





























Hadeeth Cards
Da'wa cards that highlight great meanings from the noble prophetic hadiths in a simple style and attractive display that helps the Muslim to have a deeper understanding of his religion in an easy way
All
Daga Nana Aisha Uwar Muminai - Allah ya yarda da ita - ta ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - bai taɓayin wata sallah ba bayan saukar: {Idan nasarar Allah ta zo da buɗi} [al-Nasr: 1] ta sauka gare shi sai ya ce a cikinta (sallar): "Tsarki ya tabbatar maKa Ubangijinmu da godiyarKa ya Allah Ka gafarta mini'. Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana yawan faɗa a cikin ruku'unsa da sujjadarsa: "Tsarki ya tabbatar maKa ya Allah Ubangijinmu da godiyarKa, ya Allah Ka gafarta mini" yana fassara alƙur'ani.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiUwar muminai Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - tana bada labarin cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - lokacin da aka saukar masa da: {Idan nasarar Allah ta zo da buɗi} ya fassara Alƙur'ani kuma ya yi gaggawa zuwa ruko da umarnin Allah - Maɗaukakin sarki - a cikin faɗinSa: {Ka yi tasbihi da godiyar Ubangijinka kuma ka nemi gafararSa}, to ya kasance yana yawaita faɗa a cikin halin ruku'insa da sujjadarsa a tsakiyar sallah: "Tsarki ya tabbatar maKa" da tsarkakewa gareKa daga dukkan tawaya daga abinda ba ya dacewa da Kai, "Ya Allah Ubangijinmu da godiyarKa" da yabo abin yabo gareKa dan cikar zatinka da siffofinKa da ayyukanKa, "Ya Allah Ka gafarta mini' Ka shafe mini zunubina Ka ƙetare daga gare shi .
Daga Abu Umama Iyas ɗan Sa'alaba alHarisi - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wanda ya yanki haƙƙin wani mutum musulmi da rantsuwarsa, to haƙiƙa Allah Ya wajabta wuta gare shi, kuma Ya haramta masa aljanna" sai wani mutum ya ce: Koda wani abune ɗan kaɗan ya Manzon Allah? ya ce: "Koda kara ne na itaciyar ƙirya".
Muslim ne ya rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya gargaɗar daga yin rantsuwa da Allah akan ƙarya kuma yana sane, hakan dan yankar haƙƙin wani mutum musulmi, domin cewa sakamkon hakan shi ne cancantar wuta, da haramta aljanna, kuma shi yana daga manyan zunubai. Sai wani mutum ya ce ya Manzon Allah: Koda abinda aka rantse akan shi ɗin wani abune dan kaɗan? Sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Koda hakan ya zama a itacen asuwakin da ake cira ne daga bishiyar ƙirya.
Daga Nana A'isha uwar muminai - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Manzon Allah - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan ya zo wajan mara lafiya yana yi masa addu'a zai ce : «Ya Ubangijin mutane Ka tafiyar da tsanani, Ka warkar, Kai ne Mai warkarwa, babu wata waraka sai warakarKa, warakar da bata barin wata masassara».
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan ya ziyarci wani mara lafiya zai yi masa addu'a sai ya ce: Ya Allah (Ka tafiyar) Ka gusar da (tsanani) da tsananin rashin lafiya, (ya Ubangijin mutane) kuma Mahaliccinsu kuma Mai renansu, (Ka warkar da) wannan mara lafiyar (Kai ne) tsarki ya tabbatar maKa (Mai warkarwa) ina kamun ƙafa zuwa gareKa da sunanKa Mai warkarwa, (babu wata waraka) mai tabbata ga mara lafiya (sai warakarKa) da kuma lafiyarKa, (waraka) kai tsaye (wacce bata bari) ta wanzar ta kuma bar (wata masassara) da wani rashin lafiyar daban.
