





























Hadeeth Cards
Da'wa cards that highlight great meanings from the noble prophetic hadiths in a simple style and attractive display that helps the Muslim to have a deeper understanding of his religion in an easy way
All
Daga Abu Abdullahi Nu'uman ibnu Bashir - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbbata a gare shi - yana cewa: "Lallai halal a bayyane yake kuma haram ma a bayyane yake, a tsakaninsu akwai wasu al'amura masu rikitarwa da yawa daga mutane ba sa saninsu, wanda ya kiyaye shubuhohi ya kuɓuta a addininsa da mutuncinsa, wanda ya afka cikin shubuhohi ya afka a cikin haram, kamar mai kiwo ne da yake kiwo a gefen shinge ya kusata ya yi kiwo a cikinsa, ku saurara! lallai kowane sarki yana da shinge, ku saurara! lallai shingen Allah shi ne abubuwan da ya haramta, ku saurara lallai! Lallai a jiki akwai wata tsoka, idan ta gyaru jiki ya gyaru dukkaninsa, idan ta ɓaci jiki ya ɓaci dukkaninsa, ku saurara! ita ce zuciya".
Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bayyana wata ƙa'ida mai gamewa game da abubuwa, cewa sun kasu a shari'a zuwa kashi uku: Bayyanannen halal, da bayyanannen haram, da al'amura masu rikitarwa waɗanda hukuncinsu ba a bayyane yake ba ta bangaren halacci da haramci, da yawa daga mutane basa sanin hukuncinsu. Wanda ya bar waɗannan abubuwan masu rikitarwa gareshi, to, addininsa ya kuɓuta ta hanyar nisanta daga fadawa a cikin haram, kuma mutuncinsa ya kuɓuta daga zancen mutane da abin da za su dinga aibatashi a kansa saboda aikata wannan abin rikitarwar. Wanda bai nisanci shubuhohi ba, to, haƙiƙa ya kai kansa ko dai ga faɗawa a cikin haram, ko aibatawar mutane ga mutuncinsa. Kuma Manzo - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya buga misali don ya bayyana halin wanda yake aikata shubuhohi, kuma cewa shi kamar mai kiwo ne da yake kiwon dabbobinsa kusa da ƙasar da mai ita ya sa mata shinge, dabbobin mai kiwon sun kusa su yi kiwon a cikin wannan shingen don kusancinsu gareshi, to, haka nan wanda yake aikata a bin da a cikinsa akwai shubha, to, shi da wannan ɗin yana kusantowa ga haram, kuma yana kusa da ya afka cikinsa. Bayan wannan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ba da labarin cewa a cikin jiki akwai wata tsoka (ita ce zuciya) jiki yana gyaruwa da gyaruwarta, kuma yana ɓaci da ɓacinta.
Daga Abu Hamza Anas ibnu Malik - Allah Ya yarda da shi - hadimin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Ɗayanku ba zai yi imani ba, har sai ya sowa ɗan uwansa abinda yake sowa kansa".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa imani cikakke ba ya tabbata ga wani daga musulmai har sai ya so wa ɗan'uwansa abinda yake sowa kansa na ayyukan ɗa'a da nau'ukan alkairai a addini da rayuwa, kuma ya ki abinda yake ki ga kansa, idan ya ga wata tawaya ga ɗan'uwansa musulmi a addininsa, to ya yi kokari a cikin gyarata, idan ya ga wani alheri a cikinsa to ya daidaita shi ya taimake shi, ya yi masa nasiha a al'amarin Addininsa da duniyarsa.
Daga Abu Mas'ud Uƙbah ibnu Amr al-Ansari al-Badri - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Yana daga abin da mutane suka riska daga zancen Annabci na farko: Idan ba ka da kunya, to ka aikata abin da kake so".
Bukhari ne ya rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa daga abinda ya zo a cikinsa wasicci game da Annabawa magabata, kuma mutane suka jujjuya shi tsakaninsu kuma suka gaje shi daga garesu ƙarni bayan ƙarni, har sai da yakai zuwa farkon wannan al'ummar, ka duba zuwa abinda kake son ka aikata shi, idan ya kasance abinda ba'a jin kunyarsa ne to ka aikata shi, idan ya kasance daga abinda ake jin kunyarsa ne to ka bar shi; domin abinda yake hana munanan ayyuka shi ne kunya, wanda ba shi da kunya, to sai ya kutsa a cikin kowace alfasha da abin ƙi.
