





























Hadeeth Cards
Da'wa cards that highlight great meanings from the noble prophetic hadiths in a simple style and attractive display that helps the Muslim to have a deeper understanding of his religion in an easy way
All
Daga Ɗan Abbas - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Allah ba Ya duba zuwa ga namijin da ya zo wa wani namiji ko wata mace ta dubura".
Tirmizi da Nasa'i a cikin Al-kubra ne Suka rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana narko mai tsanani da cewa Allah ba Ya duba duban rahama zuwa namijin da ya zo wa namiji ta duburarsa ko mace ta duburarta, kuma hakan laifi ne babba daga cikin manyan laifuka.
Daga Mu'awiyya alKushairi - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ce: Ya Manzon Allah, menene haƙƙin matar ɗayanmu a kansa?, ya ce; "Ka ciyar da ita idan kaci, ka tufatar da ita idan ka tufatar (da kanka), ko ka yi aiki, kada ka daki fuska, kada ka munana, kuma kada ka ƙaurace sai a ɗaki".
Abu Dawud ne ya rawaito shi da Ibnu Majah da AhmadAn tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - menene haƙƙin mata akan mijinta? sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ambaci wasu al'amura, daga cikinsu: Na farko: Kada ka keɓanci kanka da abin ci banda ita; kai ka ciyar da ita a duk lokacin da ka ci abin ci. Na biyu: Kada ka keɓanci kanka da tufatarwa da tufafi, kai ka tufatar da ita idan ka tufatar (da kanka), hak idan ka yi aiki kuma ka samu iko. Na uku: Ba'a dukanta sai da wani sababi da buƙatuwa, idan ya buƙatu zuwa dukanta dan ladabtarwa ko dan barinta wasu farillai to sai ya zama duka ba mai sa rauni ba; kuma ba'a dukan fuska; domin cewa fuska ita ce mafi girman gaɓɓai kuma mafi bayyanarsu kuma ta ƙunshi wasu sasanni manya da gaɓɓai masu laushi. Na huɗu: Kada ka yi zagi ko ka ce : Allah Ya munana fuskarki; kada ka danganta koda wani abu daga jikinta zuwa munin da shi ne kishiyar kyau; domin cewa Allah - Maɗaukakin sarki - Shi ne wanda Ya suranta fuskar mutum da jikinsa, kuma Ya kyautata halittar kowane abu, zargin halitta yana komawa ne zuwa zargin Mahalicci tsarki ya tabbata ga Allah. Na biyar: Kada ka ƙaurace sai a wurin kwanciya, kuma kada ka juya mata baya, kada ka juyar da ita zuwa wani gidan daban; wataƙila hakan a cikin abinda afkuwarsa yake sabawa ne daga ƙauracewa tsakanin miji da mata.
Daga Abdullahi ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya la'anci mai yin ƙarin gashi da wacce ta nemi a yi mata ƙarin gashi, da mai yin zane a jiki da wacce ta nemi a yi mata.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi addu'ar tsinuwa da korewa da nisantarwa daga rahamar Allah - Maɗaukakin sarki - akan nau’uka huɗu: Na farko: Mai yin ƙarin gashin kanta ko ga waninta da wani gashin daban. Na biyu: Mai neman a yi mata ƙarin gashi da buƙatar waninta cewa ya yi mata ƙarin gashi da wani gashin daban. Na uku: Al-Washimah ita ce wacce take aikin kafa allura a wani wuri na jiki, kamar fuska ko tafi ko ƙirji, sai ta sa kwalli ko makamancinsa a cikinsa, har sai gurbinsa ya yi shuɗi, ko ya yi kore; dan neman ado da kuma kyau. Na huɗu: Al-Mustaushimah ita ce wacce take son a yi mata zanen. Waɗannan ayyukan suna daga cikin manyan zunubai.