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Dinaren da ka ciyar da shi a cikin tafarkin Allah, da dinaren da ka ciyar da shi a 'yanta wuyaye (‘yanta baiwa), da dinaren da ka yi sadaka da shi ga miskini, da dinaren da ka ciyar da shi ga iyalan ka; to mafi girman su a lada shi ne wanda ka ciyar ga iyalan ka».
Muslim ne ya rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ambaci sashin nau’ukan ciyarwa, sai ya ce: Dinarin da ka ciyar da shi a yaƙi a tafarkin Allah, da dinarin da ka ciyar da shi a 'yanta wuyaye da bauta, da dinarin da ka yi sadaka ga miskini mabuƙaci, da dinarin da ka ciyar da shi ga iyalanka, sannan ya bada labarin cewa mafi girmansu a lada a wajen Allah shi ne wanda ka ciyar da shi ga iyalanka da wanda ciyar da shi ya lazimceka.
Daga Abdullahi ɗan Amr ɗan al-Aas - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Lallai kai kana azimi tsawon shekara, kuma kana tsayuwar dare?", sai na ce: Eh, ya ce: "Lallai kai idan ka aikata hakan ido zai yi rauni saboda shi, kuma zuciya zata gajiya saboda hakan, Wanda ya azimci zamani (a here) to bai yi azimi ba, azimin kwana uku azimin zamani ne gaba ɗayansa", sai na ce: Lallai cewa ni zan iya sama da hakan, ya ce: "To ka yi azimin (Annabi) Dawud - aminci ya tabbata agare shi -, ya kasance yana azimtar yini kuma ya sha yini, kuma ba ya gudu idan ya gamu da maƙiya".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi(Labari) ya kai ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - cewa Abdullahi ɗan Amr - Allah Ya yarda da shi - ya kasance yana jeranta azimi ba ya ajiyewa tsawon shekara, kuma yana sallar dare gaba ɗayansa ba ya bacci, sai ya hana shi daga hakan, kuma ya ce masa: Ka yi azimi kuma ka huta, ka yi sallar dare kuma ka yi bacci. Kuma ya hane shi daga jeranta azimi da tsayuwar dare gaba ɗayansa, kuma ya ce masa: Lallai cewa kai idan ka aikata hakan idanka zai yi rauni saboda shi zai yi kogo zai shige, kuma zuciyarka zata gaji ta ƙosa saboda haka; babu azimi (ga) wanda ya azimci shekara; inda cewa shi bai samu ladan azimin ba dan saɓawa hani, kuma bai buɗe baki ba domin cewa shi ya kame. Sannan ya shiryar da shi zuwa azimin kwana uku a kowane wata shi ne azimin shekara; domin kowace rana (kwatankwacin ladan) kwanaki goma ne, kuma hakan shi ne mafi ƙarancin riɓanyawa ga kyakkyawa. Sai Abdullahi ya ce: Lallai ni zan iya sama da hakan. Sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: To sai ka yi azimin (Annabi) Dawud - aminci ya tabbata agare shi - shi ne mafificin azimi, ya kasance yana azimin yini kuma yana hutawa yini, kuma ya kasance ba ya gudu idan ya gamu da maƙiya; domin tsarin aziminsa ba ya raunana jikinsa ba.
Daga Nu'uman ɗan Bashir - Allah Ya yarda da su -: Cewa mahaifiyarsa 'yar Rawaha ta tambayi babansa wata kyauta daga dukiyarsa ya bawa ɗanta, sai ya jinkirtata shekara sannan ya ga (ya kamata ya yi kyautar), sai ta ce: Ba zan yarda ba har sai ka sa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi shaida ga abinda ka bawa ɗana kyauta, sai babana ya riƙe hannuna, a wannan lokacin ina yaro, sai ya zo wa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai ya ce: Ya Manzon Allah, lallai cewa babar wannan 'yar Rawaha tana son in saka shaida a kan abinda na bawa ɗana kyauta, sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Ya kai Bashir, shin kana da wani dan ne banda wannan?" ya ce: Eh, sai ya ce: "Shin dukkansu ka basu kwatankwacin wannan?" ya ce: A'a, ya ce: "To kada ka sani shaida, domin cewa ni bana yin shaida akan zalinci", A Muslim: "To kasa wani shaida akan wannan ba ni ba".
Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi, kuma yana da Lafuza da damaNu'uman ɗan Bashir - Allah Ya yarda da su - ya bada labarin cewa mahaifiyarsa Amrah 'yar Rawaha - Allah Ya yarda da ita - ta tambayi babansa wata kyautar da zai bawa ɗanta daga dukiyarsa, sai ya yi nauyi ya jinkirtata har shekara, sannan ya ga ya kamata ya amsa mata abinda ta nema sai ya bawa ɗansa Nu'uman kyauta, sai ta ce: Ba zan yarda ba har sai ka sa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sheda akan abinda ka bawa ɗana, sai babana ya riƙe hannuna ni kuma a wannan lokacin ina ƙaramin yaro, sai ya zo wa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai ya ce: Ya Manzon Allah, lallai cewa babar wannan 'yar Rawaha tana son in sakaka shaida akan abinda na bawa ɗanta kyauta, sai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: Ya kai Bashir, shin kana da wani ɗan ne banda wannan? Ya ce: Eh. Sai ya ce: Shin dukkansu ka ba su kwatankwacin wannan? Ya ce: A'a. Ya ce: To kada ka sa ni shaida, domin cewa ni ba na shaida a kan zalinci. A riwayar Muslim ya ce yana mai zarginsa: Sai dai ka sa wanina ya yi shaida a kan wannan zalincin.
Daga Ɗan Abbas - Allah Ya yarda da su - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Wanda ya duba mara lafiya (wanda) ajalinsa bai yi ba, sai ya ce a wurinsa sau bakwai: Ina roƙon Allah Mai girma Ubangijin al-Arshi Mai girma Ya baka lafiya, sai Allah Ya ba shi lafiya daga wannan cutar".
Abu Daud ne ya ruwaito shi da Kuma Tirmizi da AhmadAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa babu wani musulmin da zai ziyarci wani musulmi a cikin rashin lafiyarsa wanda lokacin mutuwarsa bai yi ba, sannan mai ziyarar ya yi wa mara lafiya addu'a da faɗinsa: (Ina roƙon Allah Mai girma) a cikin zatinSa da siffofinSa da ayyukanSa, (Ubangijin al-Arshi Mai girma Ya baka lafiya), kuma ya maimaitata hakan sau bakwai sai Allah Ya ba shi lafiya daga wannan cutar.
Daga Ummu Salama Uwar muminai matar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wanda ya kasance yana da abin yankan da zai yanks shi (na Layya) to idan jijirin watan Zul-Hijja ya kama, to kada ya cire wani abu daga gashinsa ko faratansa har sai ya yi layya".
Muslim ne ya rawaito shiAnnbi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya umarci wanda ya yi nufin ya yanka abin layyarsa cewa kada ya cire wani abu daga gashin kansa ko hammatarsa ko gashin bakinsa ko waninsu ko daga faratan hannunsa ko ƙafarsa idan jinjirin watan Zul-Hijja ya bayyana har sai ya yi layya.
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi -: Lallai cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Idan (watan) Ramadan ya zo sai a buɗe ƙofofin aljanna, kuma a kukkule ƙofofin wuta, a ɗaɗɗaure shaiɗanu".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa idan watan Ramadan ya shiga sai al'amura uku su faru: Na farko: Za'a buɗe ƙofofin aljanna ba za'a kulle wata ƙofa ba daga cikinsu. Na biyu: Za'a kulle ƙofofin wuta, kuma ba za'a buɗe wata ƙofa daga cikinsu ba. Na uku: Za'a ɗaure shaiɗanu da aljanu masu tsaurin kai da sarƙoƙi, ba zasu kai zuwa ga abinda suke tsira da shi a cikin wanin (watan) Ramadan ba. Dukkanin wannan dan girmamawa ne ga wannan watan, da kwaɗaitar da masu aiki akan yawaita ayyukan ɗa'a na sallah da sadaka da zikiri da karatun Alkur'ani da wanin haka; da kuma nisantar zunubai da saɓo.