





























Hadeeth Cards
Da'wa cards that highlight great meanings from the noble prophetic hadiths in a simple style and attractive display that helps the Muslim to have a deeper understanding of his religion in an easy way
All
Daga Zaid Dan Khalid Aljuhani -Allah ya yarda da shi- "An tambayi Annabi game da tsintuwar zinare da azurfa? sai ya ce: Ka sanar dabuhunta da kuma madaurinsa, sannan kayi shela shekara, idan ba'a samu mai ita ba sai ka yi sadaka da ita, kuma ta amanto ajiya ce a wurinka to idan Mai ita yazo wata rana; sai ka biyashi" kuma an tambaye shi game da tsintuwar Rakumi sai ya ce: "Mai ya hada da ita? ka barta sabida tana da takalminta da ruwanta, tana iya shan ruwa kuma taci bishiya har mai ita ya sami abarsa, kuma aka tambaye shi game da tsintuwar Akuya sai ya ce: "ka dauketa; domin kodai ta zama rabonka ko na Dan uwanka ko kuma na kura"
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiWani Mutum ya tambayi Annabi game da hukuncin Dukiyar da ta bata daga Mai ita ta zinare da Azurfa da kuma Rakuma da Dabbobi, sai Annabi ya bayyana Hukunci wadan nan abubuwa don su zamanto misali ga sauran abubuwan da suka yi kama da su, na Dukiyoyin da suka bata, sai su Dauki Hukuncinsu, sai ya ce game da Zinare da Azurfa: Ka yi bayanin abinda aka daure ta shi da kuma gidan da aka saka ta a cikinsa, don mai ita ya iya gane ta, sai kuma ka Jarraba duk wanda ya ce tasa ce don ka gane gaskiyarsa, to idan abin da ya fada ya dace da abinda yake hakika sai ka bashi abarsa, in ba haka kuma ba bai dace da hakikanin yadda take ba, to zai ci gaba da cigiya har tsawon shekara daga tsintuwar, kuma zai rika yi a wurin taron mutane, kamar Kasuwanni, da kofofin Masallatai, da wuraren taruwar Jama'a, da kuma inda ya tsinceta, sannan an halatta masa bayan cigiyarsa tsawon shekara, ba'a samu mai ita ba to yayi Sadaka da ita amma idan mai ita ya zo a kowane lokaci komai tsawonsa to ya bashi abarsa, amma batanccen Rakumi da Mai kama da shi wanda zai iya kare kansa, to an hana tsintuwarsa, domin baya bukatar kariya, a Dabi'arta tana da kariyar kanta, don tana da karfin kare kanta daga kana nan Dabbobi, kuma tana takonta da zata iya zuwa ko ina, da wuyanta da zaya iya yin kiwo daga bishiya da kuma ruwa, kuma tana da tankin da zata iya ajiye abinci a cikinta, kuma tana iya kare kanta har mai ita ya same tawanda yake ta nemanta daga inda ta bata, kuma amma batattun akuyoyi da masu kama da su na daga kananan Dabbobi, to an umarci a tsince su kada su Hallaka ko kuma kuraye su cinye su, kuma bayan tsintar u mai u zai zo ya karbi abinsa, ko kuma su zauna tsawon shekara ana cigiya sai ta zama ta wanda take hannunsa.
Daga Aisha Allah ya yarda da ita- tace: "Saad Dan Abi Wakkas sun yi fada da shi da Abdu Bin Zam'ata game da wani yaro: Sa'ad yace: Ya Manzon Allah wannan Dan'uwa na ne Utbata Dan Abi Wakkas, ya yi daawar cewa yaron nan dansa ne, kalli kamanninsa.sai Abdu Dan Zam'ata yace: ya Manzon Allah wannan Dan'uwana ne,an haife shi akan shimfidar Baba na ne yana daga 'ya'yansa.sai Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kalli kamanninsa sai yaga kamanceceniya da Utbata a fili, sai yace: Danka ne ya kai Abdu Dan Zam'ata, Da na uwarsa ne, kwarto kuma sai dutse,ki nesance shi ke Saudatu.Daga nan bai kuma ganin Saudatu ba".