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wanda yake da mata biyu sai ya karkata zuwa ɗayansu, zai zo ranar alƙiyama alhali ɓarin jikinsa a karkace".
Abu Dawud da Tirmizi da Nasa'i da Ibn Majah da Ahmad ne Suka Rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa wanda yake da sama da mace (ɗaya), bai yi adalci tsakanin matansa gwargwadon iko ba na daidaitawa tsakaninsu a ciyarwa da wurin zama da abin sawa da wurin kwana, cewa uƙubarsa a ranar alƙiyama ta kasance ne rabin jikinsa a karkace, kuma karkacewarsa uƙuba ce gare shi akan zalincinsa, kamar yadda ya karkata a cikin mu'amalarsa.
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Lallai Allah Ya ƙetarewa al'ummata abinda ta yi tunanin shi a zuciya, muddin dai bata aikata ba ko ta yi magana ba".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su abbata agare shi - ya bada labarin cewa musulmi ba'a kama shi da zancen zuci na sharri kafin ya aikata shi ko ya fade shi, yayin da Allah Ya ɗauke ƙunci kuma Ya yi afuwa, bai riƙi al'ummar (Annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da abinda aka samu a cikin tinani da kaikawo a cikin zuciya ba, tare da ya nutsu gare shi kuma ya tabbata a wurinsa ba; idan ya tabbata a cikin zuciyarsa kamar girman kai ko taƙama ko munafunci ko ya yi aiki da gaɓɓansa ko ya faɗa da harshensa to cewa shi za'a kamashi da hakan.
Daga Aliyu - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "An ɗauke alƙalami ga mutum uku: Mai Bacci har sai ya farka, da yaro har sai ya balaga, da kuma mahaukaci har sai ya yi hankali".
Abu Dawud da Tirmizi da Nasa'i cikin alkubra da Ibnu Majah haka kuma AhmadAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin Dora hukunci na (shari'a) wanda yake lazimtar 'ya'yan Adam ne sai waɗannan ukun: Ƙaramin yaro har sai ya girma ya balaga. Da mahaukaci wato mara hankali har sai hankalinsa ya dawo gare shi . Da mai bacci har sai ya farka. Ɗora shari'a haƙiƙa an ɗauke musu ita, kuma aikata laifinsu ba'a rubuta musu, sai dai ana rubuta alheri ga yaro ƙarami banda mahaukaci da mai bacci; domin su suna cikin wadanda ibadarsu ba ta inganta ba daga gare shi saboda gushewar ji.
Daga ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Dukkan abinda yake sa maye to giya ne, kuma dukkan abinda yake sa maye haramun ne, wanda ya sha giya a duniya sai ya mutu alhali shi yana mai dawwama a shan ta bai tubaba, to ba zai sha ta a lahira ba".
Muslim ne ya ruwaito shi, shi kuwa Bukhari ya ruwaito jimla ta karshe ne ta HadisinAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa dukkan abinda yake kawar da hankali kuma ya tafiyar da shi to shi giya ne mai sa maye daidai ne ya kasance sha ne ko ci ko shaƙa ko makamancin hakan, kuma dukkan abinda yake sa maye kuma ya kawar da hankali to haƙiƙa Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya haramta shi kuma Ya yi hani daga gare shi, ƙanƙaninsa da mai yawansa. Kuma dukkan wanda ya sha kowanne nau'i daga Nau’ukan waɗannan masu sa mayen, kuma ya lazimci shansu bai tuba ba daga gare su har ya mutu; to shi ya cancanci uƙubar Allah ta hanyar haramta masa shan ta a aljanna.
Daga Anas - Allah Ya yarda da shi - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Ku yaƙi mushrikai da dukiyoyinku da rayukanku da kuma harsunanku".