Daga Umar ibnul Khaɗɗab - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Da a ce zaku dogara ga Allah haƙiƙanin dogaranSa, da Ya azirtaku kamar yadda yake azirta tsuntsu, yana wayar gari a yunwace ya kuma yi maraice cikinsa a cike».
Imam Ahmad da Tirmithi da Nasa'i da Ibnu Majah da Ibnu Hibban a cikin Sahihinsa da kuma Hakim ne Suka ruwaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana kwaɗaitar da mu da cewa mu dogara ga Allah - Mai girma da ɗaukaka - wajen jawo amfani da tunkuɗe cuta a al'amuran duniya da Addini, domin cewa ba mai bayarwa, ba mai hanawa, ba mai cutarwa, ba mai amfanarwa sai shi - tsarki ya tabbatar masa Ya ɗaukaka-, kuma mu aikata sabubban da za su jawo mana amfani su tunkuɗe mana cuta tare da gaskiyar dogaro ga Allah, a duk lokacin da muka aikata haka Allah Zai azurtamu kamar yadda Yake azurta tsuntsun da yake fita da safe alhali yana a yunwace, sannan ya dawo da yamma alhali cikinsa a cike, wannan aikin daga tsuntsu wani nau'i ne daga sabubba a tafiya don neman arziki, ba tare da ƙaryar dogaro ba da kuma kasala.
Daga Nawwas Ibnu Sam'an al-Ansari - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «al-Birr shi ne: Kyakkyawar ɗabi'a, zunubi kuma abin da ya sosu a cikin zuciya, kuma ka ƙi mutane su tsinkaya a kansa». Daga Wabisa ibnu Ma'abad - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na zo wa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ya ce: «Kazo ne kana tambaya game da al-birr da zunubi?», na ce: Eh, ya ce: «Ka tambayi zuciyarka, al-birr: Abin da ranka ya natsu zuwa gare shi, kuma zuciya ta nutsu gare shi, zunubi kuma: Abin da ya sosu a cikin zuciyarka kuma ya kaikawo a cikin ƙirji, ko da mutane sun baka fatawa kuma sun baka fatawa».
Hadisi na farko: Muslim ne ya ruwaito shi, Hadisi na biyu kuma: Ahmad da Darimi suka rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labari game da al-birr da kuma zunubi, sai ya ce: Lallai mafi girman ɗabi'un al-birr su ne kyawawan ɗabi'u tare da Allah ta hanyar jin tsoron Allah, haka tare da halitta ta hanyar jure cuta, da ƙarancin fushi, da shimfiɗar fuska, daddaɗan zance, da sadar da zumunci, da biyayya da tausasawa da kuɓutarwa, da kyakkyawar mu'amala da abokantaka, kuma cewa al-birr shi ne abin da zuciya da rai suka nutsu gare shi. Amma zunubi to abin da ya kaikawo a cikin zuciya na abubuwa masu rikitarwa kuma ya kaikawo ba tare da ƙirji ya samu natsuwa daga gareshi ba, kuma kokwanto ya faru daga gare shi a cikin zuciya, da jin tsoron kasancewarsa zunubi ne, kuma baka son ka bayyanar da shi dan kasancewarsa mummuna a idanuwa da mutanen kirki da cikakkun mutane, hakan domin rai a ɗabi'arsa yana son ganin mutane akan alherinsa, idan rai ya ƙi tsinkaya akan wasu daga cikin ayyukansa to shi zunubi ne babu alheri a cikinsa; ko da mutane sun baka fatawa to kada ka ɗauki fatawarsu muddin dai alamar shubha tana kaikawo a cikin ranka, domin fatawa bata kawar da shubha muddin dai shubhar ingantacciya ce, kuma mai bada fatawa yana bada fatawa ba tare da ilimi ba; amma idan fatawar gini ce akan wani dalili na shari'a to wajibi akan mai neman fatawa shi ne ya koma zuwa gare ta, ko da ƙirjinsa bai budeba gareta ba.
