





























Hadeeth Cards
Da'wa cards that highlight great meanings from the noble prophetic hadiths in a simple style and attractive display that helps the Muslim to have a deeper understanding of his religion in an easy way
All
Daga Abu Huraira, Allah ya yarda da shi, cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: Idan kuka ga wani yana sayarwa ko saye a cikin masallaci, to sai ku ce: Allah ba ya amfanar da kasuwancinku, kuma idan kun ga wadanda suke neman vata abu a ciki, sai ku ce: A'a.
Al-Tirmithi Ya Rawaito shiDaga Anas - Allah Ya yarda da shi - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Alƙiyama ba zata tashi ba har sai mutane sun dinga yin alfari da massalatai».
Abu Dawud da Nasa'i da ibn Majah ne Suka Rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa: Yana daga cikin alamomin kusancin ranar alƙiyama da kuma ƙarewar duniya mutane zasu dinga alfahari da ƙawata masallatansu, ko kuma alfaharinsu da duniyarsu a cikin masallatan da ba'a ginasu ba sai dan ambatan Allah.
Daga Nana Aisha Uwar Muminai - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance yana buɗe sallah da kabbara, da kuma karatu, da (faɗar) Alhamdu lillahi rabbil aalamina (Dukkan yabo ya tabbata ga Allah Ubangijin talikai), ya kasance idan ya yi ruku`u ba ya ɗago kansa, ba kuma ya miƙar da shi saidai tsaka-tsaki, ya kasance idan ya ɗago kansa daga ruku`i ba ya yin sujjada, har sai ya daidaita a tsaye, ya kuma kasance idan ya ɗago kansa daga sujjada, ba ya kuma sujjada har sai ya daidaita a zaune, ya kasance yana yin tahiya a bayan kowace raka`a biyu, ya kasance yana shimfiɗa ƙafar sa ta hagu ya kuma kafe ƙafar sa ta dama, ya kasance yana yin hani gameda irin zaman shaiɗan. sannan yana yin hani mutum ya shimfiɗa hannayen sa guda biyu irin shimfiɗawar namun daji, ya kasance yana rufe sallar da yin sallama.
Muslim ne ya rawaito shiUwar muminai Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - ta yi bayanin sallar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - cewa shi ya kasance yana buɗe sallarsa da kabbarara harama, sai ya ce: «Allahu Akbar (Allah ne Mafi girma)», kuma yana buɗe karatu da Suratul Fatiha: «Alhamdu lillahi rabbil aalamin (Godiya ta tabbata ga Allah, Ubangijin talikai)...». Ya kasance idan ya yi ruku'u bayan tsayuwa, ba ya ɗaga kansa sama kuma ba ya sunkuyar da shi a lokacin ruku'u, kawai yana maida shi daidai wa daida, idan ya ɗago kansa daga ruku'u sai ya tsayu a tsaye kafin ya yi sujjada, idan ya ɗaga kansa daga sujjada ta farko, ba ya sujjada ta biyu har sai ya tabbata a tsaye. Ya kasance yana zama bayan kowanne raka'o’i biyu dan yin tahiya kuma yana cewa: «Attahiyyatu lillahi was salawat waɗɗaibat(Gaishe-gaishe sun tabbata ga Allah da salloli da tsarkakan ayyuka)...», kuma ya kasance idan ya zauna tsakanin sujjadu biyu ko dan tahiya sai ya shimfiɗa ƙafarsa ta hagu ya zauna a kanta, ya kuma kafa ƙafarsa ta dama. Kuma yana hana mai sallah a cikin sallarsa ya zauna kamar zaman shaiɗan, hakan shi ne ya shimfiɗa ƙafafuwansa akan ƙasa, kuma ya zauna akan ƙarshensu, ko ya ɗanfara mazaunansa a ƙasa ya kafa ƙwaurukansa ya kuma ɗora hannayensa akan ƙasa kamar yadda kare yake yi, ko mai sallah ya shimfiɗa zira'insa ya shimfiɗasu a cikin sujjada kamar yadda namun daji suke yi . Kuma ya kasance yana cika sallarsa da yin sallama: «Assalamu alaikun warahmatullah» daga dama sau ɗaya, ɗayan kuma daga hagu.
