Hadeeth Cards
Da'wa cards that highlight great meanings from the noble prophetic hadiths in a simple style and attractive display that helps the Muslim to have a deeper understanding of his religion in an easy way






























Da'wa cards that highlight great meanings from the noble prophetic hadiths in a simple style and attractive display that helps the Muslim to have a deeper understanding of his religion in an easy way
Uƙuba ɗan Amir - Allah Ya yarda da shi - ya tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - game da sabubban tsirar mumini a duniya da lahira? Sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Na horeka da al'amura uku: Na farko: Ka kiyaye harshenka daga abinda babu alheri a cikinsa, daga faɗar kowane sharri, kuma kada ka yi wani furuci sai da alheri. Na biyu: Ka lazimci gidanka dan ka bautawa Allah a cikin kaɗaitakarka, ka shagalta da biyayya ga Allah - Mai girma da ɗaukaka -, ka nisanci fitinu a cikin gidanka. Na uku: Ka yi kuka ka yi nadama ka tuba daga abinda ka aikata na zunubai.
Wani mutum ya gabato daga mutanen kauye ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - dan ya nuna masa aikin da zai shigar da shi aljanna, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya amsa masa da cewa shiga aljanna da tsira daga wuta sun tsaya akan bada rukunan Musulunci, na bautar Allah Shi kadai, kuma kada ka hada wani abu da Shi. Ka tsaida salloli biyar din Allah Ya wajabta su akan bayinSa a kowanne yini da dare. Ka bada zakkar dukiyar da Allah Ya wajabtasu akanka, ka bada su ga wadanda suka cancanta l. Ka kuma kiyaye akan azimin watan Ramadan a lokacinsa. Sai mutumin ya ce na rantse da wanda raina yake a hannunSa ba zan kara komai akan aikin da aka wajabta ba wanda na ji shi daga gareka na ayyukan da'a ba, kuma ba zan rage ba daga garesu ba. Lokacin da ya juya (ya tafi) sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: Wanda yake son ya yi duba zuwa ga wani mutum daga 'yan aljanna to ya yi duba zuwa ga wannan balaraben kauyen.
Annabi - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - ya yi addu'a da ƙasƙanci da taɓewa har saida hakan ya kai, kai ka ce ya ɗora hancinsa a cikin ƙasa - ya maimaitata sau uku - sai aka tambaye shi: Waye wannan ya manzon Allah wanda ka yi mummunar Addu’a akansa? Sai (Annabi) tsira da a mincin Allah su tabbata aagre shi - ya ce: Wanda ya riski mahaifansa a lokacin tsufa - ɗayansu ko su biyun -, ba su zama sababi na shigarsa aljanna ba; hakan saboda rashin kyautata musu da kuma saɓa musu.
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana matsayin masu ambatan Allah da yawa, kuma cewa su sun kaɗaita kuma sun riga wasunsu da samun manyan darajoji acikin aljannar ni'ima, kuma ya kamantasu da dutsen Jumdan wanda shi kadai ne babu irinsa a cikin duwatsu.
Ma'anar hadisin: Wuta ba ta taba ido mai kuka saboda tsoron Allah Madaukaki, yayin da mutum ya tuna girman Allah da ikonsa na bautar da bayinsa da tuna halin da yake ciki da kuma gazawarsa cikin gaskiyar Allah Madaukaki. Yana kuka da begen rahamar sa da kuma tsoron azabarsa da fushin sa, saboda wannan anyi alkawarin samun kubuta daga wuta. Da kuma wani ido wanda wuta bata taba shi ba, wanda shine: Duk wanda ya kiyaye saboda Allah Madaukakin Sarki a bude da wuraren fada domin kiyaye rayukan musulmai. Da kuma fadinsa: "Wuta ba ta taba su ba." Wannan daga furucin sashi ne da nufin duka, kuma abin da ake nufi shi ne cewa duk wanda ya yi kuka saboda tsoron Allah Madaukaki da wanda ya kiyaye a tafarkin Allah, Allah Madaukaki ya hana jikinsu zuwa wuta.
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa musulmi mai laifi ana yi masa kwadayin afuwar Allah da gafararSa, sai mai bayyanar da sabo dan alfahari da rashin kunya, to ba ya cancantar afuwa; ta inda yake aikata laifi da daddare, sannan ya wayi gari alhali Allah Ya rufa masa asiri, sai ya zantar da waninsa da cewa shi ya aikata sabo kaza jiya, ya kwana Ubangijinsa Ya rufa masa asiri, shi kuma ya wayi gari yana tona asirin da Allah Ya rufa masa!!
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kwaɗaitar da musulmi cewa kar ya mutu sai shi yana kyautatawa Allah zato da rinjayarwarsa ɓangaren ƙauna a lokacin mutuwa da cewa Allah Zai yi masa rahama kuma Zai yi masa rangwame, domin cewa tsoro abin nema ne dan kyautata aiki, wancan halin ba halin ayyuka ba ne, abin nema a cikinsu (shi ne) rinjayar ƙauna.
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa ya haɗu da (Annabi) Ibrahim badaɗayi - aminci ya tabbata agare shi - a daren Isra'i da Mi'iraji, sai ya ce masa Ya Muhammad; Ka isarwa da al'ummarka sallama daga gareni, kuma ka sanar dasu cewa aljanna mai daɗin turɓaya ce, mai daɗin ruwa ce babu zartsi a acikinsa, kuma aljanna mai faɗi ce madaidaiciya ce babu itatuwa a cikinta, dashenta (shi ne) kalmomi masu tsarki, sune wanzajju na gari: Tsarki ya tabbata ga Allah, godiya ta tabbata ga Allah, babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Allah ne Mafi girma, duk lokacin da musulmi ya faɗesu kuma ya maimaita su za'a yi masa dashe a cikin aljanna.