





























Hadeeth Cards
Da'wa cards that highlight great meanings from the noble prophetic hadiths in a simple style and attractive display that helps the Muslim to have a deeper understanding of his religion in an easy way
All
Daga Huzaifa - Allah Ya yarda da shi - ya ce: "Na kasance tare da annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ya kai zuwa jujin wasu mutane, sai ya yi fitsari a tsaye, sai na yi nesa, sai ya ce: "ka kusanto" sai na kusanto har na tsaya daura da maƙyangymansa sai ya yi alwala sai ya yi shafa akan kuffinsa biyu.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiHuzaifa Dan Yaman - Allah Ya yarda da su - yana bada labarin cewa shi ya kasance tare da annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya so ya yi fitsari, sai ya shiga jujin wasu mutane; shi ne gurin da ake zubar da tsummokara da sharar da ake sharewa a cikin gidaje, sai ya yi fitsari alhali shi yana tsaye, ya kasance mafi yawancin al'adarsa shi ne ya yi fitsari a zaune. Sai Huzaifa ya yi nesa da shi, sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce masa: Ka kusanto, sai Huzaifa ya kusanto gare shi har ya tsaya a bayansa daura da ƙarshen diga-digansa; dan ya zama kamar kariya gare shi daga kallonsa a wannan halin. Sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya yi alwala, lokacin wanke ƙafafuwansa biyu, sai ya wadatu da shafa akan kuffinsa biyu - su ne abinda ake ɗaurawa a ƙafa na fata mara kauri da makamancinta kuma yana zama mai suturce idan sawu - kuma bai ciresu ba.
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi -: Cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya haɗu da shi a wata hanya cikin hanyoyin Madina alhali shi yana da janaba, sai ya sulale ya tafi ya yi wanka, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bibiye shi, lokacin da ya zo masa sai ya ce: «Ina kake ya Abu Huraira?» sai ya ce: Ya Manzon Allah ka haɗu da ni alhali ni ina da janaba sai na ƙyamaci in zauna da kai har sai na yi wanka, sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Tsarki ya tabbata ga Allah, lallai mumini ba ya zama najasa».
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya haɗu da Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - a sashin hanyoyin Madina, Abu Huraira ya kasance yana da janaba, kuma yana daga cikin girmamawarsa ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ƙyamaci zama da shi da kuma hira da shi alhali shi yana kan wannan halin dan yana zatan cewa shi najasa ne, sai ya tafi a ɓoye ya yi wanka, sannan ya dawo, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya tambaye shi ina ya tafi? Sai ya sanar da shi halin da yake ciki, kuma cewa shi ya ƙyamaci zama da shi ne alhali shi yana najasa saboda janabar (da ta same shi), sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi mamaki kuma ya ce masa: Lallai cewa mumini mai tsarki ne ba ya zama najasa akan kowane hali; a raye ko a mace.
Daga Nu'aman Dan Bashir zuwa ga Annabi: "Wallahi ko dai ku daidaita Sahunku ko kuma Allah ya saba tsakanin Fuskokinku" a wata Riwayar kuma: "Manzon Allah ya kasance yana daidaita sawunmu, har kace yana jera tukwane ne, har sai idan cewa yaga lallai mun fahimce shi, sannan ya fito wata rana sai ya tsaya, sai da ya kusa yayi kabbara, sai yaga wani Mutum ya turo kirjinsa waje, sai, Sai ya ce: kodai ku daidaita sahunku ko kuma Allah ya saba tsakanin fuskokinku"
Muslim ne ya rawaito shi - Bukhari da Muslim suka Rawaito shiAnnabi -Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi- ya tabbatar da cewa idan dai ba'a daidaita sahun Sallah ba to zai sassaba fuskokin wadan da sahun su ya karkace basu kuma daidaita shi ba, cewa lallai lokacin da wasu zasu wuce gaban wasu a sahu, kuma su bar kofofi a tsakaninsu, kuma Annabi -Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance yana koyar da sahabbansa da magana kuma ya shiryar da su da aiki, don ya tsaya yana daidaita su da Hannunsa, hai sai da Annabi ya tabbatar sun fahimci shi kuma sun koya, a cikin wata Sallah daga cikin Salloli sai yaga wani daga cikin Sahabbansa ya turo cikinsa a sahu a tsakanin Abokan Sallar sa sai Annabi yayi fushi kuma ya ce : " kodai ku daidaita Sahunku ko kuma Allah ya sassaba tsakanin fuskokinku".
Daga Abdullahi Dan Buhaina-Allah ya yarda da shi- ya kasance cikin sahabban Annabi -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- "Annabi -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi-yayi musu sallar Azahar sai ya mike daga raka'a biyun farko, bai yi zaman tahiya ba, si mutane suka mike tare da shi,har aka kammala salla, mutane suka jira sallamarsa: sai yayi kabbara yana daga zaune sai yayi sujjada guda biyu kafin yayi sallama,sannan sai yayi sallama".
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiAnnabi tsira da amincin Allah su tabbata agareshi yayiwa Sahabbansa Sallar Azahar,yayinda ya sallaci raka'oi biyun farko,sai ya tashi a bayansu,bai yi zaman Tahiya na farko ba,sai Mamu suka bishi a bisa hakan.Har sai da ya sallaci raka'o'i biyun karshe,kuma ya zauna don Tahiyar karshe,ya gama ta,Mutane suka jirayi sallamarsa,sai yai kabbara alhali yana cikin zamansa,sai yayi sajada dasu sajadu biyu kafin yayi sallama kwatankwacin sajadar cikin Salla,sannan yayi sallama.wannan sajadar ta kasance gyara ga Tahiyar da ya bari.
