





























Hadeeth Cards
Da'wa cards that highlight great meanings from the noble prophetic hadiths in a simple style and attractive display that helps the Muslim to have a deeper understanding of his religion in an easy way
All
An karbo daga A`isha -Allah ya kara yarda a gareta- ta ce: Manzon Allah mai tsira da aminci su kara tabbata a gareshi ya kasance {yana bude salla da kabbara. da karatu, da fadar Alhamdu lillahi rabbil aalamina, ya kasance idan yayi ruku`u baya dago kansa, ba kuma ya mikar da shi saidai tsaka tsaki, ya kasance idan ya dago kansa daga ruku`i baya yin sujjada, har sai ya daidaita a tsaye, ya kuma kasance idan ya dago kansa daga sujjada, baya kuma sujjada har sai ya daidaita a zaune, ya kasance yana yin tahiya a bayan kowace raka`a biyu, ya kasance yana shimfida kafar sa ta hagu ya kuma kafe kafar sa ta dama, ya kasance yana yin hani gameda irin zaman shaidan. sa`annan yana yin hani mutum ya shimfida hannayen sa guda biyu irin shimfidawar zaki, ya kasance yana rufe sallar da yin sallama}.
Muslim ne ya rawaito shiAisha -Allah ya kara yarda a gareta- tana siffanta sallar annabi mai tsira da aminci su kara tabbata a garesh i-da wannan hadisin mai girma- saboda yada sunna da isar da wannan ilimi, ya kasance cewa yana bude sallar da kabbarar harama, sai ya ce: (Allahu akbar) yana kuma bude karatu da karatun fatiha, wadda farkon ta tana farawa da (Alhamdu lillahi rabbil aalamin) ya kasance idan yayi ruku`u bayan tsayuwa, baya daga kansa ba kuma ya sunkuyar da shi, kawai dai yana yana sanya shi a mike dai-dai. ya kasance idan ya dago daga ruku`u sai ya kafe a tsaye kafin yayi sujjada ya kasance idan ya dago kansa daga sujjada, baya yin wata sujjadar sai ya dai-daita a zaune ya asance yana fada a bayan kowace raka`a biyu idan ya zauna: ''Attahiyyatu lillahi wassalawatu har zuwa karshe'' ya kasance idan ya zauna sai ya shimfida kafar sa ta hagu sai ya zauna a kanta, ya kuma kafe kafar sa ta dama ya kasance yana hana mai yin salla da ya yi zama a cikin sallar sa irin zaman shaidan, ta yadda zai shimfida kafafuwan sa akan kasa bayan kafafuwan nasa kuma suna kan kasa, ya zauna a karshen dunduniyar sa guda biyu, ko kuma ya kafe kafafuwan sa guda biyu, sa`annan ya sanya mazaunan sa a tsakankanin su akan kasa, kamar yadda yake hana mai yin salla da ya shimfida hannuwan sa guda biyu a cikin sujjada kamar yadda zaki ke shimfida hannuwan sa biyu, kuma kamar yadda ya bude sallar da girmama Allah tare da yin kabbara, yana rufe ta da yin sallama bisa wadanda su ke tare da shi daga mala`iku da masu salla sa`annan bisa dukkan bayin Allah na kwarai, da na farko da na karshe, ya zama wajibi kan mai yin salla da ya lura da wannan gamewa a cikin addu`ar sa.
