





























Hadeeth Cards
Da'wa cards that highlight great meanings from the noble prophetic hadiths in a simple style and attractive display that helps the Muslim to have a deeper understanding of his religion in an easy way
All
Daga Jabir - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Allah Ya yi wa mutum rahama mai saukakawa idan zai siyar, kuma idan zai siya, kuma idan zai nemi biyan bashi".
Bukhari ne ya rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi addu'a da rahama ga dukkanin wanda ya kasance mai sauki mai kyauta a cinikinsa; Ba ya tsanantawa mai saye a farashinta kuma yana mu'amalantarsa da kyakkyawan halaye, Mai sauki mai kyauta idan zai siya, baya tauye mudu kuma ba ya karanta daga kimar haja. Mai sauki mai kyauta idan ya nemi biyan basukansa; ba ya tsanantawa akan talaka da mabukaci, kai yana nemansa da sauki, kuma yana jinkirtawa wanda ke cikin mawuyacin hali.
Daga Abu Huraira Allah - Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: "Wani mutum ya kasance yana bawa mutane bashi, ya kasance yana cewa wani yaronsa: Idan kaje wurin wanda ke cikin muwuyacin hali to ka kau da kai gare shi , muna fatan Allah ya ketare mana (zunubanmu), sai ya gamu da Allah sai Ya yafe masa".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labari: Game da mutumin da ya kasance yana mu'amalar bashi tare da mutane, ko ya siyar bashi, Ya kasance yana cewa yaronsa wanda yake karbo masa basukan dake hannun mutane: Idan ka je wurin wanda ake bi bashi kuma ba shi da abinda zai biya bashin dake kansa dan gajiyawarsa "To ka kau da kai gare shi"; ko dai da jinkirta masa da rashin nace masa a kan ya biya., Ko da karbar abinda ke tare da shi koda tare da abinda ke cikinsa ne na tawaya, hakan dan kwadayi daga gare shi akan Allah Ya ketare masa kuma ya yi masa rangwame. Lokacin da ya mutu sai Allah ya yi masa afuwa kuma ya ketare daga munanan ayyukansa.
Daga Anas - Allah ya yarda da shi - da isnadi: "Duk wanda ya fita neman ilimi to zai kasance a kan tafarkin Allah har sai ya dawo."
Al-Tirmithi Ya Rawaito shiMa'anar hadisin: Wanda ya fita daga gidansa ko kasarsa Don neman ilimin shari'a, yana zuwa karkashin hukuncin wanda ya fita zuwa jihadi saboda Allah Madaukaki, don haka zai koma ga danginsa. Domin kamar mai gwagwarmaya ne wajen rayar da addini, da wulakanta Iblis, da wahalar da kai.
Daga Abu Zarr, Jundubu Ibnu Junadata, da Abu Abdurrahman, Mu'azu Ibnu Jabal - Allah Ya yarda da su - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Ka ji tsoron Allah a duk inda kake, kuma ka bi munanan (ayyuka) da kyakkyawa zai shafe shi, ka ɗabi'anci mutane da kyawawan ɗabi'u».
Tirmizi ne ya ruwaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi umarni da al'anura uku: Na farko: Tsoron Allah hakan ta hanyar aikata wajibai, da barin abubuwan da aka haramta, a kowane guri da zamani da kuma hali, a ɓoye da bayyane, haka a lokacin lafiya da bala'i da wanin haka. Na biyu: Idan ka afka cikin mummunan (laifi), to ka aikata kyakkawan (aiki) a bayan shi, kamar sallah da azimi da sadaka da aikin alheri da sada zumunci da wanin haka, domin cewa hakan zai shafe mummuna. Na uku: Ka yi wa mutane mu'amala da kyawawan ɗabi'u, na murmushi a fuskokinsu, da tausasawa da aikata alheri da kamewa daga cutarwa.
