





























Hadeeth Cards
Da'wa cards that highlight great meanings from the noble prophetic hadiths in a simple style and attractive display that helps the Muslim to have a deeper understanding of his religion in an easy way
All
Daga Jabir ɗan Abdullah -Allah Ya yarda da su -, ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana koya mana Istikhara a cikin al'amura kamar yadda yake koya mana sura daga Alƙur'ani, yana cewa: «Idan ɗayanku ya yi niyyar yin wani al'amari to ya yi (sallah) raka'a biyu ba ta farilla ba, sannan ya ce: Ya Allah ni ina neman zaɓinKa da saninKa, kuma ina neman ikonKa da ikonKa, ina roƙonKa daga falalarKa mai girma, domin cewa Kai Kana da iko ni ba ni da iko, kuma Kana sani ni kuma bani da sani, kaine Masanin abinda ke ɓoye, ya Allah idan Kasan cewa wannan al'amarin alheri ne a cikin Addinina, da rayuwata da ƙarshen al'amarina» ko cewa ya yi: "Magaggaucin al'amarina da kuma majirkincinsa, to ka kaddara mini shi kuma ka sawwaka mini shi sannan Ka yi albarka gareni a cikinsa, idan kuma Kasan cewa wannan al'amarin sharri ne gareni a cikin Addinina da rayuwata da karshemn al'amarina" ko cewa ya yi: "A cikin magaggaucin al'amarina da majirkincinsa, to ka kawar da shi daga gareni ka kawar da ni daga gare shi, kuma Ka kaddara mini alheri a duk inda yake, sannan Ka yarda da ni" Ya ce: "Sai ya ambaci buƙatarsa».
Bukhari ne ya rawaito shiIdan musulmi ya yi nufin aikata wani al'amari daga abinda bai san ina ne daidai a cikinsa ba, to an shara'anta masa ya yi sallar Istikhara yadda Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana koyawa sahabbansa - Allah Ya yarda da su - wannan sallar kamar yadda yake koya musu sura daga Alƙur'ani, sai ya yi sallah raka'a biyu ba ta farilla ba, sannan ya roƙi Allah yana mai cewa: «Ya Allah ni ina neman zaɓinKa» da neman dacewa da zaɓin al'amura biyu, kuma ina roƙonKa «da saninKa» mayalwaci wanda ya kewaye kowane abu, «ina neman ikonKa» Ka sanya ni mai iko inda babu wata dabara gareni kuma babu wani ƙarfi sai naKa «Da ikonKa» mai zarcewa Kai wani abu ba ya gajiyar da Kai, «Ina roƙonKa daga falalarKa» da kyautatawarKa «mai girma» mayalwaciya; yadda kyautarKa falala ce daga gareKa, kuma babu wani haƙƙi a cikin ni'ima ga wani a kanKa; «domin cewa Kai Kana da iko» akan dukkan komai, ni kuma mai rauni ne gajiyayye «bani da iko» akan wani abu sai da taimako daga gareKa, «Kai» "kana sani" da saninKa mai tattarowa mai kewayewa da zahiri da kuma badini, da alheri da kuma sharri, "ni" "bana sani" wani abu sai da dacewarKa da kuma shiryarwarKa, "Kai ne Masanin abinda ke boye" ilimi kai tsaye naKa ne, da iko mai zarcewa, babu haka ga waninKa sai dai abinda ka kaddara masa da kuma abinda Ka ba shi iko akansa. Sannan musulmi ya roƙi Ubangijinsa, ya ambaci buƙatarsa sai ya ce: «Ya Allah» ni na fawwala al'amarina gareKa «idan Kasan cewa» a cikin saninKa cewa wannan al'amarin «sai ya ambaci buƙatarsa» kamar siyan wannan gidan, ko a cikin siyan wannan motar, ko a cikin auren wannan matar mo wanin hakan... Idan wannan al'amarin ya kasance ya rigaya a cikin saninKa cewa a cikinsa «alheri ne a cikin Addini na» wanda shi ne igiyar al'amarina, «da rayuwata» a cikin duniyata «da ƙarshen al'amarina» da abinda al'amarina yake komawa zuwa gare shi, ko ca ya yi: «a cikin magaggaucin al'amarina da majinkircinsa» a duniya da lahira; «to Ka ƙaddara mini shi» Ka tanade shi Ka zartar da shi «gareni», kuma ka sawwaƙe shi «Ka sawwaƙe shi gareni», «sannan Ka yi albarka» kuma Ka yawaita alheri «gareni a cikinsa», «idan kuma Ka sani» ya Allah «cewa wannan al'amarin» wanda na baka zaɓi a kansa «sharri ne gareni a cikin Addini na da rayuwata da karshen al'amarina - ko cewa ya yi : A cikin magaggaucin al'amarina da majinkircinsa - to Ka juyar da shi daga gareni nima ka juyar da ni daga gare shi , kuma Ka kaddara mini alheri a duk inda yake, sanann Ka yardar da ni da shi" da ma dukkan hukuncinKa daga abinda ka so da kabinda nake so da kuma abinda nake ki».
