





























Hadeeth Cards
Da'wa cards that highlight great meanings from the noble prophetic hadiths in a simple style and attractive display that helps the Muslim to have a deeper understanding of his religion in an easy way
All
Daga Abihurairata Allah ya kara yarda a gareshi ya ce: { Manzon Allah mai tsira da aminchi yayi mana daya daga cikin sallolin isha guda biyu- ibnu sirin ya ce haka Abu hurairata ya ambace su.saidai ni na manta- ya ce sai yayi mana sallah raka`ah biyu, sa`annan yayi sallama .sai ya tashi izuwa wata itaciya da ta fito a cikin masallachin, sai ya kishingida akan wannan itaciya kamar yana cikin fushi sai ya dora hannun sa na dama akan na hagu, sai ya saqa tsakanin yan yatsun sa.sai suka ce: an rage raka`o`in salla ne? a cikin mutanen akwai Abubakar da Umar sai suks ji nauyin yimasa magana. kuma a cikin su akwai wani mutum mai tsawon hannu, ana kiransa zulyadaini sai ya ce: ya manzon Allah, kayi mantuwa ne? ko kuma sallar ta ragu ne? sai ya ce: ban manta ba kuma ba`a rage ba. sai ya ce da su: shin abinda zulyadaini ya fada haka ne? sai suka ce eh, haka ne: sai ya shiga gaba ya sallaci abinda ya bari sai yayi sallama, sa`annan yayi kabbara yayi sujjada kwatankwacin sujjadar sa ko sama da haka . sa`annan ya daga kansa yayi kabbara sannan ya kuma yin kabbara yayi sujjada kwatankwacin sujjadarsa ko sama da haka sa`annan ya dago kansa yayi kabbara sau da yawa suna tambayar sa:sa
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiMaazanni sune mafi cikar hankalin Mutane, kuma sune mafi tabbatar zukata, kuma sune mafi tsayuwa da hakkin Allah, amma duk da hakan basu futa daga iyakar Mutane ba, Mazon allah shi ne mafi cikar sifofi, kuma duk da haka wani lokaci Mantuwa takan bujuro masa, sabida kasancewa dan adam ne, kuma Abu huraira ya rawaito cewa Annabi yayi sallah da sahabbansa kodai Sallar azahar ko kuma La'asar kuma cewa Abu Huraira ya fade ta amma kuma Dan Sereen ya manta ta, yayin da yayi Sallah Raka'a biyu na farko sai ya yi Sallama, kuma yayin da ya kasance Annabi Mutum ne cikakke, ransa ba zai nutsu ba sai da cikakken aiki, sai yaji a jikinsa cewa akwai tawaya da kuma wani abu bai cika ba, kuma baisan mai ya jawo shi ba, sai ya tashi zuwa wani ita cce da aka ajiye a gaban alkiblar Masallacin kuma ya kashingida a kansa ransa yana sosuwa, kuma ya hade yan yatsunsa, kuma masu saurin futa daga Masallaci suka futa suna ganawa a tsakaninsu, cewa wani abu ya faru fa, shi ne an rage Sallah, kamar sunji nauyin Annabi ne cewa yaya zai yi kamarsa yayi mantuwa, kuma sabida kwarjininsa a zukatansu babu wanda ya iya bugar kirji da ya tambaye shi akan wannan Mai muhimmanci, cikin wadanda suke wurin har da Abubakar da Umar -Allah ya yarda da su, Musamman daman sun lura da damuwarsa da kuma kebancewarsa, sai dai wani Mutum daga cikin Sahabbai ana kiran Zulyadainshi ya yanke wannan shiru din, ta hanayar tambayarsa Annabi da cewa: Ya Manzon Allah wai Mantawa kayi ne? domin babu wanda ya iya tambaya kowanne ya yanke cewa wannan hakan zai iya faruwa, sai Annabi ya ce: yana mai gini zatonsa, ba'a rage ba kuma ba mantawa nayi ba, sai Annabi yai nufin ya tabbatar da ingancin abinda zulyadaini yake fada, domin ya sabawa zaton sa na cewa Sallar ta cika ko bata cika ba ne abinda zai rinjayar da fadinsa, sai ya ce ga wadanda suke gefensa na Sahabbansa: Haka yake abinda Zulyadain yake fada raka'a biyu kawai nayi? sai suka ce: Ey a lokacin sannan Annabi ya shige gaba ya kawo abinda ya bari na ragowar sallar, kuma bayan yayi tahiya sai yayi sallama sannan yayi Kabbara kuma yana zaune, kuma yayi Sujada kwatankwacin sujadar ainahin Sallah ko mafi tsawo daga ita, sannan ya dago kansa sannan yayi kabbara, sannan ya kuma yin kabbara kuma yayi sujada kwatankwacin sujada ko mafi tsawonta, sannan ya kuma dago kansa kuma yayi kabbara, sannan yayi sallama kuma bai tahiya ba.