Daga Abdullahi ibnu Busr - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Wani mutum Ya zo wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai ya ce: Ya Manzon Allah! Lallai cewa shari'un Musulunci sun yawaita a kanmu, to wace ƙofa ce mai tattarowa zamu yi riƙo da ita? ya ce: «Kada harshenka ya gushe yana ɗanye daga ambatan Allah». A cikin wata riwayar: Daga hadisin Mu'azu ibnu Jabal - Allah Ya yarda da shi -: Ƙarshen abin da na rabu da Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a kansa shi ne na ce: Wane aiki ne daga cikin ayyuka ya fi kuma ya fi kusanci zuwa ga Allah? Ya ce: «Ka mutu alhali harshenka yana ɗanye daga ambatan Allah».
Ahmad ne ya ruwaito shi da Tirmizi da Ibnu Majah da kuma Ibnu HibbanWani mutum ya kai ƙara wurin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - cewa nafilifilin ibadu sun yi masa yawa har ya gajiya daga yin su saboda rauninsa, sannan ya tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya shiryar da shi ga wani aiki mai sauki mai jawo lada mai yawa wanda zai rataya da shi ya yi riƙo da shi. Sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya nunar masa harshensa ya zama ɗanye mai motsawa saboda dawwamar ambatan Allah - tsarki ya tabbatar maSa Ya ɗaukaka - a kowane lokaci da hali; na tasbihi da tahmidi da istigafari da addu'a da makamancin hakan.
Daga Abu bakrata - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Shin ba na ba ku labarin mafi girman zunubai ba?" sau uku, suka ce: na'am ya Manzon Allah, ya ce: "Yi wa Allah shirka, da saɓawa iyaye" sai ya zauna alhali ya kasance a kishingiɗe, sai ya ce: "Ku saurara da faɗar zur" ya ce: Bai gushe ba yana maimaitata har sai da muka ce: Ina ma dai ya yi shiru.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana ba wa sahabbansa labari game da mafi girman zunubai, sai ya ambaci waɗannan ukun: 1. Yi wa Allah shirka: Shi ne juyar da kowanne nau'in ibada ga wanin Allah, da daidaita wanin Allah da Allah a AllantakarSa da UbangidantakarSa da sunayenSa da siffofinSa. 2. Saɓawa iyaye: Shi ne kowacce irin cutarwa ga iyayen, magana ce ko aiki, da barin kyautatawa musu. 3. Faɗin zur, shaidar zur tana daga ciki: Shi ne dukkanin maganar da take ƙarya ce da aka yi nufin tauye wanda ta faɗa kansa ta hanyar ƙwace dukiyarsa da keta mutuncinsa, ko makamancin hakan. Haƙiƙa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya maimaita gargaɗi game da faɗin zur don faɗakarwa a kan muninta da mummunan gurbinta ga zamntakewa, har sai da sahabbansa suka ce: Ina ma dai ya yi shiru don tausaya masa, da kuma ƙin abin da zai tayar masa da hankali.
Daga Mikdam dan Ma'adikarib - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Idan mutum ya so dan'uwansa to ya sanar da shi cewa shi yana sonsa".
Abu Dawud da Tirmizi da Nasa'i a cikin alkubra haka Ahmad suka ruwaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bayyana daya daga sabubban da suke karfafa alaka tsakanin muminai kuma suke yada soyayya a tsakaninsu, shi ne cewa idan mutum ya so dan'uwansa to ya sanar da shi cewa shi yana son sa.
Daga Abdullahi Dan Amr Dan Aas - Allah Ya yarda da su - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Manyan zanubai su ne: Yi wa Allah shirka, da saɓawa iyaye, da kashe rai, rantsuwa mai dulmiyarwa".
Bukhari ne ya rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bayyana manyan zunubai cewa su ne waɗanda aka yi narko (alƙawarin azaba) a kan wanda ya aikata su da narko mai tsanani a duniya ko a lahira. Na farkonsu "Yi wa Allah shirka": Shi ne karkatar da kowanne nau'i daga Nau’ukan ibada ga wanin Allah, da daidaita wanin Allah da Allah cikin abin da ya keɓanci Allah a AllantakarSa da UbangidantakarSa da sunayenSa da siffofinSa. Na biyunsu: "Saɓawa iyaye": Shi ne dukkanin abin da yake nuna cutarwa ga iyaye; magana ce ko aiki, da barin kyautata musu. Na ukunsu "Kashe rai": ba tare da wani haƙƙi ba, kamar kisa a kan zalunci da ta'addanci. Na huɗunsu "Rantsuwa mai dulmiyarwa": Ita ce rantsuwa alhali yana mai ƙarya yana sane cewa ƙarya yake, an ambaceta da hakan; domin cewa tana dulmiya mai yinta a laifi sannan a wuta.