Daga Abu Sa'idul Khudri - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Ya Abu Sa'id, wanda ya yarda da Allah a matsayin Ubangiji, da Musulunci a matsayin Addini, da (Annabi) Muhammad a matsayin Annabi, aljanna ta wajaba a gare shi», sai Abu Sa'id ya yi mamaki gareta (wannan maganar), sai ya ce: Ka maimaitata mini ya Manzon Allah, sai ya maimaita, sannan ya ce: «Ɗayar kuwa za'a ɗaukakawa bawa daraja ɗari da ita a cikin aljanna, tsakanin kowace daraja biyu kamar tsakanin sama da ƙasa ne». Ya ce: Waccece ya Manzon Allah? Ya ce: «Jihadi a tafarkin Allah, jihadi a tafarkin Allah».
Muslim ne ya rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bawa Abu Sa'idul Khudri - Allah Ya yarda da shi - labarin cewa wanda ya yi imani da Allah kuma ya yarda da Shi a matsayin Ubangiji abin bauta kuma shugaba kuma mai umarni, kuma da Musulunci a matsayin Addini dan jawuwa da miƙa wuya da dukkanin umarce-umarcensa da hane-hanensa, da kuma (Annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a matsayin Annabi da dukkan abinda aka aiko shi da shi kuma ya isar da shi; to aljanna ta tabbata gareshi, sai Abu Sa'id - Allah Ya yarda da shi - ya yi mamaki ga (wannan maganar), sai ya ce: Ka maimaita mini ita ya Manzon Allah, sai ya aikata, sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Kuma ina da wata dabi'ar daban wacce Allah Yake daukaka darajar bawa da ita sau dari a cikin aljanna, tsakanin kowace darajoji biyu kamar tsakanin sama da kasa ne, Abu Sa'ida ya ce: Waccece ya Manzon Allah? ya ce: Jihadi a tafarkin Allah, jihhadi a tafarkin Allah.
Daga Abu Sa'id Alkhudr - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- yana cewa: "Wanda ya yi azumin wani yini a tafarkin Allah, Allah Zai nisantar da fuskarsa daga wuta (tsawon) shekara saba'in".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa wanda ya azumci wani yini a yaƙi, an ce a yaƙi da waninsa yana mai ikhlasi ga Allah dan neman sakamako da lada daga Allah; to lallai Allah da falalarsa Zai nisantar da tsakaninsa da tsakanin wuta (tsawon) shekara saba'in.
Daga Sahl ɗan Sa'ad - Allah Ya yarda da shi - lallai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Mutane ba zasu gushe ba cikin alheri matuƙar sun gaggauta buɗa baki".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa mutane ba za su gushe ba a cikin alheri muddin dai sun gaggauta buɗa baki a azimi, bayan tabbatar da faɗuwar rana; hakan dan ruko da sunna, da tsayuwa a iyakarta.
