





























Hadeeth Cards
Da'wa cards that highlight great meanings from the noble prophetic hadiths in a simple style and attractive display that helps the Muslim to have a deeper understanding of his religion in an easy way
All
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi -: Lallai cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Da a ce mutane suna sanin abinda ke cikin kiran sallah (na lada) da kuma sahu na farko sannan ba za su samu ba sai idan sun yi ƙuri'a a kansa da sun yi ƙuri'a, kuma da a ce suna sanin abinda ke cikin gaggawa (zuwa sallah a farkon lokaci) da sun yi gasar zuwa gare shi, kuma da a ce suna sanin abinda ke cikin sallar dare (Issha) da Asuba da sun zo musu koda da jan ciki ne».
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa mutane da a ce suna sanin abinda ke cikin kiran sallah da sahun farko na falala da alheri da albarka sannan ba za su samu damar samun shi ba sai sun yi ƙuri'a akan sa, waye a cikinsu ya fi cancanta akan ɗan uwansa ? da sun yi ƙuri'a, kuma da a ce suna sanin abinda ke cikin gaggawa zuwa sallah a farkon lokacinta da sun yi rigegeniya gareta, kuma da a ce suna sanin gwargwadan lada a zuwa sallar Issha'i da sallar Asuba da zuwa gare su ya yi sauƙi koda da jan ciki ne akan gwiwowi kamar yadda yaro yake tafiya a farkon al'amarinsa.
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Wanda ya gangaro daga wani dutse sai ya kashe kansa to shi yana cikin wuta zai dinga gangarowa a cikinta yana abin dawwamarwa a cikinta har abada, wanda ya tsotsi wata gubar sai ya kashe kansa to gubarsa tana hannunsa zai dinga tsotsarta a cikin wutar Jahannama yana madawwami a cikinta har abada, wanda ya kashe kansa da wani ƙarfe to ƙarfen zai zama a hannunsa zai dinga cakawa cikinsa shi a cikin wutar Jahannama yana madawwami har abada a cikinta».
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi wa wanda ya yi gangancin kashe kansa gargaɗi a duniya cewa za’a yi masa uƙuba a ranar alƙiyama a cikin wutar Jahannama ta irin hanyar da ya yi wa kansa a duniya dan sakamakon da ya dace, wanda ya faɗo daga saman dutse sai ya kashe kansa to shi yana cikin wutar Jahannama zai dinga faɗowa a cikinta daga dutsen Jahannama zuwa kwarinta yana madawwami a cikinta, wanda ya kwankwɗi wata guba sai ya kashe kansa da ita to gubarsa tana hannunsa zai dinga kwankwaɗarta a cikin wutar Jahannama yana madawwami a cikinta har abada, wanda ya cakawa kansa wani karfe a cikinsa sai ya kashe kansa, to karfensa yana hannunsa zai dinga sukar kansa da shi a cikinsa a cikin wutar Jahannama yana madawwami a cikinta har abada.
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «(Mutum) bakwai Allah - Maɗaukakin sarki - Zai inuwantar da su a cikin inuwarSa ranar da babu wata inuwa sai inuwarSa: Shugaba adali, da saurayin da ya taso a cikin bautar Allah, da mutumin da zuciyarsa ta rataya da masallatai, da mutum biyu da suka so juna saboda Allah, sun haɗu saboda Shi kuma suka rabu saboda Shi, da mutumin da mace mai matsayi da kyau ta neme shi sai ya ce: Lallai ni ina jin tsoron Allah, da mutumin da ya yi sadaka sai ya ɓoyeta har (hannunsa) na hagu bai san abinda (hannunsa) na dama ya ciyar ba, da mutumin da ya ambaci Allah shi kaɗai sai idanuwansa suka zubar da hawaye».
