





























Hadeeth Cards
Da'wa cards that highlight great meanings from the noble prophetic hadiths in a simple style and attractive display that helps the Muslim to have a deeper understanding of his religion in an easy way
All
Daga Abu Katada AsSulami - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Idan ɗayanku ya shiga masallaci, to, ya yi sallah raka'a biyu kafin ya zauna".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kwaɗaitar da wanda ya zo masallaci ya shige shi a kowanne lokaci, da kowacce manufa, ya yi sallah raka'a biyu kafin ya zauna, su ne raka'o'i biyun gaisuwar masallaci.
Daga Abu Humaid ko daga Abu Usaid ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Idan ɗayanku zai shiga masallaci, to, ya ce: Ya Allah Ka buɗe min ƙofofin rahamarKa, idan zai fita, to, ya ce: Ya Allah ina roƙonKa daga falalarKa".
Muslim ne ya rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya shiryar da al'ummarsa addu'ar da ake faɗa a yayin shiga masallaci: (Ya Allah ka buɗe min ƙofofin rahamarKa), sai ya roƙi Allah - Maɗaukakin sarki - Ya sawwaka masa hanyoyin rahamarSa, idan ya yi nufin fita, to, ya ce: (Ya Allah ina roƙonKa daga falalarKa), sai ya roƙi Allah daga falalarSa da ƙarin kyautatawarSa daga arziki na halal.
Daga Salim ɗan Abulja'ad ya ce: Wani mutum ya ce: Ina ma dai na yi sallah in huta, kamar cewa su (sauran mutanen) sun aibata masa hakan, sai ya ce: Naji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa: "Ya Bilai, ka yi iƙamar sallah, ka hutar da mu da ita".
Abu Dawud ne Ya Rawaito shiWani mutum daga sahabbai ya ce: Ina ma na yi sallah in huta, kai ka ce waɗanda ke gefensa sun aibata hakan gare shi , sai ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa: Ya kai Bilal! ka kira sallah ka yi iƙamarta; don mu samu hutu da ita; saboda abin da ke cikinta na ganawa da Allah - Maɗaukakin sarki - da kuma hutu ga rai da zuciya.
Daga Abu Hazim Dan Dinar Lallai wasu mutane sun zo wa Sahlu ɗan Sa'ad Al-sa'idiy alhali sun yi musu a sha'anin minbarin (Manzon Allah) katakwayensa na mene ne, sai suka tambaye shi game da hakan, sai ya ce: Na rantse da Allah ni na san na mene ne su, haƙiƙa na gan shi a farkon ranar da aka ajiye shi, da kuma farkon ranar da Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya fara zama a kansa, Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya aika zuwa ga wance - wata mace daga Mutanen Madina -Sahlu ya ambace ta -; "Ki umarci yaronki kafinta ya haɗa min katakwaa da zan zauna a kansu idan zanyiwa mutane magana". Sai ta umarce shi sai ya yisu daga bishiyoyin daji, sannan ya zo da su, sai ta aika zuwa ga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, sai ya yi umarni aka ajiyesu a nan, sannan na ga manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya yi sallah a kansu ya yi kabbara alhali yana kansu, sannan ya yi ruku'u alahali yana kansu, sannan ya sauko da baya, sai ya yi sujjada a asalin minbarin sannan ya dawo, yayin da ya gama sai ya fuskanci mutane sai ya ce: "ya ku mutane, kawai na aikata haka ne don ku yi koyi da ni, kuma ku san sallata".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiWasu mutane sun zo wa ɗaya daga sahabbai suna tambayarsa game da minbarin Annabi wanda Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya riƙeshi: Da me aka yi shi? Haƙiƙa sun yi jayayya a hakan, sai ya ambata musu cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya aika zuwa ga wata mata daga Mutanen Madina tana da wani yaro kafinta, sai ya ce da ita: Ki umarci yaronki ya yi min minbarin da zan zauna a kansa lokacin da zan yi wa mutane magana, sai matar ta amsa, ta umarci yaronta ya yi wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - minbari na bishiyar Ɗarfa'u, lokacin da ya gama sai matar ta aika da munbarin zuwa ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, sai ya yi umarni da shi sai aka ajiye shi a wurinsa a masallaci, sannan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya yi sallah a kansa ya yi kabbara alhali yana kansa, sannan ya yi ruku'u alhali yana kansa, sannan ya sauka yana tafiya ta baya, ba tare da ya juyo da fuskarsa ba zuwa ta baya ba, sai ya yi sujjada a asalin minbarin sannan ya dawo, lokacin da ya gama sallar sai ya fuskanci mutane, ya ce: ya ku mutane, kaɗai na aikata haka ne don ku yi koyi kuma ku san sallata.