Daga Abu Bakrata - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa: "Idan musulmai biyu suka haɗu da takubbansu, to, wanda ya kashe da wanda aka kashe suna cikin wuta", sai na ce: Ya Manzon Allah, wannan mai kisan ne, to, mene ne laifin wanda aka kashe? ya ce: "Lallai shi ma ya kasance mai kwaɗayi ne a kan kashe ɗan uwansa".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana ba da labarin cewa idan musulmai biyu suka haɗu da takubbansu, kowanne daga cikinsu yana nufin kashe abokinsa, to, mai kisan yana cikin wuta saboda kashe abokinsa, sahabbai suka rikita ga wanda aka kashe; Ta yaya zai zama a wuta? sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ba da labarin cewa shi ma yana wuta don kwaɗayinsa a kan kashe ɗan uwansa, babu abin da ya hanashi kisan sai gaggawar mai kisan da kuma rigayarsa da yayi.
Daga Umar dan Khaɗɗab - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira daa mincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Dukkan ayyuka (ba sa inganta) sai da niyya, kaɗai mutum (ana ba shi ladan) abin da ya niyyata ne, wanda hijirarsa ta kasance zuwa ga Allah da manzonsa, to, hijirarsa tana ga Allah da manzonsa, wanda hijirarsa ta kasance don duniya da zai sameta, ko wata mace da zai aureta, to, hijirarsa tana ga abin da ya yi hijira zuwa gareshi". A wani lafazin na Bukhari; "Dukkan ayyuka (ba sa yiwuwa) sai da niyyoyi, kaɗai kowane mutum (ana ba shi ladan) abin da ya niyyata ne".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bayyana cewa dukkanin ayyuka ababen izina ne da niyya, wannan hukuncin mai gamewa ne a cikin dukkanin ayyuka na ibadu da mu'amaloli, wanda ya yi nufin wani abin amfani da aikinsa ba zai samu komai ba sai wannan abin amfanin, kuma babu sakamako gareshi, wanda yayi nufin neman kusanci da aikinsa zuwa ga Allah - madaukakin sarki zai samu sakamako da lada daga aikinsa ko da aikin ya kasance na al'ada ne, kamar ci da sha. Sannan (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya buga misali don bayanin tasirin niyya a ayyuka tare da daidaituwarsu a sura ta zahiri, sai ya bayyana cewa wanda ya yi nufin neman yardar Ubangigjinsa da hijirarsa, to, hijirarsa hijira ce ta shari'a abar karɓa za a yi masa sakayya a kanta don gaskiyar niyyarsa, wanda ya yi nufin wani abin amfani na duniya na dukiya, ko kasuwanci, ko mata da hijirarsa ba zai samu komai daga hijirarsa ba sai wancan abin amfanin da ya yi niyyarsu, kuma ba zai samu lada da sakamako ba.
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: "Lallai cewa wani mutum ya cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -: Yi min wasiyya, sai ya ce: "Kada ka yi fushi" sai ya maimata da yawa, ya ce: "Kada ka yi fushi".
Bukhari ne ya rawaito shiƊaya daga cikin sahabbai - Allah Ya yarda da su - ya nemi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya shiryar da shi a kan wani abin da zai amfaneshi, sai ya umarceshi da kada ya yi fushi, ma'anar hakan cewa shi ne ya nisanci sabubban da za su sa shi fushi, kuma ya tsare kansa idan fushi ya faru gareshi, kada ya zarce tare da fushinsa da kisa ko duka ko zagi da makamancin hakan. Mutumin ya maimaita neman wasiyya da yawa, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi bai ƙara komai a wasiyyarsa ba a kan "Kada ka yi fushi".
Daga Umar ɗan Khaɗɗab - Alah Ya yarda da shi - ya ce: Ya ji Annabin Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa: "Da a ce za ku dogara ga Allah haƙiƙanin dogaro, da Ya azurtaku kamar yadda yake azurta tsuntsu, yana wayar gari a yunwace kuma ya yi yammaci a ƙoshe".