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi wa nau'i bakwai na muminai bushara cewa Allah - Maɗaukakin sarki - Zai inuwantar da su a inuwar al-ArshinSa a ranar da babu wata inuwa sai inuwarSa: Na farko: Shugaba adali a kansa ba fasiƙi ba, kuma mai adalci tsakanin talakawansa ba azzalimi ba; shi ne babban shugaba, dukkan wanda ya jiɓinci wani abu na al'amuran musulmai sai ya yi adalci a cikinsa zai risku da hakan. Na biyu: Saurayin da ya taso a cikin bautar Allah, kuma ya ƙarar da samartakarsa da nishaɗinsa, har ya mutu akan hakan. Na uku; Mutumin da zuciyarsa ta rataya da masallaci idan ya fita daga cikinsa har sai ya dawo zuwa gare shi, saboda tsananin soyayyarsa gare shi da kuma lazimtar masallacin da ci gaba da kasancewa a cikinsa da zuciya, koda wani abu mai bijirowa ya bijirowa jiki (kamar rashin lafiya) kuma ya zama a wajen masallacin. Na huɗu; Mutum biyu kowane ɗaya daga cikinsu ya so ɗayan saboda Allah a haƙiƙa, kuma suka dawwama akan soyayyar Addini wani abu mai bijirowa na duniya bai rabasu ba daidai ne sun haɗu a haƙiƙa ko a'a har mutuwa ta rabasu. Na biyar: Da mutumin da mace ta neme shi akan kanta dan aikata alfasha, kuma mai asali ce da ɗaukaka da matsayi da alfarma da dukiya da kyau, sai ya ƙi kuma ya ce: Ni ina jin tsoron Allah. Na shida: Mutumin da ya yi sadaka kaɗan ce ko mai yawa bai yi riya a cikinta ba kai ya ɓoyeta har hagunsa bata sanin abinda damansa take ciyarwa. Na bakwai: Mutumin da ya ambaci Allah da zuciyarsa daga tinani ne, ko da harshensa na zikiri, a keɓance daga mutane sai hawaye suka kwaranyo daga idanuwansa dan jin tsoron Allah da kuma girmama Shi - Maɗaukakin sarki -.
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Kada ɗayanku ya yi nuni zuwa ga ɗan uwansa da makami, domin shi bai sani ba wataƙila Shaiɗan ya fizge daga hannunsa sai ya faɗa ciki ramin wuta».
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi gargaɗi ga musulmi ya nuna ɗan uwansa musulmi da kowane irin makami, domin cewa shi bai sani ba wataƙila Shaiɗan ya ɗauke shi akan motsa makamin a hannunsa, sai ya kashe ɗan uwansa ko ya cutar da shi, sai ya faɗa cikin saɓon da zai kai shi ya faɗa cikin ramin wuta.
Daga Abu Shuraih - Allah Ya yarda da shi - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Wallahi ba muminin ba ne, wallahi ba mumini ba ne, wallahi ba mumini ba ne», aka ce: Waye ya Manzon Allah? ya ce: «Wanda maƙocinsa ba ya aminta daga sharrinsa».
Bukhari ne ya rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi rantsuwa kuma ya ƙarfafi rantsuwarsa sau uku, sai ya ce: Wallahi ba mumini ba ne, wallahi ba muminin ba ne, wallahi ba mumini ba ne, sai sahabbai suka tambaye shi : Waye wanda ba mumini ba ya Manzon Allah? ya ce: Wanda maƙocinsa yake jin tsoron yaudararsa da zalincinsa da kuma sharrinsa.
Daga Anas - Allah Ya yarda da shi ya ce: Wasiyyar Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - mai gamewa ta kasance lokacin da rasuwarsa ta zo masa: «Ku kula da sallah da abinda hannayenku suka mallaka, ku kula da sallah da abinda hannayenku suka mallaka», har Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya fara gargarar mutuwa, amma harshensa bai iya faɗinta ba.
Nasa'i ne ya ruwaito shi cikin Alkubra da Ibnu MajahMafi yawan wasiyyar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ga al'ummarsa ta kasance alhali shi yana cikin magagin mutuwa: Ku lazimci sallah ku kiyayeta, kada ku rafkana daga gareta, haka nan haƙƙoƙin abinda hannayenku suka mallaka na bayi maza da kuyangi mata ku kyautata mallakinsu, bai gushe ba yana maimaita ta, har maƙogwaransa ya fara gargarar mutuwa da ita, harshensa bai kusa ya bayyananar da ita ba.