Daga Sale Dan Khauwat Dan Jubair -Allah ya yarda da shi- daga wanda yayi sallar tsoro tare da Annabi a ranar yakin Zaturriqa'a:cewa: wani yanki suka yi sahu tare da Annabi, wani bangaren ya fuskanci abokan gaba,sai ya jagoranci wanda suka yi sahu tare da shi suka sallaci raka'a daya,sannan ya tsaya kyam,su kuma suka cika sallar,sannan suka juya suka fuskanci abokan gaba,su kuma wadancan suka zo,suka sallaci raka'ar da ta rage,tare da Annabi tsira da amincin Allah-,sai ya zauna,su kuma suka ciko raka'ar da ta rage musu, sai Annabi yayi sallama suma suka yi.
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiAnnabi -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- ya je wani yaki tare da sahabbansa yawancinsu a kasa suke,sai suka gaji har suka nannada yanki a kafafuwansu, duk da dai ba'a yi yakin ba, musulmi ne suka tsorata abokan gabarsu, to a wannan hadisin abokan gab a ba'a bangaren Alkibla suke ba,saboda gidajensu suna gabas da Madina,sai Annabi ya kasa su kashi biyu,wasu suka yi sahu tare da shi,wasu kuma suka fuskanci abokan gaba wadanda masu salla suka juya musu baya,sai Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya sallaci raka'a daya tare da sahun farko,sai suka ciko raka'a daya suka yi sallama,sannan suka je suka fuskanci abokan gaba,shi kuma ya tsaya a tsaye, har wadancan masu fuskantar abokan gaba suka zo, ya sallaci raka'ar da ta rage tare da su, sai yayi zamansa suka mike suka ciko raka'a daya,sannan yayi sallama suma suka yi.Jama'ar farko sun dace da samun kabbarar harama tare da liman,ita kuma ta biyu ta dace da samun sallama tare da liman,kuma abokan gaba basu sami dama ba,sahabbai kuma sun samu daidaito wajen samun falalar jam'in.
A kan Al-Bara 'bin Azib - Allah ya yarda da shi - ya ce: "Annabi - Salatin Allah da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya yi magana da mu a ranar Idin layya bayan salla, sai ya ce: Duk wanda ya yi sallolinmu da ibadunmu ibadunmu, kuma duk wanda ya gabatar da ibada kafin salla, to bai kamata mu kiyaye ta ba. Abu Burda bin Nayyar - kawun mahaifin Al-Baraa bin Azeb - ya ce: Ya Manzon Allah, na yi shiru da hirata kafin na yi salla, kuma na san cewa yau rana ce ta ci da sha. Ya ce: Hirar ku ita ce ragon nama. Ya ce: Ya Manzon Allah, lalle ne mu, muna da runguma a kanmu, wadanda suka fi soyuwa a gare ni fiye da tumaki biyu. Za ku ba ni lada? Ya ce: Ee, kuma ba za a ba ka lada a bayanka ba.