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiSun kasance suna dorawa bayi mata haraji, harajin da suke biyansa ta hanyar fajirci, kuma suna iya baiwa wanda ya yi zinar da su dan in ya nemi hakan. Sai Utbata Dan Abi Wakkas yayi lalata da baiwar Zam'ata Dan Al'aswad, sai baiwayr ta zo da yaron, sai Utbata yayi wasici ga Dan'uwansa Sa'ad da ya riskar da yaron zuwa ga kanshi. Bayan an yi Fatahu Makka, da Sa'ad ya ga yaron sai ya gane shi saboda kama da yayi da Dan'uwansa, sai yaso ya riskar da shi da Dan'uwansa, sai suka yi husuma da shi Abdu Dan Zam'ata, sai Sa'ad ya kawo hujjarsa inda yake cewa: Lallai Dan'uwansa ya tabbatar da cewa dansa ne,kuma ga kamanni nan ma, sai Abdu Dan Zam'ata yace: shi Dan'uwa na ne, Da ne daga cikin 'ya'yan Baba na, yana nufin: Babansa shi ne Uban gidan baiwar da ta haifi yaron, kuma shi ne mamallakin baiwar. Sai Annabi ya kalli yaron, sai yaga sunyi kama da Utbata. Sai ya yanke hukuncin Da na Uwarsa ne, mazinaci kuma ya yi asara, ba shi da alaka da yaron; saboda asali zai bi wanda ya mallaki uwar ne kuma ya take ta ta hanya ingattacciya, duk da haka da Annabi yaga kamamnin yaron da utbata wajen Dan
An rawaito daga Al-minhal Sayar Bn Salama ya ce: (Na shiga ni da Babana ga Abu baraza Al-aslami, sai ya ce da shi yaya Annabi SAW yake Sallar farilla? sai ya ce: ya Kasance yana Sallar Azahar -wacce suke kiranta ta farko- lokacin da Rana ta karya, kuma yana Sallatar La'asar sannan dayan mu ya dawo zuwa Masaukinsa a karshen Madina Rana tana nan, na manta abunda ya ce a Magriba, kuma ya Kasance yana son ya jinkirta Isha wacce muke kiranta Al-atama, kuma ya kasance yana kin ayi bacci kafinta, da kuma yin Magana Bayanta kuma ya kasance yana yana tafiya daga Sallar Asuba lokacin da Mutum zai iya gane na kusa da shi, kuma ya kasance yana Karanta Aya Sttin zuwa Dari.
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiAbu Barzah -Allah ya yarda da shi- ya fadi lokutan Sallar Farilla, Sai ya fara da cewa shi Annabi SAW ya Kasance yana Sallar Azahar, lokacin da Rana ta Karkata daga daga tsakiyar Sama zuwa Yamma, kuma wannan shi ne farkon lokacinta, kuma yana Sallar La'asar, sannan daya daga Masallatan ya dawo gidan sa a mafi nisan wuri daga Madina kuma Rana bata gushe ba tana nan, wannan shi ne farkon lokacinta, amma Magriba Mai riwayar ya manta abunda ya zo cikinta, kuma Nassoshi sun nuna haka Ijma'in Malamai kan cewa farkon lokacin ta da faduwar Rana, kuma Manzon Allah ya Kasance yana son ya jinkirta Isha, Saboda lokacinta wanda ya fi shi ne a Sallaceta a karshen lokacinta Na Mukhtari, kuma ya Kasance yana kin ayi Bacci kafinta don tsoron ya jinkirta ta daga lokacinta Mukhtari ko ya rasa Jam'i, da kuma tsoron bacci ya cimmasa da kuma barin Sallar dare kuma yana kin yin Hira bayanta saboda tsoron makara ga barin Sallar Asuba, ko rasa Sallar jam'i, Kamar yadda yana tafiya bayan Sallar Asuba, a lokacin da Mutum yana iya gane waye yake zaune a gefensa, tare da cewa zai Karanta a cikin sallarsa Aya Sittin zuwa dari, daga cikin abunda ya ke nuna cewa shi yana Sallatarta da duku duku.
Daga Anas -Allah ya yarda da shi- yace:"Annabi -tsira da amincin Allah- yahana namiji ya shafa Za'afaran"
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiAnnabi SAW ya hana ma ya Kasance Mutum ya rina jikinsa ko kayansa da da Za'afaran, kuma saboda yana daga cikin Turaren Mata, sai ya hana Maza yin hakan saboda hana Kamanceceniya da su
An rawaito daga Ali Bn Abi Dali -Allah ya yarda da shi- zuwa ga Annabi: "Babu wani Sauran Maraici bayan Balaga, ko kuma hakurin wuni zuwa dare"
Abu Daud Ya Rawaito shiNa farko: ba'a daukar Mutumin da ya balaga Maraya Na biyu: Sun kasance a lokacin Jahiliyya suna bautawa Allah -Mai girma da daukaka- da yin shiru, sai ya zauna wuni guda yayi shiru baya Magana har rana ta fadi, sai ya hana Musulmi yin hakan; saboda wannan yana hana yin Tasbihi da kuma Tahlili da Tahmidi da umarni da kyakkyawan aiki da kuma hani da Mummunan aiki, da Karatun Qur'ani da wanin hakan, kuma har walau yana daga cikin aikin Jahiliyya saboda haka aka hana hakan.
