'a Biyu sannan ya juya".Daga Muslim kuma"Cewa Manzan Allah tsira da amincin Allah su tabbata agareshi yayi masa Salla da Mahaifiyarsa sai ya tsayar dani a Damansa,ya tsayar da Macen a bayanmu".
Muslim ne ya rawaito shi - Bukhari da Muslim suka Rawaito shiMulaika Allah ya yarda da ita ta gaiyaci Manzan Allah tsira da amincin Allah su tabbata agareshi saboda wani Abinci da ta shirya masa,hakika Allah Madaukakin Sarki ya halicceshi abisa mafi Girman Karamci kuma mafi Daukakar Dabi'u,yana daga cikinta Kaskantar da Kai mai yawa,ya kasance duk da daukakar Kadarinsa da kuma girman Matsayinsa yana amsa gaiyatar Babba da Karami,da Namiji da Mace,da Mawadaci da Talaka,yana nufi da hakan Manufofi Madaukaka, da kudure-kudure masu girma na daga gyara zukatan Mabukata,da kaskantar da kai ga Miskinai,da kuma sanarda Jahilai,da wasun wadannan na daga manufofinsa ababan yabo,sai yazo wajan wannan mai Gaiyatar,yaci daga Abincinta,sannan yayi amfani da wannan damar don ya sanar da wadannan Raunanan wadanda da yawa ba zasu iya gogayya da Manyaba a Mazauninsa mai Al-Barka,sai ya umarcesu da tsayawa don yayi musu Salla,kuma su san yadda ake yin Salla daga gareshi,sai Anas ya nufi wata tsohuwar Tabarma,wacce tayi kura saboda tsahon zama da amfani,sai ya wanke ta,sai Manzan Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya tsaya yana yi musu Salla,sai Anas yayi sahu,da wani Maraya dake tare dashi,sahu Daya bayan Annabi tsira da amincin Allah su tabbata agareshi,sai tsohuwar-maiGaiyatar-tayi sahu a bayan Anas da Marayan,tana Salla tare dasu,sai yayi musu Salla raka'a Biyu,sannan ya juya bayan ya cika hakkin Gaiyatar da kuma ilmantarwa tsira da amincin Allah su tabbata agareshi,Allah yayi mana baiwa ta binsa cikin Aiyukansa da Dabi'unsa.
Daga Abdullahi Dan Umar daga Annabi: "Idan Dayanku Matarsa ta nemi izininsa zuwa Masallaci kada ya hanata;ya ce sai Bilal dan Abdullahi Wallahi sai mun hana su, yace: sai abdullahi ya fuskanto shi, sai ya zage shi zagi sosai, ban taba jin zagi irinsa ba a baya, kuma ya ce: ina baka labari daga Annabi kuma ya ce: Wallahi sai mun hanasu" a wani lafazin kuma: "Kada ku hana bayin Allah Masallatan Allah"
Buhari da Muslim suka rawaito shi da ruwayoyin saAn rawaito daga Umar -Allah ya yarda da su- cewa Annabi ya ce: Idan Dayanku Matarsa ta nemi izininsa zuwa Masallaci kada ya hana ta; don kada ya haramta mata fafalalar sa,mun Jam'i a Masallaci kuma a cikinsa akwai bayanin Hukuncin futar Mace zuwa Masallaci don yin sallah, kuma cewa shi Halak ne, kuma Daya daga cikin yayan Abdullahi dan Umar yana nan a lokacin da abin ya faru, kuma ya kasance ya ga lokacin mai tsawo wanda ya canza daga zamanin Annabi da yawaitawar Mata da ado, sai wannan ya sanya shi kishi ya kamashi kan tsare Mata, kan haka ne ma ya ce-ba tare da futo na futo da sharia ba- kuma wallahi da ya hanasu sai mahaifinsa ya gano daga Maganarsa cewa yana musantawa ne da wannan maganar tasa akan Sunnar Annabi wannan yasa yayi fushi da sabida da Allah da Manzonsa, kan cewa zaginsa zagi ne babba mai tsanani, kuma ya ce: ina baka labari daga Annabi kuma kai kana cewa wallahi sai mun hanasu?