Nayi Sallah tare da Manzon Allah SAW ya sanysa Hannunsa na Dama kan Hannunsa na Hagu akan Qirjinsa
Ibn Khuzaimah ya rawaito shiaga Abu Hurairah - Allah ya yarda da shi - ya ce: "Abin da na yi a bayan wani ya fi addu'ar manzon Allah, Salati da amincin Allah su tabbata a gare shi fiye da haka-don haka. Don haka muka yi salla a bayan wannan mutumin kuma ya kasance yana tsawaita biyu na farko daga la'asar, kuma ya sau biyu a kan sauran biyu, kuma ya yi haske a rana, kuma ya karanta a cikin Magriba a takaice Kuma yana karantawa a abincin dare a rana da daddare da makamantansu, da safe kuma sai ya karanta dogayen Surori guda biyu. ”
Al-Nasa'i Ya Rawaito shi - Ahmad ne ya rawaito shiHadisin ya nuna cewa daya daga cikin limaman Masallacin Annabi ya yi daidai da addu’ar Annabi –sallal Lahu alaihi wa sallama- kuma ya kasance yana bin sa a tsawaita raka’o’in farko na Zuhr da sassautawa a raka’o’i biyun karshe da kuma la’asar ma. Da kakin zuma
Daga Ibn Abbas -Allah ya yarda da su- ya ce Manzon Allah ya buxe mana labule kuma Mutane sunyi Sahu a bayan Abubakar sai ya ce: "Ya ku Mutane babu abunda ya ragu daga cikin Alamomin Annabta sai Kyakkyawan Mafarkin da Musulmi zai ganshi, ko a ganar masa, ku saurara kuma lallai ni ina hana karanta Al-qur'ani a a Ruku'u ko a Sujada amma a Ruku'u ku girmama Allah kuma a Sujada to kuyi qoqrin Addu'a an kusa a amsa Muku"
Muslim ne ya rawaito shiManzon Allah SAW ya buxe labule da iqanin abunda ya faru, a haqyake qofar Xakinsa da gidan kuma Mutane sunyi sahu bayan Abubakar -Allah ya yarda da shi- suna sallah cikin jam'i,kuma shi bai iya yin Sallah tare da su ba saboda rashin lafiya sai ya Umarci Abubakar da yayi sallah da Mutane, sai ya ce: "yaku mutane cewa shi babu abunda ya ragu na Alamomin Annabta sai kawai Mafarki nagari" to bayan Mutuwar Manzon Allah SAW da yankewar wahayi babu abunda ya Sai kyakkyawan Mafarki ai wanda yake dacewa da abunda ya faru sai ya tiqa dacewa da abunda ya faru sai Masu Imani su gani don suyi Bushara kuma suyi farin ciki da shi, su qara tabbaci kan tabbaci, da kuma kasancewarsa yana daga yankin Annabta; saboda Manzon Allah SAW ya zauna farkon Annabtarsa yana ganin Mafarki sai kuma abun ya faru kamar walqiyar Asuba, saboda haka wani Vangare ne na Annabtar sa -Amincin Allah a gare shi- da kuma faxinsa: "Sai Busharori" yin bayani da Bushara ya rinjayar da mafi yawa, in kuma ba haka ba to ai akwai Mafarkin da jan kunne ne daga allah kuma gaskiya ne da Mu,ini yake gani don sauqaqawa a gare shi, don ya shirya abunda zai faru kafin faruwarsa, kan haka Mafarki ya za,anto kodai bushara ga Mumini ko kuma nusarwa gare shi daga waya Gafala da kuma yace Mumini zai ganshi ko a hanar masa, duk xaya ne Musulmi ne ya gani ko ganar masa akai, faxinsa kuma: "Cewa ni na hana Karanta Qur'ani a Ruku'u ko Sujada" yana nufin cewa Allah SWT ya hana Manzonsa ya karanta Qur'ani a halin Rku'u ko Sujada, kuma duk abunda aka hana SAW wannan yana nufin cewa Al-ummarsa ma tana cikin wannan hanin sai in an smu Dalilin da ya kevance shi SAW wannan idan ya nufi karatu a ruku'un ko sujadar amma idan ya nufi yin Addu'a ne to babu laifi akansa kuma ya zo cikin Hadisi "Kuma kowane Mutum da abunda yayi niyya" hikimar hanin -Allah shi ne Mafi sani- cewa Ruku'u da Sujada