Daga Hiɗɗan ɗan Abdullahi Al-Raƙashi ya ce: Na sallaci wata sallah tare da Abu Musa Al-Assh'ari, a lokacin zama sai wani mutum daga mutane ya ce: An haɗa sallah da aikin alheri da kuma zakka, ya ce: Lokacin da Abu Musa ya gama sallar ya yi sallama, sai ya juya ya ce: Waye mai faɗin kalmar kaza da kaza a cikinku? ya ce: Sai mutane suka yi shiru, sannan ya ce: Waye ya faɗi kalmar kaza da kaza a cikinku? sai mutane suka yi shiru, sai ya ce: Wataƙila kai Hiɗɗanu kai ka faɗeta? sai ya ce: Ban faɗeta ba, haƙiƙa na ji tsoron kada ka zargeni da ita, sai wani mutum daga mutanen ya ce: Ni na faɗeta, kuma ban nufi komai da ita ba sai alheri, sai Abu Musa ya ce: Shin kun san me zaku fada a sallarku? lallai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya yi mana huɗuba sai ya bayyana mana sunnonimmu, ya kuma sanar da mu sallolinmu. "Idan za ku yi sallah, to, ku daidaita sahunku, sannan ɗayanku ya yi muku limanci, idan ya yi kabbara sai ku yi kabbara, idan ya ce: {Ba waɗanda ka yi fushi da su ba, ba kuma ɓatattu ba} [Al-Fatiha: 7], sai ku ce: Ameen, Allah zai amsa muku, idan ya yi kabbara ya yi ruku'u, sai ku yi kabbara ku yi ruku'u, domin cewa liman yana yin ruku'u ne kafinku, kuma yana ɗagowa ne kafinku", sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Waccan da waccan, idan ya ce: Allah Ya ji wanda ya gode maSa, sai ku ce: Ya Allah Ubangijinmu godiya ta tabbata gareKa, Allah Zai jiye muku (wato Zai amsa); domin cewa Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya faɗa a kan harshen AnnabinSa - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -: Allah Ya ji wanda ya gode maSa, idan ya yi kabbara ya yi sujjada sai ku yi kabbara sai ku yi sujjada, domin cewa liman yana yin sujjada ne kafinku kuma yana ɗagowa ne kafinku", sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Waccan da waccan, idan an zo wurin zama; to, farkon abin da ɗayanku zai faɗa (shi ne): gaisuwa ta tabbata ga Allah tsarkakan salloli sun tabbata ga Allah, aminci ya tabbata a gareka ya kai wannan Annabi da rahamar Allah da albarkarSa, aminci ya tabbata a garemu da bayin Allah nagari, ina shaidawa cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, ina shaida cewa (Annabi) muhammadu bawanSa ne, kuma manzonSa ne".
Muslim ne ya rawaito shiSahabi Abu Musa Al-Ash'ariy - Allah Ya yarda da shi - ya yi wata sallah, alokacin da ya yi zaman da a cikinsa akwai tahiya, sai wani mutum daga masallata a bayansa ya ce: An haɗa sallah a cikin Alkur’ani da aikin alheri da kuma zakka, lokacin da Abu Musa - Allah Ya yarda da shi - ya gama sallar sai ya fuskanci mamu, sai ya tambayesu: Waye a cikinku ya faɗi kalmar: An haɗa sallah da aikin alheri da zakka a cikin Alkur’ani ?! sai mutanen suka yi shiru, wani daga cikinsu bai yi magana ba, sai ya maimaita musu tambayar karo na gaba, yayin da babu wanda ya amsa masa, sai Abu Musa - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Wata ƙila kai ya Hiɗɗan kai ka faɗeta! don ƙarfin halinsa da kuma kusancinsa gareshi, da dangantakarsa da shi ta yadda ba zai cutar da shi ba a tuhumarsa, kuma don ya sanya mai maganar na haƙiƙa zuwa tabbatarwa, sai Hiɗɗan ya kore hakan, sai ya ce: Haƙiƙa na ji tsoron za ka zargeni saboda zaton cewa ni na faɗeta; a nan sai wani mutum daga mutanen ya ce: Ni na faɗeta, kuma ban nufi komai da ita ba sai alheri, sai Abu Musa ya ce yana mai sanar da shi; Shin kun san ya za ku ce a sallarku?! hakan nuna ƙyama ne da ɓangarensa, sannan a ƙarshe Abu Musa ya sanar da cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya yi musu huɗuba wata rana, sai ya bayyana musu shari'o'insu, ya kuma sanar da su sallarsu, sai (Annabi) tsira da amin Allah su tabbata agare shi - ya ce: Idan za ku yi sallah, to, ku daidaita sahunku, sannan ɗaya daga cikinku ya yi muku limanci, idan liman ya yi kabbarar harama, sai ku yi kabbara irinsa, idan ya karanta fatiha ya kai { Ba waɗanda aka yi fushi da su ba, ba kuma ɓatattu ba} [Al-Fatiha: 7], sai ku ce: Ameen; idan kun aikata hakan Allah Zai