





























Hadeeth Cards
Da'wa cards that highlight great meanings from the noble prophetic hadiths in a simple style and attractive display that helps the Muslim to have a deeper understanding of his religion in an easy way
All
Daga Aliyu ɗan Abu Ɗalib - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya riƙe alhariri da hagunsa, kuma zinare da damansa, sannan ya ɗaga hannayensa da su, sai ya ce: "Lallai waɗannan biyun haramun ne ga mazan al'ummata, kuma halal ne ga matansu".
Abu Dawud da Nasa'i da ibn Majah ne Suka Rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya riƙe wani tufafi na alhariri ko wani yanki daga gare shi, da hannunsa na hagu, kuma ya riƙe zinariya ta ado ko mai kama da ita, da hannunsa na dama, sannan ya ce: Lallai alhariri da zinariya, sanya su haramun ne akan maza, amma mata to su halal ne garesu.
Daga Anas Dan Malik - Allah ya yarda da shi - ya ce " Mun kasance tare da Annabi - Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi- a cikin wata tafiya a cikinmu wasu suna Azumi , wasu kuma basa yi, ya ce gida gida a cikin rana mai zafi, kuma muka yawaita shiga Inuwa Ma'abocin Gwado, a cikinmu wani yana kare Rana da Hannunsa, ya ce sai masu Azumi suka fara faduwa, kuma sai Marasa Azumin suka tashi suka kafa musu shema kuma suka rika bawa tawagar ruwa, Sai Manzon Allah ya ce: "nnabi _ Tsira da Amincin Allah ya yarda da shi - Ya hana Sabi Zarce a Azumi sai suka ce : Cewa ai kaima kana yi sai ya ce: cewa ni ai ba irinku bane , ni ai ana ciyar da ni kuma ana shayar da ni
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiSahabbai sun kasance tare da Annabi a wata tafiya tasa, wasunsu basa Azumi wasu kuma suna yi kuma Annabi ya tabbatar da kowa matsayin da yake kai sai suka a wata rana mai zabi don su huta daga wahalar tafiya da zafin rana, yayin da suka sauka a wannan zafin rana, sai masu Azumi suka fara faduwa sabida da zafin rana da kuma kishirwa basu iya aikata komai ba, sai marasa Azumi suka tashi suka kafamusu shema suka shayar da Rakuma kuma suka yi wa Masu Azumi Hidima, to Yayin da Annabi yaga aikinsu da hidimar da suke na iwa Runduna sain ya karfafa musu a kuma ya fadi falalarsu, kuma ya ce: "Masu Buda baki sun tafi da lada
Daga Abdullahi Dan aid Dan Asim ya ce: yayin da Allah ya kwaranyo Arziki ga Manzonsa a ranar yakin Hunain; sai ya rabawa Mutane, haka ga wadanda ake janyo hankalinsu zuwa Musulunci, kuma bai bawa Mutanen Madina komai ba, kamar wani abu ya dan sosa musu rai; don bai basu komai ba kamar yadda ya bawa Mutane, sai yayi Huduba yana mai cewa: Ya ku mutanen Madina, Ban sameku Batattu ba sai kuma Allah ya shiryar da ku da ni? kuma kun kasance kan ku a rarrabe sai kuma ya hada kanku dani ? kuma kuna talakawa sai Allah ya Azutaku sabida ni? ko yaushe yace wani abu sai su ce Allah da Manzonsa sune mafi baiwa a gare mu, sai ya ce Mai ya hanaku ku Amsawa Manzon Allah? sai suka ce: Allah da Manzonsa sune mafi baiwa a gare mu, sai ya ce: da kun so da kunce ka zo mana abu da kaza da abu kaza yanzu baku yarda ba Mutane su tafi da Azuya da Rakumi, ku kuma ku tafi da Manzon Allah cikin tawagarku? Ba don Ladan Hijira ba da na zamanto daya daga cikin Mutanen Madina, kuma da ace Muta ne zasu bi wani kwari ko lungu, ni da nabi kwarinda Mutanen Madina suka haka ma lungun da suka bi don nuna don goyon bayansu, kuma Mutane zasu buya lallai cewa ku zaku gamu da tuntube bayana, to kuyi hakuri har ku gamu dani a tafkin Alkausara.