An rawaito daga Anas -Allah yayarda da shi- cewa shi ya ce da Sabit -Allah ya yi masa rahama: bana yo maka Rukya ba da rukyar Manzon Allah -Amincin Allah a gareshi-? ya ce E , yace: "Ya Ubangiji Mai renon Mutane, mai tafiyar da cuta, ka warkar kaine mai warkawa, babu mai warakarwa sai kai, warakarwar da bata barin cuta"
Buhari ne ya rawaito shiLallai cewa Anas Bn Malik -Allah ya yarda da shi- ya kirawo Sabit Al-Bunani kuma ya ce da shi bana yi maka Ruqya ba da Ruqyar Manzon Allah SAW ya kasance yana roqon Ubagijinsa ga Mara lafiya kan ya yayewa mara lafiyar tsananinsa da raxaxinsa kuma ya sanya shi waraka da babu wata Waraka bayanta, kuma Malamai sun haxu kan halacin Ruqya idan ta haxa abubuwa uku: 1- ta kasance da zancen Allah aka yi ta ko sunayensa ko Siffofinsa, 2-kuma ta kasance da Yaren Larabci ko kuma da abunda za'a iya gane Ma'anarsa, kuma anso ta Kasance da Lafazan da suka zo a cikin Hadisisai 3-kuma mai yin Ruqya xin ya qudurce cewa Ruqyarsa ba ba zatayi tasiri ba ita kaxai sai da qudurar Allah SWT
An rawaito daga Abu Huraira -Allah ya yarda da shi- daga Annabi: "Kada xayanku ya kusura yayi Sallah da tufa xaya, babu komai a Kafaxunsa"
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiCewa Manzon Allah SAW ya kasance idan zai kabbara yana xaga Hannayensa har sai sunkai daidai Kunnuwansa, kuma idan yayi ruku'u yana xaga Hannayensa har sukai daidai kunnuwansa
Muslim ne ya rawaito shiMalik bin Al-Hawith, Allah ya kara yarda a gare shi, yana fada cewa Annabi - Salati da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance: "Ya kasance yana daga hannayensa har su zama daidai da kunnuwansa." Wato: Idan ya kara takbilar Ihram, sai ya daga hannayensa har sai ya daidaita su, kuma a wata ruwaya: Kunnuwansa. " Kuma rassan kunne: saman. Kuma a cikin hadisin Ibnu Umar - Allah ya yarda da shi - cewa: "Ya kasance yana daga hannayensa har ya daidaita kafadunsa da su," ma'ana akasin haka kuma daidai yake da kafadunsa. Wadannan ruwayoyi guda uku ne: Na farko: Yana daga hannayensa har kunnuwansa zasu daidaita dasu. Na biyu: Yana daga hannayensa har sai rassan kunnensa sun daidaita da su. Na uku: Yana daga hannayensa har sai ya daidaita kafadunsa dasu. An ba shi zabi tsakanin wancan, ko kuma ya daga hannayensa sama a kan kafadun domin yatsun yatsun sahu su daidaita rassan kunnuwan sa, watau saman kunnuwan sa, manyan yatsun sa, murfin kunnuwan sa, da tafin hannun sa a kafadun sa. Da kuma fadinsa: "Idan ya girma, sai ya daga hannayensa," ma'ana: Yana daga hannayensa lokacin da yake yin takbeer. Kuma a cikin wata ruwaya kamar yadda Muslim ya ruwaito: "Yana daga hannayensa, sa'annan ya ce takbeer," ma'ana a bayansa, a wani kuma: "Yana cewa takbeer, sannan ya daga hannayensa." Wadannan su ne hotuna uku na daga hannaye yayin yin takbilar. A kan wannan: Wannan Sunnar za a ambace ta ne ta hanyoyi daban-daban, kuma za a bi ta duka daidai da Sunna a cikin duk abin da aka ambata game da ita - da fatan Allah Ya yi mini albarka ...
Daga Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce: "Ana yanke hannu a rubu'un dinari (ɗaya bisa huɗu) zuwa sama".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa ɓarawo ana yanke hannunsa saboda satar rubu'in dinari na zinare, da abinda ya ƙaru a kan hakan, kuma ya yi daidai da abinda ƙimarsa ta yi daidai da ƙimar 1.06 Gram na zinari.
Daga Abu Burda - al-Ansari - Allah Ya yarda da shi - cewa shi ya ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: "Ba'a yi wa wani mutum bulala sama da goma sai a haddi daga cikin haddodin Allah"
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi hani a yi wa wani bulala sama da bulala goma sai dai a cikin saɓo, ba wai ana nufin cewa abinda ya zo a cikinsa na iyakance adadi daga mai shara'antawa na bulala ko duka ko uƙuba keɓantacciya ba, abin nufi ba'a yin ƙari a cikin bulalar ladabtarwa akan bulala goma, kamar yi wa mata bulala ko ɗa.
Daga Ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Wanda ya riƙi wani kare saidai karen farauta ko kiwo ƙiradi biyu zai ragu daga aikinsa kowace rana", Salim ya ce: Abu Huraira ya kasance yana cewa: "Ko karen noma", kuma ya kasance manomi ne.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi gargaɗi daga riƙon karnuka, saidai dan buƙatar farauta, ko gadin dabbobi da shuka, wanda ya riƙe kare ga wanin haka kowace rana ƙiraɗi biyu zai ragu daga ladan aikinsa; kuma shi wani gwargwado ne sananne a wurin Allah - Maɗaukakin sarki -.