An rawaito daga Kais Bn Abi Hazim, ya ce: Sayyadin Abubakar -Allah ya yarda da shi- ya shiga wajen wata Mata daga Kabilar Ahmas ana kiranta da Zainab, sai ya ganta bata Magana? Sa suka ce: tayi rantsuwar Hajji ne ba tare da Magana ba, sai ya ce da ita: kiyi maganarki, cewa hakan bai halatta ba, wannan yana daga cikin aikin Jahiliyya, sai tayi Maganarta.
Buhari ne ya rawaito shiAbubakar -Allah ya yarda da shi ya shiga wajen wata Mata a cikin Kabilar Ahmas sunan ta Zainab, sai ya sameta bata magana, sai ya tambayeta mai yasa bata magana sai suka ce: tayo Hajji ne bata Magana, sai ya ce da ita: kiyi maganarki, saboda barin maganar baki daya bai halatta ba; saboda cewa shi ya Kasance daga cikin Ibadun Jahiliyya sannan sai Musulunci ya Haramta shi, kuma shigar Namiji zuwa mace ba tare da zargi ba ko kadaita kamar yadda Sayyadina Abubakar yayi -Allah ya yarda da shi- ya halatta.
Abdullahi Bin Amru Bin Ass - Allah ya yarda da su zuwa ga Annabi: "Dawowa daga Yaki kamar Tafiya yakin ce"
Abu Daud Ya Rawaito shiA cikin wannan Hadisin Akwai bayanin Falalar Allah Madaukakin Sarki ga bayinsa a lokacin da suka sauke Nauyin Ibadu Saboamar yadda ake basu lada lokacinj tafiya zuwa gareta; haka ake basu lada lokacin da suke dawowa ma daga sauke ta, don haka Annabi ya bada Labarin cewa Mai dawowa daga Yaki kamar Mai tafiya yakin ne, kuma daidai suke a wajen lada, Kamar yadda ake rubuta takun Mai tafiya Masallaci da kuma dawowarsa zuwa iyalansa.
An rawaito daga Abu Huraira -Allah ya yarda da shi ya ce: Manzon Allah SAW ya ce: "Bawa da aka Mallaka Mai gyara yana da Lada Biyu" kuma na rantse da wanda Ran Abuhuraira ya ke a Hannunsa ba don Jihadi a tafarkin Allah ba da kuma Hajji, da kuma biyayyar Mahaifiyata ba, da nai kwadayin na Mutu ina Bawa
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiAbu Huraira -Allah ya yarda da shi- ya ce: Manzon Allah ya ce: "Bawa da aka Mallaka Mai gyara yana da Lada Biyu"; saboda tsayuwa da hakkin Allah Madaukakin Sarki- na ibadu da tsayuwarsa da hakkin Maigidansa na Hidima, Sannan Abuhuraira -Allah ya yarda da shi- ya bada labarin cewa ba don babu Jahadi akan Bawa ba, da kuma tsayuwarsa ga Hidimar Mahaifiyarsa na ciyarwa da Hidima wallahi da na fi son in zamanto na Mutu a Matsayin yana Bawa sabida Ladan da yake cikinsa
An karvo daga Abdullahi Bin Umar Bn Khaxxab -ALlah ya yarda da su- ya ce: "Manzon Allah SAW yayi mana Sallar tsoro a wasu kawanakinsa, sai wata Jama'a suka tsaya tare da shi, wasu kuma suka fuskanci abokan gaba, sai yayi musu raka'a xaya, sannan suka tafi, sai wasu kuma suka zo, sai yayi musa raka'a xaya, sai kowace Jama'a ta rama Raka'a xaixai."
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya yi addu’ar tsoron sahabbansa a wasu yakoki da yake yi da mushrikai lokacin da Musulmi suka hadu da makiyin kafiransu kuma suna tsoron a kawo musu hari a lokacin da suke cikin addu’a, da kuma Abokan gaba ba sa fuskantar alkibla, a cikin addu'a, mazhabar tana fuskantar makiya, suna kiyaye masu ibada. Sa'annan wanda ke tare da shi ya yi raka'a, sannan suka tafi yayin da suke salla, sai suka tsaya suna yankan abokan gaba, sai mazhabar da ba ta yin salla ta zo ta yi raka'a da ita, to Annabi - Allah yi masa salati da sallama - ya gaishe shi. Sannan mazhabin da ke tare da shi a karshe suka tashi suka gama ragowar raka'o'in a kanta, sannan suka tafi tsare, kuma rukuni na farko suka yi rakan wanda shi ma yake a kansa, kuma wannan yana daga cikin sifofin sallah. na tsoro, kuma an tsara shi ne kamar yadda Ibn Abbas - Allah ya yarda da su - ya ce: Juna). Bukhari ne ya rawaito.