amsa muku addu'arku, idan ya yi kabbara ya yi ruku'u sai ku yi kabbara ku yi ruku'u; domin cewa liman yana ruku'u ne kafinku kuma yana ɗagowa kafinku, kada ku rigaye shi; domin a lokacin liman ya rigayeku a gabatowa zuwa ruku'u; to, za ta gyara muku da jinkirinku a ruku'u bayan ɗagowarsa a lokacin, to, waccan lokacin da waccan lokacin, sai gwargwadon ruku'inku ya zama kamar gwargwadon ruku'insa, idan liman ya ce: Allah ya ji wanda ya gode maSa, sai ku ce: ya Allah Ubangijinmu godiya ta tabbata gareKa, idan masallata suka faɗi hakan, to, Allah - tsarki ya tabbatar maSa - Yana jin addu'arsu da kuma maganarsu; domin cewa Allah - tsarki ya tabbatar maSa Ya ɗaukaka - ya faɗa a kan harshen AnnabinSa tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -: Allah Ya ji wanda ya gode maSa, sannan idan ya yi kabbara ya yi sujjada, to, ya wajaba a kan mamu su yi kabbara su yi sujjada, domin cewa liman yanayin sujjada ne kafinsu, kuma yana ɗagowa ne kafinsu, to, waccan lokacin da waccan lokacin, kuma gwargwadon sujjadar mamu ya zama kamar gwargwadan sujjadar liman ne, idan ya kasance a lokacin zama domin tahiya ne, to, farkon faɗin mai sallah ya zama: "Gaisuwa da tsarkakan salloli sun tabbata ga Allah" mulki da wanzuwa da girma dukkaninsu ababen cancanta ne ga Allah - Maɗaukakin sarki -, haka nan salloli biyar dukkaninsu na Allah ne, "Aminci ya tabbata a gareka ya kai wannan Annabi da rahamar Allah da albarkacinSa, aminci ya tabbata agaremu da kuma bayin Allah na gari", to, ku roƙi Allah kuɓuta daga dukkanin aibi da tawaya da ɓarna; kuma muna keɓantar Annabinmu Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - da sallama, sannan mu yi wa kawunanmu sallama, sannan mu yi sallama ga bayin Allah na gari masu tsayawa da abin da ya wajaba a kansu na haƙƙokin Allah da kuma haƙƙokin bayinSa, sannan mu shaida cewa babu abin bautawa da agsakiya sai Allah, kuma mu shaida cewa (Annabi) Muhammad bawanSa ne kuma ManzonSa ne.
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - Lallai ya kasance yana yin kabbara a kowacce sallar farilla da watanta, a Ramadan da waninsa, sai ya yi kabbara a yayin da yake miƙewa, sannan ya yi kabbara a yayin da yake yin ruku'u, sannan ya ce: Allah Ya ji wanda ya gode maSa, sannan ya ce: Ya Ubangijimmu godiya ta tabbata gareKa kafin ya yi sujjada, sannan ya ce: Allah ne mafi girma a yayin da yake tafiya ƙasa don yin sujjada, sannan ya yi kabbara a yayin da yake ɗago kansa daga sujjada, sannan ya yi kabbara a yayin da yake ɗago kansa daga sujjada, sannan ya yi kabbara a yayin da yake miƙewa daga zama a raka'a ta biyu, zai aikata haka a kowacce raka'a, har sai ya gama sallar, sannan ya ce a yayin da yake juyawa: na rantse da wanda raina yake a hannunSa lallai ni ne mafi kusancinku kamanceceniya da sallar manzon Allah -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - wannan ita ce sallarsa har ya bar duniya.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiAbu Huraira - Allah Ya yarda da shi - yana ruwaito wani yanki daga siffar sallar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, yana ba da labarin cewa ya kasance idan ya tashi yin sallah yana kabbarar harama a yayin da yake miƙewa, sannan ya yi kabbara a yayin da yake cirata zuwa ruku'u, da yayin da yake yin sujjada, da yayin da yake ɗago kansa daga sujjada, da yayin da yake yin sujjada ta biyu, da yayin da yake ɗago kansa daga gareta, da yayin da yake miƙewa daga raka'a biyun farko bayan zama don tahiyar farko a sallah mai raka'a uku ko huɗu, sannan ya aikata hakan a dukkanin sallah har sai ya gamata, ya kasance yana cewa a yayin da ya ɗago bayansa daga ruku'u: Allah Ya ji wanda ya gode maSa, sannan ya ce alhalin yana tsaye: Ya Ubangijimmu godiya ta tabbata a gareKa. Sannan Abu Huraira yake cewa a yayin da ya idar da sallar: Na rantse da wanda raina yake a hannunSa, lallai ni ne mafi kusancinku kamaceceniya da sallar Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - wannan ita ce siffar sallarsa har ya bar duniya.