Daga Anas bn Malik - yardar Allah ta tabbata a gare shi - "Annabi mai tsira da amincin Allah, da Abubakar da Omar - Allah ya yarda da su - sun kasance suna gabatar da salla da" Godiya ta tabbata ga Allah, Ubangijin talikai ". Kuma a cikin wani labari: "Na yi Sallah tare da Abubakar, Umar da Othman, kuma ban ji wani daga cikinsu yana karantawa ba" Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai. " Kuma ga Muslim: "Na yi addu'a a bayan Annabi - Salatin Allah da amincin Allah su tabbata a gare shi - da Abu Bakr, Umar da Othman, kuma suka bude da" Godiya ta tabbata ga Allah, Ubangijin talikai, "ba za su ambaci" Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai, "a farkon ko ƙarshen karatun.
Muslim ne ya rawaito shi - Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDaga Abu Sa`id al-Khudri - yardar Allah ta tabbata a gare shi - a cikin marfoo: "Daga cikin mafiya sharrin mutane akwai matsayi a wurin Allah ranar tashin kiyama. Namiji ne ya kai wa ga matar ya sadar da shi gare shi, sannan ya buga shi".
Muslim ne ya rawaito shiAnnabi mai tsira da amincin Allah - ya yi bayanin cewa daga cikin sharrin mutane Allah ne ya tsara su a ranar tashin kiyama kuma ya siffantu da wannan cin amanar, kuma shi ne wanda yake da niyyar yada sirrin gidan aure, wanda sai masu aure ne kawai za su gani. Abubuwan jin dadi da kuma bayanin dalla-dalla game da hakan, da kuma abin da ke faruwa ga mace a ciki dangane da magana ko aikatawa da makamantansu. Dangane da ambaton saduwa kawai, idan ba ta da fa'ida ko bukata, to ba a so. Saboda ya saba wa koyarwar sojan gona, kuma shi - Allah da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Duk wanda ya yi imani da Allah da Ranar Lahira, to ya fadi alheri ko ya yi shiru," kuma idan akwai wata bukata gare shi, ko amfanar da shi, ta hanyar hana shi juyawa daga gare ta, ko da'awar cewa ba zai iya saduwa ba, ko Hakanan, ba makaruhi bane ambaton kasancewar maslaha a cikin haka, kamar yadda Sunnah ta nuna.
Daga Ummusalama -Allah ya yarda da ita- tace:"Ummu Sulaim Matar Abi Dalha ta zo wajen Annabi -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- tace:"Ya Manzon Allah, Allah baya jin kunya game da gaskiya,shin mace zata yi wanka idan tayi mafarki?sai Manzon Allah -tsira da amincin Allah- yace: Eh, zata yi amma in ta ga ruwa."
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiUmmu Sulai 'Yar Madina -Allah ya yarda da ita- ta zo wajen Annabi -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- don ta tambaye shi,kasancewar tambayar na da alaka da matunci,akan ji kunyar fada,shi ne ta fara gabatar da yan kalmomin don yin shimfida ga tambayar ta. Sai tace: Allah Madukaki shi ne Gaskiya,bai hana ambaton gaskiya,in dai akwai wani amfani cikin tambayar,bayan Ummu Sulaim ta gabatar da wannan shimfida,sai ta fadi tambayarta kai tsaye,tace:shin mace zata yi wanka in tayi mafarki ana saduwa da ita?Sai Annabi tsira da aminci yace,za ta yi wanka indai har ta ga mani.
Daga Nana A'isha Uwar muminai - Allah Ya yarda da ita - matar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ta ce: Wata mata ta zo a tare da ita akwai 'ya'yanta biyu mata, bata samu komai awurina ba banda wani dabino ɗaya, sai na bata shi sai ta raba shi tsakanin 'ya'yan nata mata biyu, sannan ta tashi sai ta fita, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya shigo sai ta zantar da shi, sai ya ce: «Wanda ya jiɓinci wani abu daga waɗannan 'ya'ya matan, sai ya kyautata musu, zasu zama kariya gare shi daga wuta».
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiUwar muminai Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - ta bada labarin cewa wata mata ta zo mata a tare da ita akwai 'ya'yanta biyu mata tana tambayarta ta bata abinda zata ci, Nana A'isha bata samu komai a wurinta ba banda dabino ɗaya, sai ta bata shi sai matar ta raba dabinon tsakanin 'ya'yan nata mata biyu ba ta ci komai daga gare shi ba, sannan ta tashi sai ta fita, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya shiga (gida) sai Nana A'isha ta zantar da shi, sai ya ce: Duk wanda ya jiɓinci wani abu daga waɗanan 'ya'ya matan, sai ya kyauata musu ya tarbiyantar da su ya ciyar da su ya shayar da su ya tufatar da su kuma ya yi haƙuri akan haka, zasu zama sutura da kariya gare shi daga wuta.