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiA kan Sahl bin Saad - yardar Allah ta tabbata a gare shi - cewa wata mata ta zo wajan Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - tare da alkyabba mai suttura.ta ce nayi ta ne da hannuna sai Manzon ya karveta yana mai bukatarta sai ya futo mana wani lokaci ya daure da ita sai wani Mutum ya ce ka bani ita banga abu mafi kyawunta! ba Ya ce: "To." Don haka Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya zauna a cikin majalisin, sannan ya dawo ya ninke ta sannan ya aika masa da ita, sai mutanen suka ce masa: baka kyauta ba Annabi - SAW- ya sanya ta cikin buqata, sai ka tambaye shi kuma kasan cewa bai hana wanda ya tambaye shi, sai ya ce: Wallahi ban nemi ya bani badon insanya, amma ni natambaye shi ne don ta zama likkafanina na. Sahl ya ce: ita ce Likafaninsa.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi Kwatankwacin saDaga Abdullahi Dan Umar - Allah ya yarda da shi - zuwa ga Annabi : ""lallai Annabi ya Hana siyar da Walittaka ko kyautarta
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiAn rawaito daga Abu Huraira -Allah ya yarda da shi- cewa wani balaraben kauye yazo sai ya ce: ya Manzon Allah, "Lallai cewa matata ta haifi Bakin Yaro, sai Annabi ya ce Kana da Rakuma? sai ya ce E, sai ya ce yaya launukansu yake? sai yace: jajaye sai yace shin cikinta akwai wadanda yasha banban da su? ya ce: E lallai cikinsu akwai wadanda suka sha baban, ya ce: to ta yaya aka samu hakan? ya ce: To watakila ya gado jini ne, yace wannan ma watakila ya ya gado jini ne"
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiAn karbo daga Sa'ad Dan Abi Wakkas-Allah ya yarda da shi-yace:Manzan Allah-tsira da amincin Allah su tabbata agareshi-yazo min don ya dubani shekarar Hajjin ban-kwana daga wani ciwo da yayi tsanani agareni,sai nace:Ya Ma'aikin Allah,hakika ciwo yakai inda yakai agareni kamar yadda kake gani,kuma ni Ma'abocin Dukiya ne,bamai gadona sai 'ya mace bana yi Sadaka da Biyu bisa Ukun Dukiyata ba?yace:a'a,nace:Rabi fa ya Ma'aikin Allah?yace:a'a,nace:Daya bisa Ukufa?yace:Daya bisa Uku,kuma Daya bisa Uku da yawa,hakika cewa kai kabar Magadanka Mawadata shi yafi akan kabarsu Talakawa suna rokon Mutane,kuma cewa kai ba zaka ciyar da wata ciyarwa ba kana mai neman Fuskar Allah face Allah ya baka lada da ita,hatta abinda zaka saka a Bakin Matarka.Yace:Nace ya Ma'aikin Allah zan barwa abokanaina a bayana?yace:Hakika cewa kai ba za'a barka ba ka aikata wani aiki da kake neman Fuskar Allah sai ka kara Daraja dashi da Daukaka,kuma watakila kuma idan aka barka har wasu su amfana da kai wasu kuma su cutu da kai,ya Allah ka cikawa Abokanaina Hijirarsu,kada ka juyar dasu a bayansu,sai dai sadauki shine Sa'ad Dan Khaula(Manzan Allah-tsira da amincin Allah su tabbata agareshi-yana yi masa Rasa'i don ya Rasu a Makka)
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiSa'ad Dan Abi Wakkas Allah ya yarda dashi yayi rashin lafiya lokacin Hajjin ban kwana rashin lafiya maitsanani wacce saboda tsananinta yaji tsoran Mutuwa Sai Manzan Allah tsira da amincin Allah su tabbata agareshi ya duba shi kamar yadda al'adarsa take cikin bibiyar Sahabansa da jajantawa a garesu Sai Sa'ad ya ambatawa Annabi tsira da amincin Allah su tabbata agareshi damuwoyinsa, abinda ya kudira na cewa zai Sadaka da dukan Dukiyarsa, sai yace: Ya Ma'aikin Allah, hakika ciwo mai tsanani yayi tsanani agareni wanda nake jin tsoran Mutuwa daga gareshi, kuma ni ma'abocin Dukiya mai yawa ne, kuma cewa shi babu daga Magada Raunana wadanda