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Mafi munin mutane sata shi ne wanda yake satar sallarsa" sai ya ce: Ta yaya zai saci sallarsa? sai ya ce: "Ya zamo ba ya cika ruku'unta, ba ya cika sujjadarta".
Ibnu Hibban ne ya Rawaito shiAnnabi -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bayyana cewa mafi tsananin mutane muni a sata shi ne wanda yake satar sallarsa; hakan ya kasance ne domin karɓar dukiyar wani wataƙila zai iya amfani da ita a duniya, saɓanin wannan satar, domin ya saci haƙƙin kansa na sakamako da lada, suka ce: Ya Manzon Allah, ta yaya zai saci sallarsa? sai ya ce: Ba ya cika ruku'unta kuma ba ya cika sujjadarta; hakan yana nufin ya yi gaggwa a ruku'u da sujjada, ba zai zo da su ba a kan cikkakkiyar fuskar su ba.
Daga Ibnu Abi Aufa - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance idan ya ɗago bayansa daga ruku'u sai ya ce: "Allah Ya ji wanda ya gode maSa, ya Allah Ubangijimmu godiya ta tabbata gareKa, cikar sammai da cikar ƙasa da cikar abin da ka so daga wani abu bayan nan"
Muslim ne ya rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance idan ya ɗago bayansa daga ruku'u a sallah yana cewa: Allah Ya ji wanda ya gode maSa", wato: Cewa wanda ya godewa Allah - Maɗaukakin sarki - Allah - Maɗaukakin - sarki Ya amsa masa, Ya karɓi godiyarsa kuma Ya saka masa, sannan ya godewa Allah da faɗinsa; "Ya Allah Ubangijinmu godiya ta tabbata a greKa, cikon sammai da cikon ƙasa da cikon abin da Ka so daga wani abu bayan nan", godiyar da za ta cika sammai da ƙassai da abin da ke tsakaninsu, kuma ya cika abin da Allah Ya so daga wani abu.
Daga Warrad magatakardar Mugira ɗan Shu'uba ya ce: Mugira ɗan Shu'uba ya yi min shifta ( yana fada ina rubutawa) ta wata wasiƙa zuwa ga Mu'awiyya: Lallai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance yana faɗa a bayan kowacce sallar farilla: "babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Shi kaɗai Yake ba Shi da abokin tarayya, mulki nasa ne godiya tasa ce, Shi mai iko ne a kan dukkan komai, ya Allah ba mai hana abin da Ka bayar, ba mai bayar da abin da Ka hana, mai wadata wadatarsa bata amfanar da shi (komai) a wajenKa".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance yana faɗa a bayan kowacce sallar farilla: "Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Shi kaɗai yake ba Shi da abokin tarayya, mulki nasa ne, godiya ta tabbata a gareShi, Shi mai iko ne a kan dukkan komai, ya Allah ba mai hana abin da Ka bayar, kuma ba mai bayar da abin da Ka hana, kuma mai wadata wadatarsa ba ta amfanar da shi (komai) a wajenKa". Wato: Ina tabbatar da kalmar tauhidi babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, ibada ta gaskiya ina tabbatar da ita ga Allah, kuma ina koreta daga waninSa, babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma ina tabbatar da cewa mulki na haƙiƙa cikakke na Allah ne, dukkanin godiyar wadanda ke sammai da ƙasa abar cancanta ce ga Allah - Maɗaukakin sarki -, yayin da yake Shi mai iko ne a kan dukkan komai, kuma abin da Allah Ya kaddara shi na bayarwa ko hanawa ba mai juyar da shi, kuma a wajenSa wadata ba ta amfanar da ma'abocinta, kaɗai aikinsa nagari ne zai amfanar da shi.