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiYayin da Allah yai budi ga Manonsa na ganimomi masu yawa a yakin Hunain kuma bayan ya bar takunkumin da ya sanywa Ta'if kuma sai ya dawo mata da wasu ganimomi kuma maf yawan su Dabbobi ne kuma sun kai sama da Rakumi Dubu arba'in da da Dari da Ashirin na Dabbobisai Annabi ya bawa wasu Mutane sababbin shiga Musulunci don ya jawo hankalinsusai wasu daga cikin Mutanen Madina abun bai musu dadi ba amma manyan cikin su sun san ewa yadda Annabi yayi shi gaskiya yayin da Maganar su ta isar masa lokacin da wasu suka ce Annabi ya badaganima ga Mutanen da takubbunan mu suke digar jini daga yakarsu sannan ya kyale mu sai Annabi yayi umarnin da a tara su a wani wuri da ake kira kubba sai suka taru sai ya ce musu ya isarmun maganganun wasunku. har zuwa karshen abinda suka ce sai yai musu fada kuma sannan ya yi ikirari gare su abinda suka gabatar masa na taimako da kuma taimakonsu ga Musulunci da ya zo da shi sai ransu yayi dadi kuma suka san abu mai girma da Allah ya tanadar musu na zama da Annabinsa, da kuma dawowarsu tare da shi cikin tawagarsu, bugu da kari da abinda ya tanadar musu na ladan lahirasabida abinda suka gabatar na bajinta, sai Annabi ya Umarce suda hakuri akan abinda zai same su bayansa na juya musu baya. Taisir (306) tanbih Al'afham(3/403) Ta'asis Al'ahkam 93/197
Daga Abu Sa'id -Allah ya yarda da shi- cewa Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi cewa ya kasance yanayin E'itikafi a goman tsakiya na Ramalana wata shekara sai yai E'itikafi har sai da ranar Ashirin da daya ta o wacce ita ce rananar da yake futowa a safiyarta daga E'itikafin sa ya ce: "Duk wanda ai yi E'itikafi tare da ni to yayi a goman karshe, to hakika an nunamun wannan daren sannan kuma aka manatar da ni ita, kuma na ganni ina Sujada a ikin Ruwa da tabo a Asubar ta, to ku neme ta a goman karshe kuma ku neme ta a Mara na kowawane dare kuma Masallacin ya kasance rufin arbar dabino ne , to sai Masallacin yayi ta zuba to naga -Manzon Allah- da idanuna goshinsa alamar ruwa da tabo a Asubar ranar Ashirin da daya.
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiAbu Sa'id Al'khudri yana bada labari cewa Annabi ya kasance yana yin I'itikafin goman tsakiya na Azumi don neman daren lailatul kadari, sai wata shekara yayi -kamar yadda ya saba- har sai da adaren Ashirin da daya, ita ce ranar da yake futowa a safiyarta daga I'itikafinsa, sai ya san cewa lallai daren lailatul kadari tana goman karshe, sai yace da Sahabbansa: Duk wanda yayi I'itikafi tare da ni goman tsakiya, to ya zarce da I'itikafinsa, yayi a goman karshe, kuma ya bada labarin cewa Allah yanuna masa ita a Mafarkinsa sannan ya mantar da shi ita, sai dai ya ce kamar yagani a barcin wasu alamominta a cikin wannan shekarar su ne: Sujadarsa a cikin sallar Asuba akan tabo mai ruwa, to Allah ya gasgata Mafarkin Annabinsa, sai akayi ruwa a daren Ashirin da daya kuma ya kasance Masallacinsa an gina shi ne da yayin danga, kuma kututtudabino shi ne ginshikansa kuma rufinsa na ganyen Dabino ne, to sai Masallacin yayi ta zubar ruwa, sai Annabi yayi Sujada a safiyar Ashirin da daya, a cikin ruwa da tabo, Taisir Allam (349) Tanbih Al'afham (3/472) Ta'asis Al'ahkam 3/292
Daga Jabir ɗan Abdullah -Allah Ya yarda da su -, ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance a wata tafiya, sai ya ga cunkoso da wani mutum an yi masa inuwa, sai ya ce: «Menene wannan», sai suka ce: Mai azimi ne, sai ya ce: «Azimi a halin tafiya bai zama daga aikin alheri ba». A cikin wani lafazin na Muslim: «Na horeku da rangwamin da Allah Ya yi muku».
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiManzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance a cikin wata tafiya, sai ya ga wani mutum mutane sun haɗu a kansa alhali an yi masa inuwa saboda zafin rana da tsananin ƙishirwa, sai ya ce: Me ya same shi ? sai suka ce: Mai azimi ne, sai ya ce: Azimi a halin tafiya bai zama daga cikin ayyukan alheri ba, na horeku da rangwamin da Allah Yayi muku.