Daga Ubadah ɗan Samit - Allah Ya yarda da shi - yace: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Zinare da zinare, azirfa da azirfa, alkama da alkama, sha'ir da sha'ir, dabino da dabino. gishiri da gishri, (dole su zama) tamka da tamka, daidai da daidai (a lokacin da za’a yi canji), idan waɗannan jinsinan suka canza, to ku siyar yadda kuke so idan ya zama hannu da hunnu ne".
Muslim ne ya rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana hanyar yin inagntaccen ciniki a cikin nau’ukan da riba take shiga cikinsu (abubuwa) guda shida sune: Zinare, da azirfa, da alkama, da sha'ir, da dabino, da gishiri, idan sun kasance daga irin nau'in ne kamar saida zinare da zinare azirfa da azirfa... to babu makawa daga sharuɗɗa biyu: Na farko: Tabbatar daidaituwa a cikin awon sikeli ne, idan ya kasance abin aunawa ne na sikeli kamar zinare da azirfa, ko samun daidaito a awo idan ya kasance abin aunawa ne na kwano kamar alkama da sha'ir da dabino da kuma gishiri. Na biyu: Mai siyen ya karɓi abin siyarwar shi kuma mai siyarwar ya karɓi kuɗin, hakan (ya zama) a gurin da akayi cinikin. Idan waɗannan nau’ukan suka saɓa kamar saida zinare a bada azirfa, da dabino a bada alkama misali, to cinikin ya halatta da sharaɗi ɗaya, shi ne mai siyarwar ya karɓi kuɗin shi kuma mai siyen ya karɓi abin siyan a gurin da aka yi cinikin, inba haka bafa to cinikin ɓatacce ne, kuma sun faɗa cikin ribar da aka haramta, mai siyen da mai siyarwar duk ɗaya ne a hakan.
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Duk mayafin da ya yi ƙasa da idan sawu to yana cikin wuta".
Bukhari ne ya rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya gargaɗi maza daga sakin dukkan abinda yake suturce jikinsu tufa ne ko wanduna ko waninsu ƙasa da idan sawun diga-digai, kuma abinda ke ƙasan idan sawu na ƙafar mai mayafin da ya sake shi to shi yana cikin wuta dan yi masa uƙuba akan aikinsa.
Daga sarkin muminai baban Hafs Umar ibnul Khaɗɗab - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: «Dukkan ayyuka basa yi yiwuwa sai da niyyoyi, kuma kowanne mutum yana da ladan abin da ya niyyata ne wanda hijirarsa ta kasance zuwa ga Allah da ManzonSa to hijirarsa tana ga Allah da ManzonSa, wanda hijirarsa ta kasance dan duniya da zai sameta ko wata mace da zai aureta to hijirarsa tana ga abin da ya yi hijira zuwa gare shi».
Limaman Malaman Hadisi guda biyu ne suka rawaito shi, Abu Abdullahi Muhammad bn Isma'il bn Ibrahim bn al-Mughirah bn Bardizbah al-Bukhari, da Abul Husain Muslim bn al-Hajjaj bn Muslim al-Kushairi an-Naisaburi, a cikin Sahihansu guda biyu, waɗanda su ne mAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bayyana cewa dukkanin ayyuka ababen izina ne da niyya, wannan hukuncin mai gamewa ne a cikin dukkanin ayyuka na ibadu da mu'amaloli, wanda ya yi nufin wani abin amfani da aikinsa ba zai samu komai ba sai wannan abin amfanin, kuma babu sakamako gareshi, wanda yayi nufin neman kusanci da aikinsa zuwa ga Allah - madaukakin sarki zai samu sakamako da lada daga aikinsa ko da aikin ya kasance na al'ada ne, kamar ci da sha. Sannan (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya buga misali don bayanin tasirin niyya a ayyuka tare da daidaituwarsu a sura ta zahiri, sai ya bayyana cewa wanda ya yi nufin neman yardar Ubangigjinsa da hijirarsa, to, hijirarsa hijira ce ta shari'a abar karɓa za a yi masa sakayya a kanta don gaskiyar niyyarsa, wanda ya yi nufin wani abin amfani na duniya na dukiya, ko kasuwanci, ko mata da hijirarsa ba zai samu komai daga hijirarsa ba sai wancan abin amfanin da ya yi niyyarsu, kuma ba zai samu lada da sakamako ba.