sune halin Qasqanta da kuma risinawa, sannan cewa Sujada tana kasancewa a Qasa bata dace da Qur'ani a karanta shi a wannan Yanayin ba kuma faxinsa: "amma a Ruku' ku girmama Allah " ai kuce Tsarki ya tabbata ga Allah mai girma, da makamancinsa na Tasbihai waxanda aka samu daga Suuna, amma faxinsa: "Kuma a cikin Sujada to kuyi qoqarin yin Addu'a" ai ya dace ga Mai Sallah da yawaita Addu'a a lokacin sujada; saboda wuri ne da ake amsa Addua, kuma ya zo a cikin Muslim cewa SAW cewa ya ce: "Mafi kusancin lokacin da Bawa yake kusantar Ubangijinsa shi ne lokacin da yake Sujada , to ku yawaita Addu'a" sai dai haxe da faxin tsarki ya tabbata ga Ubangiji Mafi xaukaka; saboda Wajibi ne kuma faxinsa: " ankusa a amsa muku" ai ana sa ran samun amsar Addu'aku; Saboda shi ne lokaci mafu kusancin bawa da Ubangijinsa a halin yana Sujada, kuma shi ne wurin da ke so ya tsawaita Addu'a da yawaitawa, idan Mutum ya kasance
Daga Wa'il Bn Hajar -Allah ya yarda da shi- Cewa Manzon Allah SAw ya kasance ian ya yayi Ruku'u yana rarraba 'Yanyatsunsa kuma idan yayi Sujada sai ya haxe su
Ibnu Hibban ne ya Rawaito shiMa'anar Hadisin: "ya kasance idan yayi ruku'u yana rarraba Yatsunsa kuma idan yayi Sujada yana haxe Yatsunsa" ai cewa Manzon Allah SAW ya kasance idan ya kasance a Ruku'u yana kama Guiwoyinsa da Tafukan hannayensa kuma yana ya rarrabe tsakanin Yatsunsa; saboda wancan shi ne mafi cikiar ruku'u; kuma shi ne mafi tabbatar faruwar daidaita bayansa da Kansa, kuma amma a cikin Sujada sai ya sanya Tafukan Hannayensa a kan Qasa, kuma ya haxe yatsunsa ta yadda kowanne yana jikin xayan; don saboda ya samu cikar fuskantar Al-qibla da su, kuma shi ne mafi taimakawa kan jurewa a lokacin Sujada
Daga Malik Bn Huwairith -Allah ya yarda da shi Lallai cewa Manzon Allah SAW idan ya kasanc a Wuturin Sallarsa baya tashi har sai ya daidaita a zaune
Buhari ne ya rawaito shiYa kasance cikin koyarwar Manzon Alllah SAW idan ya tashi daga Raka'ar farko zuwa ta biyu, da ta Uku zuwa ta Hudu baya tashi har sai ya tabbata a zaune zama takaitacce, sannan ya ya tashi, kuma wannan zaman ana kiransa da zaman Hutawa, kuma haqiqa Adadin Sahabbai da yawa sun rawaito hakan
Daga Asim ya ce: na tambayi Anas -Allah ya yarda da shi- game da Al-qunuti, ya ce: kafin ya xago daga Ruku'u, sai na ce: lallai cewa Wane yana rayawa cewa kai kana cewa bayan ruku'u? sai ya ce: Yayi qarya, sannan ya gaya mana cewa Manzon Alllah SAW: "cewa shi yayi yayi al-qunuti wata xaya bayan Ruku'u, yana Addu'a ga wasu Mutane daga cikin Bani Sulaim" kuma ya ce: "Ya aika Mutum Arba'in ko Saba'in -yana dai kokwantn yawan- Na Makarantan Qur'ani zuwa ga wasu Mutane Mushirikai" sai waxan can Mutane suka far musu suka kashe su, kuma ya kasance a tsakaninsu akwai Manzon Allah SAW a lokacin "Ban tava ganin sa yayi bacin rai ba kamar bacin rai akan su"
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiWanna Hadisin yana bayanin Halaccin Al0qunuti a faruwar Wata Musiba, kuma cewa ita tana kasancewa ne bayan Ruku'u saboda aikin Manzon Allah SAW lokacin da banu sulaim suka warware masa Al-qawarin da ke tsakaninsu da Musulmai da kshe Mutum saba'in ko Arba'in na Makaranta Qur'ani waxan da Manzon Allah SAW ya turasu zuwa gare su sai yayi Al-qunuti wata xaya akan su bayan Ruku'i.