Hadeeth Cards
Da'wa cards that highlight great meanings from the noble prophetic hadiths in a simple style and attractive display that helps the Muslim to have a deeper understanding of his religion in an easy way






























Da'wa cards that highlight great meanings from the noble prophetic hadiths in a simple style and attractive display that helps the Muslim to have a deeper understanding of his religion in an easy way
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya yi alƙawarin narkon azaba ga wanda ya aikata wasu ayyuka cikin al’ummarsa, da ya ce: Ba ya daga cikimmu. Na farko: Wanda ya yi camfi ko aka yi masa camfi, asalinsa: suna sakin tsuntsu ne lokacin fara wani abu, kamar tafiya ko fatauci ko wanin haka, idan ya yi dama sai ya ce akwai sa’a, sai ya yi abin da ya sa a gaba, idan kuma ya yi hagu sai ya ce babu sa’a sai ya ƙi yi, bai halatta ya yi haka da kansa ba, ko ya sa a yi masa, camfi da kowanne abu na ji ne ko na gani ya shiga ƙarƙashin haka, da tsuntsaye ko dabbobi aka yi, ko masu fama da nakasa, ko wasu lambobi ko ranaku, da sauransu. Na biyu: Wanda ya yi bokanci ko aka yi masa bokanci’. Duk wanda ya ce ya san gaibu ta hanyar taurari, ko wanin haka, ko ya je wurin wanda ya ce ya san gaibu kamar boka da makamantansu, ya kuma gasgata shi a abin da ya faɗa na cewar ya san gaibu, to, haƙiƙa ya kafirta da abin da aka saukarwa Annabi Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi. Na uku: Wanda ya yi asiri ko aka yi masa asiri’. Shi ne wanda yake yin a siri da kansa, ko ya sa a yi masa asiri, domin ya amfanar da wani da shi, ko don ya cutar da wani, ko ya ƙulla ƙulli da zare da asiri da surkulle da aka haramta da tofi a kai.
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana tsoratarwa a kan zuwa wurin mai duba -suna ne fitacce na boka, da mai taurari, mai zane a kasa da makamantansu, irin wanda yake kafa dalilin sanin gaibu ta hanyar wasu abubuwa na farko-farkon lamari- zallar tambayarsa a kan wani abu na gaibu, zai haramta masa ladan sallah na kwanaki arba’in, wannan uƙuba ce, a kan wannan laifi, kuma zunubi ne mai girma.
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana bayyana duk wanda ya koyi, ya samu wani tsagi na ilimin taurari da buruji da kuma kafa dalili da motsinsu da shigarsu da fitarsu a kan abin da zai faru a bayan ƙasa na mutuwar wane, ko rayuwarsa, ko rashin lafiyarsa, da makamancin haka cikin abinda zai faru nan gaba, to, haƙiƙa ya koyi wani tsagi na sihiri, kuma duk lokacin da mutum ya ƙara wannan ilimin, to, ya ƙara asiri [tsafi] ne.
Annabi ya fada a cikin wannan Hadisin cewa wasu Zunubai suna daga cikin Manyan zunubai su ne: Cewa ka a Sanya abokin tarayya ga Allah cikin Rububiyyarsa ko bautarsa, kuma ya fara da shi ne; sabida cewa sune mafi girman zunubai, da kuma yanke kauna da debe haso daga Allah; domin hakan munana zato ne ga Allah da kuma Jahiltar yalwar rahamarsa, kuma da yana daga cikin talala ga bawa da ni'ama har sai ya kamashi da laifinsa bai shirya ba, kuma ba ana nufin bayyana baki dayan Manyan Zunubai ba ne cikin abinda aka ambata ba; domin Manyan zunubai suna da yawa, abin nufi bayanin mafi girmansu.
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana bayyana cewar imani rassa ne, kuma halaye ne masu yawa, sun kunshi ayyuka da ƙudurce-ƙudurcen zuciya da maganganu. Kuma mafi girman ɗabi’un imani da falala shi ne faɗin: "Babu abin bautawa da cancanta sai Allah". Tare da sanin ma’anarta, da kuma aiki da abin da take nunawa na cewa Allah Shi ne abin bauta guda ɗaya, wanda Ya cancanci a bauta masa Shi kaɗai ban da wani ba shi ba. Kuma mafi ƙarancin ayyukan imani shi ne kawar da duk abin da zai cutar da mutane a kan hanyoyi. Sannan sai Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ba da bayanin cewa kunya tana cikin ɗabi’u na imani, kuma ɗabi’a ce da take zaburarwa a kan yin abu mai kyau da kuma barin mummuna.
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance a wata tafiyarsa a lokacin mutane suna wurin baccin su inda suke bacci a bukkokinsu da shemominsu. Sai ya aika wani mutum don ya sami mutane ya umarcesu da yanke kowanne abu da aka rataya a wuyan raƙumi, shin na tsirkiya ne, ko wani abu kamar ƙararrawa ko takalmi, domin sun kasance suna yi musu rataye saboda tsoron kambun baka, sai aka umarce su da su yanke, domin babu abin da take karawa, kuma anfanarwa da cutarwa suna hannun Allah ne Shi kadai.
Duk ya juyar da Zuciyarsa ko aikinsa ko baki dayansu zuwa wani abu da take kaunar Anfaninsa ko ije wata Cuta Allah zai jibanta shi zuwa wancan abun da ya rataya da shi, saboda duk wanda ya jibanta Al-amarinsa zuwa ga Allah to ya isar masa kuma zai sawwake masa kowa ne abu mai Wahala, kuma duk wanda ya jibanta al-amarinsa zuwa ga waninsa to Allah zai bar shi zuwa wancan abun kuma ya Kaskanta shi
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana bayanin wanda ya faɗa kuma ya shaida da bakinsa: Babu abin bautawa da cancanta sai Allah. Wato babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma ya kafircewa abin da ake bautawa da ba Allah ba, ya barranta da dukkanin addinai ban da Musulunci, to, haƙiƙka dukiyarsa da jininsa sun haramta a kan Musulmai, ba abin da muke da shi sai zahirin aikinsa, ba za a kwace dukiyarsa ba, ba za a zubar da jininsa ba, sai dai idan ya aikata wani laifi, ko ɓarna da za ta tabbatar da hakan a Hukunce Hukuncen Musulunci. Allah Shi ne Yake jiɓintar hisabinsa ranar Alƙiyama, idan ya yi da gaskiya a ba shi lada, idan kuma munafiki ne a yi masa azaba.
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bayyana cewa waɗanda suke jin ƙai (Ubangiji) Al-Rahman Yana jin ƙan su da rahamarSa wacce ta yalwaci kowanne abu; don sakayyar da ta dace. Sannan (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya yi umarni da jin ƙan waɗanda ke ƙasa mutum ne, ko dabba, ko tsuntsu, ko waninsa na nau'ikan halitta sakamakon hakan (shi ne) Allah Zai ji kanku daga saman sammanSa.