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi -: Cewa Annabi-tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -ya shiga masallaci, sai wani mutum ya shigo, sai ya yi sallah, sannan (ya zo) ya yi sallama ga Annabi-tsira da amincin Allah su tabbata agare shi-sai ya amsa masa kuma ya ce: Koma ka yi sallah domin cewa kai baka yi sallah ba", sai ya koma ya yi sallah kamar yadda ya yi sallar, sannan ya zo ya yi sallama ga-Annabi tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ya ce: "Koma ka yi sallah, domin cewa kai baka yi sallah ba" sau uku, sai ya ce: Na rantse da wanda ya aikoka da gaskiya ba zan iya yin wacce ta fita ba, to ka koya mini, sai ya ce: "Idan ka tashi zuwa sallah to ka yi kabbara, sannan ka karanta abinda ya sawwaka tare da kai na Alkur'ani, sannan ka yi ruku'u har sai ka natsu kana mai ruku'u, sannan ka dago har sai ka daidaita a tsaye, sannan ka yi sujjada har sai ka natsu kana mai sujjada, sannan ka dago har sai ka natsu a zaune, kuma ka aikata hakan acikin sallarka gaba dayanta".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya shiga masallaci, sai wani mutum ya shigo a bayansa sai ya yi sallah raka'a biyu da gaggawa, bai nutsu a cikin tsayuwarsa da ruku'unsa da sujjadarsa ba, Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana lura da shi a cikin sallarsa, sai ya zo wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a lokacin Ma’aikin Allah yana zaune a gefen masallaci sai ya yi masa sallama, sai ya amsa masa sallamar, kuma ya ce masa: Ka koma ka sake sallarka, domin kai baka yi sallah ba. Sai ya dawo yana sallah da gaggawa kamar yadda ya yi sallar, sannan ya zo sai ya yi sallama ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai ya ce masa: Ka koma ka yi sallah; domin kai baka yi sallah ba, ya aikata haka sau uku. Sai mutumin ya ce: Na rantse da wanda Ya aikoka da gaskiya, ba zan iya yin wacce tafi wannan ba to ka koya mini, sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Idan ka tashi zuwa sallah to ka yi kabbarar harama, sannan ka karanta Fatiha da kuma abinda Allah Ya so ka karanta, sannan ka yi ruku'u har sai ka natsu kana mai ruku'u, shi ne ka sanya tafukanka biyu akan gwiwoyinka sai ka miƙar da bayanka ka tabbata dan yin ruku'inka, sannan ka ɗago ka daidaita bayanka har sai ƙasusuwa sun koma mararrabarsu kuma ka daidaita a tsaye, sannan ka yi sujjada har sai ka natsu kana mai sujjada, shi ne ka tabbatar da goshi tare da hanci, da hannaye da gwiwoyi da geffan diga-digai akan ƙasa, sannan ka ɗago har sai ka natsu kana zaune tsakanin sujjada biyu, sannan ka aikata hakan a kowace raka'a ta sallarka.
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi -: Lallai cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Idan bawa musulmi ya yi alwala - ko kuma mumini - sai ya wanke fuskar sa, to kowane kuskuren da ya yi kallo da shi da idanun sa zai fice daga fuskar sa tare da ruwa - ko kuma tare da ƙarshen ɗigon ruwa - idan ya wanke hannayen sa, kowane kuskure zai fita daga hannayen sa waɗanda hannayen sa suka damƙa tare da ruwa - ko tare da ƙarshen ɗigon ruwa -, idan ya wanke ƙafafuwan sa kowane kuskuren da ƙafafuwan sa suka tafi gare shi zasu fita tare da ruwa - ko tare da ƙarshen ɗigon ruwa - har sai ya fita tsarkakakke daga zunubai".
Muslim ne ya rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa idan musulmi ko mumini ya yi alwala sai ya wanke fuskarsa a cikin alwalar duk ƙaramin kuskuren da ya kalla da idanuwansa zai fita daga fuskarsa tare da ruwan da ya zuba bayan wankewar ko tare da ƙarshen ɗigon ruwan, idan ya wanke hannayensa kowane ƙaramin kuskuren da hannayensa suka aikata shi zai fita daga hannayensa tare da ruwan ko tare da ƙarshen ɗigon ruwan, idan ya wanke ƙafafuwansa kowane ƙaramin kuskuren da ƙafafuwansa suka taka (zuwa gare shi) zai fita tare da ruwan ko tare da ƙarshen ɗigon ruwan har sai ya fita tsarkakke daga ƙananan zunubai idan ya gama alwalar.