Daga Abu Addarda'i -Allah ya yarda da shi- Mun fito tare da Manon Allah -Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi- a cikin watan Azumin Ramalan, cikin wani matsanancin zafin rana, har sai da takai dayanmu yana dora hannunsa akan sa sabida tsananin zafin Rana kuma cikinmu babu mai Azumi sai Manzon Allah in Tsira da Amincin \Allah su tabbata a gare shi-da kuma Abdullahi Dan Rawaha
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiAbu Al-dardaa yana bada labari _ Allah yarda da shi- cewa sun futo a lokacin wata tafiya a cikin watan Ramalana, kuma ranar ta kasance mai tsananin zafi ce, har ya kai cewa sabida tsananin afinta dayan su yana dora hannunsa a kansa don ya kare rana mai tsanani, kuma duka cikinsu babu Mai Azumi sai Annabi -Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi , da kuma Abdullahi Dan Rawaha Al-ansari - Allah ya yarda da shi hakika su biyun sun jure tsananin kuma sunyi Azumin wanda wannan yana nuna halascin yin Aumi a tafiya duk da wahalar da take ciki wacce batakai matsayin wacce zata kai hallaka ba .Taisir Al-allam (shafi27) Tabih Al-afham (Mujalladi 3/432) Ta'asisu Al-ahkam3/241).
Daga Abu Huraira - Allah ya yarda da shi -:zuwa ga Annabi : "Babu komai na Zakka akan Musulmi cikin dokinsa "
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiAngina Zakka ne kan daidaito da kuma Adalci, don haka Allah ya wajabta ta cikin Dukiyoyin Mawadata kuma wacce take karuwa da kuma wacce aka tanada don juyawa, kamar abubuwan da suke futa daga cikin Kasa, da kayan siyarwa, kuma Dukiyar da bata Karuwa, wacce aka tanada don ajiya da Amfani to wannan babu zakka acikinta; don kebantarwar Musulmi don bukatar kansa: kuma kamar Abun Hawansa, Kamar Doki, da Rakumi, da Mota, kuma haka bawansa da ya tanada don yi masa Hidima da shimfidar sa da kwanuka da aka tanada don amfani sai dai antogace Zakkar fidda kai, to lallai cewa Ta wajaba kuma koda ba'a tanadi ta ba don kasuwanci, domin suna danfare da jiki ba da Dukiya ba.
Daga Abdullahi Dan Umar - Allah ya yarda da shi - zuwa ga Annabi : "nnabi _ Tsira da Amincin Allah ya yarda da shi - Ya hana Sabi Zarce a Azumi sai suka ce : Cewa ai kaima kana yi sai ya ce: cewa ni ai ba irinku bane , ni ai ana ciyar da ni kuma ana shayar da ni"
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiAnnabi -Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi- ya hana Sahabban sa sabi zarce a cikin Azumi don jin kai a gare su da kuma tausaya musu sai dai Sahabbai saboda sonsu da aikin Alkairi da duk abinda zai kusanta su zuwa ga Allah shi yasa suke kwadayi sabi zarce dincikin Azumi don koyi da Annabi kasancewar sa yana yi don haka suka ce: Ai kaima kanayi sai ya basu labari da cewa yana da wanda yake ciyar da shi kuma ya ke Shayar da shi da abinda zai maye gurbin abinci da shi, to duk wanda yake son yayi to yayi zuwa lokacin Suhur to ita Shari'ar Musulunci Mai sauki ce Mai sauki ce babu wahala a cikinta, kuma ba bu shige da kutsa kai cikin abunda bai sani ba domin cikin wannan akwai Azabtar da kai da bawa kai wahala, kuma Allah bai dorawa rai ba sai abunda zata iya yi, kuma saukakawa da rangwantawa yafi sa aiki ya dawwama kuma yafi sanya aiki kubuta daga gajiyawa da kosawa kuma cikin hakan akwai Adalci wanda shi Allah yasanya a bayan Kasa, kuma shi ne abawa Allah hakkinsa da ya nema na Ibada, da kuma bawa rai bukatar ta na kashin kanta.
Daga Muhammad Dan Abbad Dan Ja'afar Ya ce: "Na Tamabayi Jabir Dan Abdullahi: "ai dace ga mace ba tayi Imani da Allah da Ranar Lahira tayi Tafiyar wuni da Kwana ba tare da Maharramunta ba"
Al-Nasa'i Ya Rawaito shi - Bukhari da Muslim suka Rawaito shiYayin Da Jumu'a ta Kasance Ranar idi ga Musulmi, Sharia ta hana kebance jumua da azumi ko tsayiwar dare, sai dai yayi Azumi kafinta ko bayanta ko kuma yakasance cikin Azumin da ya saba, don kada jahilan Mutane suma su keban ce Ranar jumu'a da kara wata Ibada ba ta Hanyar Sharia ba.