Tirmizi da Ibnu Majah da Ahmad Suka ruwaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana kwaɗaitar da mu da cewa mu dogara ga Allah - Mai girma da ɗaukaka - wajen jawo amfani da tunkuɗe cuta a al'amuran duniya da Addini, domin cewa ba mai bayarwa, ba mai hanawa, ba mai cutarwa, ba mai amfanarwa sai shi - tsarki ya tabbatar masa Ya ɗaukaka-, kuma mu aikata sabubban da za su jawo mana amfani su tunkuɗe mana cuta tare da gaskiyar dogaro ga Allah, a duk lokacin da muka aikata haka Allah Zai azurtamu kamar yadda Yake azurta tsuntsun da yake fita da safe alhali yana a yunwace, sannan ya dawo da yamma alhali cikinsa a cike, wannan aikin daga tsuntsu wani nau'i ne daga sabubba a tafiya don neman arziki, ba tare da ƙaryar dogaro ba da kuma kasala.
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - Daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi -, a cikin abin da yake hakaitowa daga Ubanngijinsa - mai girma da ɗaukaka -, ya ce: "Wani bawa ya aikata wani zunubi, sai ya ce: Ya Allah Ka gafarta min zunubina, sai (allah) Mai girma da ɗaukaka ya ce: Bawana ya yi laifi, sai ya san cewa yana da Ubangijin da zai gafarta masa zunubi, kuma yana yin uƙuba a kan zunubi, sannan ya dawo ya sake yin zunubi, sai yace: Ya Ubangiji Ka gafarta min, sai Maɗaukakin sarki Ya ce: Bawana ya yi laifi, sai ya san cewa yana da Ubangijin da zai gafarta masa zunubi, kuma Yanayin uƙuba a kan zunubi, sannan ya dawo sai yayi zunubin, sai ya ce: Ya Ubangiji ka gafarta min laifina, sai Maɗaukakin sarki Ya ce: Bawana ya yi laifi, sai ya san cewa yana da Ubangijin da zai gafarta zunubi, kuma yanayin uƙuba a kan zunubi, ka aikata abin da ka so haƙiƙa na gafarta maka".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiAnnabi -tsira da amincin Allah su tabbat a gareshi - yana ruwaitowa daga Ubangijinsa cewa idan bawa ya aikata zunubi sannan ya ce: Ya Allah Ka gafarta min zunubina, Allah - Maɗaukakin sarki - Zai ce: Bawana ya aikata zunubi, kuma ya san cewa yana da Ubangijin da zai gafarta masa zunubi, Ya suturtashi ya yafe masa, ko yayi masa uƙuba a kansa, haƙiƙa Na gafarta masa. Sannan bawan ya dawo sai ya yi zunubi, sai ya ce: Ya Ubangiji Ka gafarta min zunubina, sai Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: Bawana ya aikata zunubi, sai ya san cewa yana da Ubangijin da yake gafarta zunubi, sai ya suturta shi ya yafe masa, ko Ya yi masa uƙuba a kansa, haƙiƙa Na gafartawa bawana. Sannan bawan ya dawo sai ya yi zunubi, sai ya ce: Ya Ubangiji Ka gafarta min zunubina, sai Allah Ya ce: Bawana ya aikata zunubi, sai ya san cewa yana da Ubangijin da yake gafarta zunubi, sai ya suturta shi ya yafe masa, ko Yayi masa uƙuba a kansa, haƙiƙa Na gafartawa bawana, sai ya aikata abin da ya so muddin dai cewa shi a duk lokacin da ya yi zunubi zai bar zunubin ya yi nadama, ya yi niyyar barin komawa a cikinsa, sai dai zuciyarsa tana rinjayarsa, sai ya afka a cikin zunubi karo na gaba, muddin dai yana aikata haka yana zunubi yana tuba, to, zan gafarta masa; domin cewa tuba yana rushe abin da ke kafinsa.