Daga Abu Sa'id Alkhudr - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Mun kasance muna fitar da zakkar fidda kai lokacin da Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana cikinmu, daga kowane ƙaramin (yaro) da babba, ɗa ne ko bawa, Sa’i na abinci, ko Sa’i na cukwi, ko Sa’i na sha'ir, ko Sa’i na dabino, ko Sa’i na zabibi, kuma bamu gushe ba muna fitar da shi har saida Mu'awiya ɗan Abu Sufyan - Allah Ya yarda da shi - ya gabato gurinmu yana mai aikin Hajji, ko yana mai Umarah sai ya yi wa mutane magana akan minbari, ya kasance daga abinda ya yi wa mutane magana da shi cewa ya ce: Lallai ni na ga cewa mudu biyu na alkamar Sham, sun yi daidai da sa'i ɗaya na dabino, sai mutane suka yi riko da hakan, Abu sa'id ya ce: Ammma ni ba zan gushe ba ina fitar da shi kamar yadda na kasance ina fitar da shi, muddin dai na rayu har abada.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiMusulmai sun kasance suna fitar da zakkar fidda kai Sa’i ɗaya na abinci a zamanin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da zamanin Khalifofi masu shiryarwa a bayansa daga ƙaramin (yaro) da babba. Abin cin su ya kasance sha'ir ne da (zabibi): Bushasshen inibi, da (cukwi): Busasshen nono da kuma dabino. Gwargwadan Sa’i mudu huɗu ne, mudu kuma ya yi daidai da cikin tafi biyu na namiji madaidaici (ba babba ba ba kuma ƙarami ba). Lokacin da Mu'awiya - Allah Ya yarda da shi - ya zo Madina alhali shi yana Khalifa, kuma alkamar Sham ta yi yawa, sai ya yi huɗuba sai ya ce: Lallai ni ina ganin cewa mudu biyu na alkamar Sham (rabin Sa’i), sun yi daidai da Sa’i ɗaya na dabino, sai mutane suka yi riƙo da hakan. Abu Sa'idul Khudri - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Amma ni ba zan gushe ba ina fitar da shi kamar yadda na kasance ina fitar da shi a zamanin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi har abada muddin dai ina raye.
Daga Zaidu ɗan Sabit - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Mun yi sahur tare da Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sannan ya tashi zuwa sallah, na ce: Nawa ne tsakanin kiran sallah da sahur? ya ce: Gwargwadan ayoyi hamsin.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiWasu daga sahabbai - Allah Ya yarda da su - sun yi sahur tare da Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya tashi zuwa sallar Asuba. Sai Anas ya cewa Zaid ɗan Sabit - Allah Ya yarda da shi -: Nawane gwargwadan lokaci sahur tsakanin kiran sallah da iƙama? Sai Zaid ɗan Sabit - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Gwargwadan karanta ayoyi hamsin ne matsakaita, ba dogwaye ba ba kuma gajeru ba, ba karatu da gaggawa ba ba kuma a hankali ba.
Daga Nana A'isha Uwar muminai - Allah Ya yarda da ita - matar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: Cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana i'itikafin goman ƙarshe na Ramadan, har Ya koma ga Allah , sannan matansa suka yi i'itikafi a bayansa.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiNana A'isha uwar muminai - Allah Ya yarda da ita - ta bada labarin cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya lazimci i'itikafi a goman ƙarshe na Ramadan, dan neman Lailatul Qadr, kuma ya zarce akan hakan har zuwa lokacin da Allah Ya ɗauki ransa, haƙiƙa matansa - Allah Ya yarda da su - sun lazimci i'itikafi a bayansa.
Daga Anas ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Ku yi sahur, domin lallai cewa akawai albarka a cikin sahur".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kwaɗaitar akan sahur shi ne cin (abin ci) a ƙarshen dare dan yin tanadi ga azimi; domin cewa a cikinsa akwai (albarka) alheri mai yawa na lada da sakamako, da tashi a ƙarshen dare dan addu'a, da ƙarfafuwa akan azimi, da nishaɗuwa gare shi, da kuma sauƙaƙa wahalarsa.
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Kada ku gabaci Ramadan da azimin yini ko yini biyu sai dai mutumin da ya kasance yana yin wani azimi to ya azimce shi".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya hana musulmi ya yi azimi kafin Ramadan da yini ɗaya ko yini biyu akan niyyar lissafa shi a (watan) Ramadan; domin wajabacin azimin Ramadan an rataya shi ne da ganin jinjirin wata, babu buƙatuwa ga ɗorawa kai, sai dai wani wanda ya kasance yana yin wani azimin da ya sabayi kamar azimin yini da fashin yini (irin na annabi Dawud), ko ranar litinin ko alhamis sai ya yi daidai da shi to ya azimce shi; wannan bai zamo daga tarbar Ramadan a wani abu ba, an riskar da hakan abinda ya kasance azimi ne na wajibi kamar ramuwa da bakance.