nake tsoran talauci da tozarta a kansu face 'yata Guda daya, to bayan wannan shin na iya Sadaka da Biyu bisa Uku na Dukiyata, don na gabatar dashi ga managarcin aikina? sai Annabi tsira da amincin Allah su tabbata agareshi yace: a'a Yace: Rabi fa ya Ma'aikin Allah? yace: a'a yace: Daya bisa uku fa? sai yace: ba abinda zai hanaka Sadaka da Daya bisa uku duk da cewa mai yawa ne Domin cewa saukowa izuwa abinda yake koma bayansa na daga Daya bisa Hudu ko Daya bisa biyar shi yafi Sannan Annabi tsira da amincin Allah su tabbata agareshi ya bayyana masa Hikima cikin saukowa cikin Sadaka da mafi yawan Dukiya izuwa mafi karancinta da lamari Biyu: 1. shine cewa shi in ya mutu alhali ya bar Magadansa Mawadata masu amfani da Nagartarsa da Dukiyarsa to hakan shi yafi akan ya fitar dashi daga garesu izuwa waninsu, ya barsu suna rayuwa abisa kyautayin Mutane. 2. ko kuma a wanzar dashi ya sami Dukiyarsa, sai ya ciyar da ita ta hanyoyin da Shari'a ta shara'anta, kuma ya nemi lada awajan Allah sai a saka masa abisa hakan, har acikin abinda yake mafi wajabcin ciyarwa akansa shine abinda zai ciyar da Matarsa Sannan Sa'ad Dan Abi Wakkas yaji tsoran ya mutu a Maka wacce yayi Hijira daga gareta ya kuma barta saboda Allah Madaukaki, sai yin hakan ya tauye masa wani abu daga sakamakon Hijirarsa, sai Annabi tsira da amincin Allah su tabbata agareshi ya bashi Labari cewa ba za'a barshi bisa dole a cikin Garin da yayi Hijira daga gareshi ba, sannan yayi wani aiki acikinsa don neman ladan Allah face ya kara Daraja da shi, sannan Annabi tsira da abincin Allah su tabbata agareshi yayi masa Bushara da abinda yake nuni da cewa zai warke daga ciwonsa, Allah ya amfani Muminai dashi, ya kuma cutar da Kafirai dashi,sai hakan ta kasance kamar yadda Mai Gaskiya abin Gasgatawa ya bada labari, sai ya warke daga rashinlafiyarsa, kuma ya zama Jagora mafi Girma acikin yakin Farisawa, kuma Allah ya amfani Musulunci da Musulmai dashi, yayi Bude Bude kuma Allah ya cutar da Shirka da Mushirikai dashi, sannan Annabi tsira da amincin Allah su tabbata agareshi ya yiwa Sahabbansa Addu'a cewa ya tabbatar musu da Darajarsu, ya kuma karbeta daga garesu, kuma kada suyi Ridda a cikin Addininsu ko kuma kar ya mayar dasu Garin da suka yi Hijira daga gareshi, sai Allah ya karbi hakan daga gareshi, Godiya da Baiwa tasa ce, kuma dukkan Godiya ta tabbata ga Allah wanda ya Daukaka Musulunci dasu Sannan ya ambaci Sa'ad Dan khaula,shi yana cikin masu kaura wadanda sukayi kaura daga Maka sai dai Allah ya kaddara cewa zai mutu acikinta, sai ya mutu kuwa acikin nata, sai Annabi tsira da amincin Allah su tabbata agareshi yayi masa Rasa'i: ana nufin: bai ji masa dadi ba saboda ya mutu a Maka; hakika sun kasance suna ki ga wanda yayi Hijira ya mutu a Kasar da yayi Hijira daga gareta.
Daga Ibnu Abbas - Allah Ya yarda da su - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Ku riskar da (kason gado) ta hanyar farillai ga ma'abotansu, abin da ya rage to namiji makusanci shi ne ya fi cancantarsa ».
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiAnnabi -tsira da aminci su tabbata a gare shi- ya umarci masu raba gado da su raba wa waɗanda suka cancanci rabon bisa adalci kamar yadda sharia ta yi bayani, kamar yadda Allah Yake nufi, sai a baiwa magada abin da Allah ya kaddarawa kowa a cikin Littafinsa, shi ne biyu cikin uku, da ɗaya cikin uku, da ɗaya cikin shida, da Rabi, da ɗaya cikin huɗu, da ɗaya cikin takwas. Abin da ya yi saura bayan wannan, to sai a baiwa mafi kusanci ga mamacin daga cikin maza; su ake kira Asubai.