Daga Abdullahi Bn Abbas -Allah ya yarda da su- ya ce: "Na iso akan Jaka, kuma ni a lokacin na kusa Balaga, kuma Manzon Allah SAW yana Sallah da Mutane a Minna ba yana kallon Garu ba, na wuce ta gaban Sahu, sai na sauka, sai na saki Jakar tana kiwo, na shiga Sahu, babu wanda yai mun Inkarin hakan"
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDaga Abu Huraira-Allah ya yarda da shi- yace: Manzon Allah ya kasance in zai yi salla sai ya yi kabbara yayin da yake mikewa , sannan kuma yana yin kabbara yayin da yake yin ruku'u, sannan yana cewa-Allah ya ji mai gode masa, yayin da yake dago bayansa daga raka'a,sannan bayan ya mike yana cewa': ya Ubangijinmu a gare ka dukkanin godiya ta tabbata gare ka, sannan sai ya yi kabbara lokacin da yake tafiya zuwa sujjada, sannan sai ya yi kabbara liokacin sdago kansa daga sujjada, sannansai yayi kabbara yayin da yake yin sujjada, sannan sai yayi kabbara yayinda yake dago kansa, sannan sai ya aikata irin haka a cikin sallarsa dukanta har zuwa karshe, haka kuma yana yin kabbara yayin da yake mike wa daga tahiyar farko, sannan yace: "lallai nine na fiko iya kamant a sallar Manzo tsira da aminci su tabbata a gare shi"
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiSalla dukkaninta girmama Allah ne ta hanyar zance da aiki, acikin wannan hadisin madaukaki akwai bayanin shiar na salla, shine tabbatar da girma ga Allah madaukaki, babban abin da ya kara nuna girmanta shi ne shar'anta ta da aka yi don girmama Allah da daukaka shi. A lokacin da masallaci zai fara salla sai ya yi kabbarar harama yana tsaye ya daidaita.bayan ya gama karatu ya tafi zuwa ruku'u,sai yayi kabbar, idan ya dago daga ruku'u, sai yace: Allah ya ji mai gode masa ,sai ya mike sosai sai ya godewa Allah ya yabe shi a tsayen,sai ya sake kabbara don kai goshi sujjada, sannan sai ya yi kabbara yayin da yake dago kansa daga sujjada,sai ya aikata haka a cikin dukkan salarsa, har ya kammala,idan ya mike don ciko raka'oi biyu bayan tahiya ta farko sa i ya yi kabbara yayin da yake mikewa. kuma shari'a ta sanya yin kabbara a kowane guri sai dai a waje dagowa daga ruku'u
Daga Abdullah bin Omar, Abu Hurairah, da Abu Dharr - Allah ya yarda da su - a kan annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - cewa ya ce: “Idan zafin ya yi zafi sosai, ku yi sanyi tare da addu’a. Jahannama tana da zafi.
Buhari ne ya rawaito shi - Bukhari da Muslim suka Rawaito shiAnnabi mai tsira da amincin Allah ya wuce a kan jinkirta sallar azahar lokacin da zafi ya tsananta - wanda yake shi ne numfashi da hasken Wuta - har zuwa lokacin sanyi don kada zafin rana da bakin ciki su shagaltar da shi daga girmamawa.
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annbai - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Ku yi gaggawa da jana'iza, idan ta gari ce to alheri kuke kaita gare shi, idan kuma koma bayan haka ne, to sharri ne kuke sauke shi daga wuyayenku".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi umarni da yin gaggawa da shirya jana'iza da yi mata sallah da kuma binneta; idan jana'izar ta kasance ta garice to alheri ne, kuke gabatarwa gare shi na ni'imar ƙabari, idan kuma ta kasance koma bayan haka ne to sharri ne kuke saukewa daga wuyayenku.
Da hadisin Aisha Allah ya yarda da ita daga Manzon Allah tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi " Manzon Allah tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi ya yayi kautar Dabbobi wani lokaci:":
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiA’isha yardar Allah ta tabbata a gare ta, tana ba da labarin shiriyar Annabi - sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam - kuma shiriyar ita ce abin da dabbobin shanu suke ba wa Makka, don neman kusanci zuwa ga Allah - Tsarki da daukaka - a yanka shi a cikin Haram, kuma shiriyar zuwa Makka shekara ce da sadaukarwa. Allah ya tabbata a gare shi - tunkiya, kuma ya ba da rakumi, kamar yadda sunna ta yanka shi a cikin Harami don maslahar Allah - mai girma da daukaka -, kuma ana rarraba shi ga matalauta da mabukata: mabukatan Harami, game da hadayar da ta wajabta jin dadi, Alkur'ani, ko wani abu da yake sakaci da ayyuka, ko aikata haramtattun abubuwa, ana kiransa fansa kuma yana Hadaya farilla ce Amma game da wannan hadayar da A'isha ta ambata, kyauta ce da mumini ya ba da kansa daga ƙasarsa, ko kuma ya saye ta daga hanya ya ba ta can a matsayin kyauta daga Ka'aba mai kusantar Allah - ɗaukaka da ɗaukaka