





























Hadeeth Cards
Da'wa cards that highlight great meanings from the noble prophetic hadiths in a simple style and attractive display that helps the Muslim to have a deeper understanding of his religion in an easy way
All
Daga Abul Ja'ad al-Damri - Allah Ya yarda da shi -, kuma ya kasance sahabi ne, cewa manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wanda ya bar Juma'o'i uku dan wulaƙantar da su Allah zai yi yumƙi akan zuciyarsa".
Abu Dawud da Tirmizi da Nasa'i da Ibn Majah da Ahmad ne Suka Rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi gargaɗi daga barin sallar Juma'a, kuma wanda ya bar sallar Juma'a sau uku dan sakaci da kasawa ba tare da wani uzuri ba Allah zai rufe zuciyarsa ta hanyar hana isar alheri gare shi .
Daga Abdullahi Ibnu Abbas - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - bai taɓa yaƙar wasu mutane ba har sai ya kirasu (zuwa ga Addini).
Ahmad da Baihaki suka Rawaito shiIbnu Abbas - Allah Ya yarda da su - ya bada labarin cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - bai taɓa farawa da yaƙar wasu mutane ba har sai ya kirasu zuwa ga Musulunci a farko, idan ba su amsa kiransa ba sai ya yaƙe su.
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annbai - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: Mutum uku zan yi rigirma da su a ranar alƙiyama: Mutumin da ya bada amana da sunana sannan ya yi yaudara, da mutumin da ya saida ɗa ya ci kuɗinsa, da mutumin da ya hayi ɗan ƙodago ya cika masa aikinsa amma bai ba shi ladansa ba".
Bukhari ne ya rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: Nau'i uku na mutane zan yi rigima da su a ranar alƙiyama, duk wanda na zama abokin rigimarsa kuwa zan rinjaye shi: Na farko: Wanda ya rantse da Allah, ya yi alƙawari. sannan ya warware shi ya yi yaudara. Na biyu: Wanda ya saida ɗa akan cewa bawa ne, sai kuma ya ci kuɗinsa ya yi tasarrufi da ƙimarsa. Na uku: Wanda ya dauki ɗan ƙodago dan yin wani aiki, sai ya kammala masa aikin, amma bai biya shi kuɗin aikinsa ba.
Daga Ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Mumini ba zai gusheba a cikin yalwar Addininsa ba, muddin dai bai zubar da jinin da aka haramta masa ba».
Bukhari ne ya rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa mumini ba zai gushe ba a cikin yalwar ayyukansa na gari, da fatan samun rahamar Allah da gafararSa da kuma rangwaminSa, har sai idan ya kashe wani mutumin da aka haramta masa kashe shi to haƙiƙa ayyukansa zasu yi masa ƙunci; domin ba zasu iya biyan laifin kisa da kuma zunibinsa mai girma ba.
Daga Anas ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Wasu mutane daga Ukl ko Urainah suka zo (wurin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -), sai suka ƙyamaci zama a Madina sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya umarce su suje gurin raƙuman (zakka), kuma su sha fitsarinsu da nononsu, sai suka tafi, lokacin da suka samu lafiya sai suka kashe mai kiwon (dabbobin) Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, suka kora dabbobin, sai labari ya zo a farkon yini, sai ya aika aka bi bayansu, lokacin da rana ta ɗaga sai aka zo da su, sai ya yi umarni a yanke hannayensu da ƙafafuwansu, kuma aka tsire idanuwansu, aka jefasu a cikin zafin rana, suna neman a shayar da su ruwa amma ba'a shayar da su ba. Abu Ƙilabah ya ce: Waɗannan sun yi sata sun yi kisa, sun kafirta bayan sun yi imani, sun yaƙi Allah da ManzonSa.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiWasu mutane daga ƙabilu biyu na Ukl da Urainah waɗanda su musulmai ne sun zo wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai wata cuta ta samesu wacce cikinsu ya kumbura, kuma suka ƙyamaci zama a Madina saboda abincinta da iskarta ba su dace da su ba. Sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya umarcesu su je inda raƙuman zakka suke, su sha fitsarinsu da nononsu, sai suka tafi, lokacin da suka samu lafiya suka yi ƙiba launinsu ya dawo musu sai suka kashe mai kiwon dabbobin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, suka kora raƙuman, sai labari ya zo a farkon yini (da safe), sai ya aika a nemo su, sai aka riskesu, lokacin da rana ta ɗaga sai aka zo da su gurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a ɗaure, sai ya yi umarni a yanke hannayensu da ƙafafuwansu, kuma aka tsiyayar da idanuwansu, domin haka suka yi wa makiyayin, kuma aka jefasu a cikin zafin rana, sunan neman a shayar da su ruwa amma ba'a shayar da su, har suka mutu. Abu Ƙilabah ya ce: Lallai su sun yi sata, sun yi kisa, sun kafirce bayan sun yi imani, kuma sun yaƙi Allah da ManzonSa.
