





























Hadeeth Cards
Da'wa cards that highlight great meanings from the noble prophetic hadiths in a simple style and attractive display that helps the Muslim to have a deeper understanding of his religion in an easy way
All
Daga Abu Ayuba Al'ansary -Allah ya yarda dashi- zuwa ga Annabi: "Yin sammako ko yammaci don Allah shi ne mafi alheri: a cikin fitowar Rana da faduwarta". Daga Anas -Allah ya yarda dashi- zuwa ga Annabi: "Yin sammako ko yammaci don Allah: shi ne mafi alheri akan duniya da abin da ke cikinta".
Muslim ne ya rawaito shi - Bukhari da Muslim suka Rawaito shiWadannan hadisai biyu suna nuna mana falalar yin jihadi don Allah koda kuwa dan kadan ne gwargwadon lokacin safiya ko na yamma, ballantana kuma lokaci mai yawa wanda cikinsa akwai tsananin hakuri da gwagwarmaya da abokan gaba, wannan shi ake nufi da yi don Allah, watau yakar kafirai. Kuma ya kamata asan cewa neman ilmin sharia shina bangare ne mai girma na jihadi don Allah, hakanan taimakon gaskiya, hakanan ruguza hujjojin zindikai arna turawa yanmishan masu yakar musulumci masu son gani bayansa shi ne mafi girma cikin jihadi a tafarkin Allah. Manufar jihadi, shi ne bayyana Musulunci da taimaka masa, kuma dakushe arna, yana daga jihadi mai girma. Ya Allah ka datar da Musulmi a wajen taimakawa addininsu, da daukaka kalmarka. Kai ne Makusanci Mai amsawa.
Daga Zahdam Bn Muxrib Al-Jarmi ya ce: "Mun kasance tare da Abu Musa Al-ash'ari -Allah ya yarda da shi- sai ya ce akawo masa Daron abinci, cikinsa akawai Naman Kaza, sai wani Mutum Ja daga cikin Bani taimillahi ya zo, yayi kama da bayi, sai yace taho mu ci, sai Mutumin yaqi, sai yace da shi taho mu ci saboda naga manzon Allah SAW yana cin kaza"
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDaga Zahdam Bn Muxrib Al-Jarmi ya ce: "Mun kasance tare da Abu Musa Al-ash'ari -Allah ya yarda da shi- sai ya ce akawo masa Daron abinci, cikinsa akawai Naman Kaza, sai wani Mutum Ja daga cikin Bani taimillahi ya zo, yayi kama da bayi, sai yace taho mu ci, sai Mutumin yaqi, sai yace da shi taho mu ci saboda naga manzon Allah SAW yana cin kaza"
Daga Abdullahi ɗan Mas’ud - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Duk wanda ya rantse akan wata rantsuwa alhali shi yana fajiri a cikinta dan ya ci dukiyar wani mutum musulmi, to zai gamu da Allah alhali Shi yana Mai fushi akansa". ya ce: Sai Ash'As ya ce: Wallahi a kaina hakan ya kasance; ya kasance akwai wani fili tsakanina da wani mutum cikin Yahudawa, sai ya yi min musun filin, sai na kawo shi ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce dani: "Shin kana da shaidu?" Na ce: A'a. Ya ce: Sai ya cewa Bayaahudan: "Ka rantse". Ya ce: Na ce: Ya manzon Allah, to sai ya rantse ya tafi da dukiyata. Sai Allah - Maɗaukin sarki - ya ce: {Lallai ne wadanda suke musanya alkawarin Allah da rantse-rantsensu da wani farashi dan kadan}. har zuwa ƙarshen ayar,
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi gargaɗi daga yin rantsuwa tare da sanin mai rantsuwar cewa shi maƙaryaci ne a cikinta, dan ya ya karbi dukiyar waninsa; to zai gamu da Allah alhali Yana mai fushi da shi. Sai Ash'As ɗan Ƙais - Allah Ya yarda da shi - ya bada labarin cewa , Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya faɗi hakan lokacin da ya kasance akwai rigima ta mallakar wani fili tsakaninsa da wani mutum cikin Yahudawa, sai suka kai ƙara zuwa ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai ya cewa Ash'As: Wajibi ne ka zo da shaidun da suke tabbatar da abinda kake ƙararsa, idan ka kasa to baka da wani abu sai rantsuwar abokin rigimarka wanda ake ƙararsa, sai al-Ash'As ya ce: Ya manzon Allah, to bayahude zai rantse kuma ba ya taka tsantsan ya tafi da