Abu Dawud da Nasa'i haka Ahmad suka ruwaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi umarni da yaƙar kafirai, da yin ƙoƙari a fuskantarsu ta kowace hanya gwargwadan iko dan kalmar Allah ta zama ita ce maɗaukakiya, daga hakan: Na farko: Ciyar da dukiya a yaƙarsu; na siyan makamai da ciyarwa ga mayaƙa da makamancin hakan. Na biyu: Fita da rai da jiki dan haɗuwa da su da kuma tunkuɗesu. Na uku: Da kiransu ga wannan Addinin da harshe, da tsaida hujja akansu, da tsawatar da su da yi musu raddi.
Daga Khuraim Dan Fatik - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Ayyuka shida ne, mutane kuma hudu ne, akwai tabbatattu biyu. Da tamka da tamka, da kyakkyawa da tamkarta goma, da kyakkyawa da dari bakwai. Amma masu tabbatattu biyu: Wanda ya mutu ba ya taranya wani abu da Allah zai shiga Aljanna. Wanda ya mutu yana taranya wani abu da Allah zai shiga wuta. Amma tamka da tamka: Wanda ya himmantu da kyakkyawa har ya jiyar da zuciyarsa ita, kuma Allah Ya santa daga gareshi za'a rubuta masa kyakkyawa, wanda ya aikata mummuna, za'a rubuta mummuna akansa. Wanda ya aikata kyakkyawa da tamkarta goma, wanda ya ciyar da wani abu a tafarkin Allah to kyakkyawa da dari bakwai. Amma mutane akwai wanda aka yalwatawa a duniya aka kuntata masa a lahira, da kuma wanda aka kuntatawa a duniya kuma aka yalwata masa a lahira, da wanda aka kuntatawa a duniya da lahira, da wanda aka yalwatawa a duniya da lahira".
Ahmad ne ya rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa ayyuka nau'uka shida ne, kuma mutane sinfi hudu ne. Ayyuka shidan su ne: Na farko: Wanda ya mutu alhali shi ba ya tarayya da wani abu ga Allah to Aljanna ta tabbata a gare shi. Na biyu: Wanda ya mutu alhali shi yana taranya wani abu da Allah wuta ta tabbata a gare shi yana madawwami a cikinta. Su ne tabbatattu guda biyu. Na uku: Kyakkyawa da aka niyyata, wanda ya yi niyyar aikata kyakkyawa kuma ya kasance mai gaskiya a cikin niyyarsa har sai ya jiyar da zuciyarsa hakan, kuma Allah Yana sanin wannan niyyar daga gare shi, sannan wani al'amari ya bijiro gareshi ba zai iya aikata wannan kyakkyawan ba za'a rubuta masa kyakkyawa cikakkiya. Na hudu: Mummuna da aka aikata. wanda ya aikata wata mummuna za'a rubuta masa mummuna daya. Su biyun: Tamka da tamka ne ba tare da ribanyawa ba. Na biyar: Kyakkyawar da take da goma irinta, ita ce wanda ya yi niyyar aikata kyakkyawa ya kuma aikatata; za'a rubuta masa kyakkyawa goma. Na shida: Kyakkyawar da take kasancewa da kaykkyawa dari bakwai, ita ce wanda ya ciyar da wata ciyarwa daya a tafarkin Allah sai a rubuta masa wannan kyakkyawar da kyakkyawa dari bakwai, wannan daga falalarSa ne - tsarki ya tabbara maSa Ya daukaka - da karamcinSa ga bayinSa. Amma sinfin mutane hudu, su ne: Na farko: Wanda aka yalwatawa a duniya daga arziki, aka ni'imtar da shi a cikinta yana samun abinda yake so a cikinta, saidai cewa shi abin kuntatawa ne a lahira kuma makomarsa ita ce wuta, shi ne kafiri mawadaci. Na biyu: Wanda aka kuntatawa a duniya daga arziki, saidai cewa abin yalwatawa ne a lahira, kuma makomarsa ita ce Aljanna, wannan shi ne mmumini talaka. Na uku: Wanda aka kuntatatawa a duniya da lahira, shi ne kafiri talaka. Na hudu: Wanda aka yalwatawa a duniya da lahira, shi ne mumini mawadaci.