Daga Aliyu - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Wanda ya aikata laifin da za'a iya yi masa haddi sai aka gaggauto da uƙubarsa a duniya to Allah Shi ne Mafi karamcin Ya yi wa bawanSa uƙuba (biyu, daya aduniya da kuma) a lahira, wanda ya aikata laifin da za’a yi masa haddi sai Allah Ya suturta shi kuma Ya yi masa afuwa to Allah Shi ne Mafi karamcin ya dawo da abinda Ya riga Ya yi afuwarsa».
Tirmizi ne ya Rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa wanda ya aikata wani saɓon da yake wajabta haddin shari'a, kamar zina da sata, sai ya samu uƙubarsa kuma aka tsayar masa da haddi a duniya, to lallai hakan zai shafe masa wannan saɓon, kuma zai shafe uƙubarsa ta lahira; domin cewa Allah Shi ne Mafi karamci kuma Mafi jin ƙan ya haɗawa bawanSa uƙuba biyu. Wanda kuma Allah Ya suturta shi a duniya, ba a yi masa uƙuba ba akan wannan saɓon, kuma Allah Ya yi masa afuwa Ya gafarta masa, to Allah Shi ne Mafi buwaya kuma Mafi girma Mafi karamcin ya dawo da uƙubar zunubin da Ya riga Ya gafarta shi kuma Ya yi afuwarsa.
Daga Umar Ibnul Khaɗɗab - Allah Ya yarda da shi -: Cewa wani mutum a zamanin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sunansa Abdullahi, kuma ya kasance ana yi masa laƙabi da jaki, ya kasance yana sa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - dariya, Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance ya yi masa bulala saboda giya, sai aka zo da shi wata rana sai ya sa aka yi masa bulala, sai wani mutum daga cikin mutanen ya ce: Ya Allah Ka tsine masa, ina mamakin yawan abin da ake zuwa da shi saboda shi?! sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Kada ku tsine masa, na rantse da Allah ban san wani abu daga gare shi ba sai dai yana son Allah da ManzonSa".
Bukhari ne ya rawaito shiA zamanin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - akwai wani mutum sunansa Abdullahi, ana yi masa laƙabi da jaki, ya kasance yana sa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - dariya a cikin wasu daga cikin kalamansa, (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya kasance ya yi masa bulala saboda giya, sai wata rana aka zo da shi ya sha giya sai ya sa aka yi masa bulala. Sai wani daga cikin mahalarta ya zage shi, ya ce: Allah Ya tsine masa, ya mamakin yawan zuwan da ake yi da shi ya sha giya?! sai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Kada ku yi masa mummunar addu'ar korewa daga rahamar Allah, na rantsae da Allah ban san wani abuba daga gare shi sai cewa shi yana son Allah da ManzonSa.
Daga Abu al-Darda'i - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Shin bana baku labarin abin da ya fi azimi da sallah da sadaka daraja ba?" Suka ce: Eh, ya ce: "Yin sulhu tsakanin waɗanda ke rigima, domin ɓacin tsakanin waɗanda ke rigima shine mai askewa".
Abu Dawud da Tirmizi ne Suka Rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya tambayi sahabbansa: Shin bana baku labarin abin da ya fi ladan nafilar azimi da sallah da sadaka ba? Suka ce: Eh.. Ya ce: Yin sulhu tsakaknin masu rigima inda rigima take gadar da rabuwa da kuma kadaita da ƙiyayya da juyawa juna baya tsakanin mutane, domin abin da yake haifuwa akan ɓata waɗanda ke rigima na ƙiyayya wacce ita ce ɗabi'ar da sha'aninta shine ta halakar ta tunɓuke Addini da duniya kamar yadda aska take tunɓuke gashi.
An karbo daga Al-Sa'ib Bn Yazid -Allah ya yarda da su- ya ce:Annabi yayi Hajji tare da ni a Hajin bankwana, kuma ni ina Dan shekara Bakwai
Buhari ne ya rawaito shiAl-Sa'ib Bn Zaid -Allah ya yarda da su- Karamin Sahabi ne, Iyayensa sunyi Hajji da shi a lokacin Annabi ya riski Hajjin bankwana, kuma Annabi ya tabbatar da Hajjin Yara, kuma an kirga musu ita a Hajjin Tadawwu'i, sai dai yazama dole iodan ya Balaga yayi wani Hajjin don Sauke Farali, kuma Yaro zaiyi irin abunda Manya suke yi na Harama da rashin sanya dinkakkun kaya da yin Talbiyya da waninta, to idan ya kasa yi sai Waliyyinsa yayi masa, Kamar Babansa ko Mahaifiyarsa.