dukiya ta, sai Allah - Maɗaukakin sarki - Ya saukar da gasgata hakan a cikin Alƙur'ani a faɗinSa - tsarki ya tabbatar maSa -: {Lallai waɗanda suke musanya}. Suke canja {da alƙawarin Allah}, da wasiyyarSa ga muminai da dawo da amana {da rantse-rantsensu} da rantsuwarsu da sunanSa suna maƙaryata {ɗan kudi kaɗan} na rabon duniya {To waɗannan basu da wani rabo a lahira} kuma basu da wani nasibi {Kuma Allah ba Zai yi musu magana ba}, da zancen da zai faranta musu rai ya amfanar da su ba, kai ya yi fushi da su, {Kuma ba Zai kallesu ba a ranar alƙiyama} kallo na rahama da kyautatawa, {Kuma ba Zai tsarkakesu ba} da yabo mai kyau ba, kuma ba Zai tsarkakesu da gafara daga zunubai da datti ba {Kuma azaba mai raɗaɗi ta tabbata a garesu} mai sa ciwo saboda abinda suka aikata.
Daga rafi'u ɗan Khadij - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Mun kasance tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a Zul-hulaifa, sai yunwa ta kama mutane, sai suka samu raƙuma da tumakai, ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana cikin ƙarshen mutane, sai suka yi gaggawa, suka yanka, suka girka tukwane, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi umarni da tukwane, sai aka kifar da su, sannan ya raba, sai ya daidaita tumakai goma da raƙumi ɗaya sai wani raƙumi ya yi tsaurin kai, sai suka neme shi, sai ya gajiyar da su kuma a cikin mutanen dawakan kaɗan ne, sai wani mutum daga cikinsu ya sunkuyar da kibiya, sai Allah Ya tsare shi, sannan ya ce: "Lallai akwai halayyar daji ga wadannan dabbobin kamar dabbobin daji, wanda ya bijere muku daga cikinsu to ku yi haka da shi'. Sai ya ce: wato rafi'u: Lallai mu muna jin kwadayi - ko muna jin tsron - makiya gobe, kuma babu wuka a tare da mu, shin zamu yanka ne da kara? ya ce: "Duk abinda ya zubar da jini, kuma aka ambaci sunan Allah akansa to sai ku ci shi, banda hakori da farce, kuma zan zantar da ku game da haka: Amma a hakori to kashi ne, amma farce to wuƙar mutanen Habasha ce".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiRafi'i ɗan Khadij - Allah Ya yarda da shi - ya bada labarin cewa su sun kasance tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a Zul-Hulaifa, sai yunwa ta kama mutane, alhali sun samu ganimar raƙuma da tumakai daga mushrikai, sai suka yi gaggawa kafin raba ganima sai suka yanka wasu daga cikinsu, kuma suka kafa tukwane, ba tare da sun nemi izinin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ba, kuma (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana tafiya a cikin ƙarshen mutane, lokacin da (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya sani sai ya yi umarni da tukwanan, sai aka kifar da su da abinda ke cikinsu na miya, sannan ya raba ganimar a tsakaninsu, sai ya sanya goma daga cikin tumakai a madadin rakumi daya, sai wani rakumi ya gudu daga cikinsu, sai suka kasa kama shi, kuma dawakan sun kasance kada ne, sai wani mutum ya harbe shi da kibiya, sai Allah Ya tsare musu shi, sai (Annab) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Lallai akwai wasu ɗabi'u kamar ɗabi'un daji ga waɗannan dabbobin masu sabo, wanda ya rinjayeku daga cikinsu kuma kuka kasa kama shi to ku yi haka da shi. Sai Rafi'u ya ce: Lallai mu mana fatan fuskantar maƙiya gobe, kuma muna jin tsoron yankanmu ga dabbobin ya cutar da makamanmu alhali ana tsananin buƙatar yanka, kuma babu wuƙa a tare da mu, shin zamu yanka ne da busassun karare? Sai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Duk abinda ya zubar da jini kuma ya kwaranyar da shi da yawa, kuma aka ambaci sunan Allah a kansa to ku ci shi, banda haƙori da farce, kuma zan zantar daku game da hakan: Amma haƙori to ƙashi ne, amma farce to mutanen Habsha kafirai ne suke amfani da shi.
Daga Abu Huraira -Allah ya yarda da shi- zuwa ga Annabi: "Da wani mutum zai maka leken asiri ba da izinika ba, sai ka jefe shi da dutse, har ka cire masa ido: ba laifi yin hakan
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiAnnabi tsira da aminci su tabbata a gare shi ya bada labari cewa da wani zai leka gidan wani ta bayan kofa ko ta saman katanga ko makamanci hakan, sai ya jefe shi da dutse ko ya soke shi da wani karfe a ido, to ba wani abu na zunubi ko na kisasi; Don kuwa shi ya janyowa kansa.
Daga Abu Huraira -Allah ya yarda da shi- zuwa ga Annabi: "Ba wani wanda aka yi wa rauni a tafarkin Allah face sai ya zo Ranar Alkiyama, raunin nasa yana jini: kalarsa kalar jini, kanshinsa kuma kanshinalmiski
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiAnnabi tsira da amincin Allah yana bayyana mana falalar jihadi a tafarkin Allah Madaukaki da kuma irin abin da mai jihadi ke samu, na lada, cewa duk wanda aka yiwa rauni a tafarkin Allah ko an kashe shi ko ya warke, to zai zo Ranar kiyama gaban al'umma da damarar yaki, zai zo da ciwonsa danye, yana da launin jini kanshin Almiski.
Duk wanda ya rantse kan wata rantsuwada ya takure kansa da ita yana son karvar Dukiyar wani Musulmi, kuma a halin Qarya ya ke, zai gamu da Allah SWT yana fushi da shi
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDaga Abu Qatada Al-ansari -Allah ya yarda da shi- ya ce: Mun fita tare da Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - zuwa yakin Hunain- sai ya faxi Qissar sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Duk wanda ya kashe wani (a wajen yaqi) yana da kayansa da abun da yake tare da shi na ganima"
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiCewa Annabi - SAW- ya ce a ranar Hunain: Duk wanda ya kashe wanda sukai futo na futo kuma yana da Shaida ko Dalili, yana da ganima, wato yana da tufafi da makaman wanda aka kashe, da sulkensa da ya yi yaƙi da shi, da kuma cewa Abu Qatada ya kashe wani mutum, sai ya ce wa waɗanda suke kewaye da shi: Na kashe wani mutum, don haka ya yi rantsuwa Wanda ya san wannan dole ne ya ba da shaida a gare ni, ya faɗi hakan sau uku.
Daga Asma'u Yar Abubakar ta ce: "Mun yi yanka a lokacin Annabi Doki kuma Muka ci namansa" a wata Riwayar kuma "Kuma Mu muna Madina".
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiNana Asma'u tana Bada labarin cewa sun soke doki a lokacin Annabi kuma sun ci namansa, kuma cikin hakan akwai Dalilai kan Halaccin cin Naman doki kuma babu wanda zai kasa gane halacin hakan don kawai an hada ambatonsu da Jaki da Alfadari a ayar da take cewa: "Kuma doki da Alfadari da Jaki duk don ku haune kuma kuyi Ado kuma Allah yana halittar wasu Abubuwan da baku sani ba" [Annahl: 8].