





























Hadeeth Cards
Da'wa cards that highlight great meanings from the noble prophetic hadiths in a simple style and attractive display that helps the Muslim to have a deeper understanding of his religion in an easy way
All
Daga Anas - Allah Ya yarda da shi ya ce: Na kasance ina shayar da mutane ( giya) a gidan Abu Ɗalha, kuma giyarsu ta kasance a wannan lokacin ita ce tsimi, sai a (Cakuɗa bushasshen dabino da 'ya'yan dabino kafin su zama ɗanye) Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya umarci wani mai kira ya yi kira: Ku saurara lallai cewa giya haƙiƙa an haramtata, ya ce: Sai Abu Ɗalha ya ce da ni: Ka fita ka zubar da ita, sai na fita sai na zubar da ita, sai ta kwaranya a lungunan Madina, sai wasu cikin mutane suka ce: Haƙiƙa an kashe wasu mutane alhali ita tana cikin cikinsu, sai Allah Ya saukar da: {Babu laifi ga waɗanda suka yi imani kuma suka aikata aiki na gari a abinda suka ɗanɗana} [al-Ma'ida: 93] karanta ayar har ƙarshenta.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiAnas ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi - ya bada labarin cewa shi ya kasance yana cikin shayar da wanda yake cikin gidan mijin babarsa Abu Ɗalha - Allah Ya yarda da shi -, giyarsu ta kasance a wannan lokacin ita ce tsimi, shi ne cakuɗa bushasshen dabino da 'ya'yansa kafin ya zama ɗanye, sai ga mai kira daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana kira: Ku saurara lallai cewa giya haƙiƙa an haramtata, ya ce: Sai Abu Ɗalha ya ce da ni: Ka fita, ka zubar da ita, sai na fita sai na zubar da ita, sai giyar ta kwarara a lungunan Madina, sai wasu daga mutane suka ce: Haƙiƙa an kashe (a jihadi) wasu sahabbai kafin haramtata alhali ita tana cikin cikinsu, sai Allah Ya saukar da: {Babu laifi akan waɗanda suka yi imani kuma suka aikata aiki na gari a abinda suka dandana} [al-Ma'ida: 93] Aya. Wato: Babu zunubi akan waɗanda suka yi imani a cikin abinda suka dandana kuma suka sha na giya kafin haramtata.
Daga Abu Najih Irbad ibn Sariyah - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya yi mana wa’azi, wa’azin da zukata suka firgita daga gare shi, kuma idanuwa suka zub da hawaye daga gare shi, muka ce: Ya Manzon Allah! kamar wa’azin mai bankwana, ka yi mana wasiyya, sai ya ce: «Ina yi muku wasicci da jin tsoron Allah, da ji da bi, ko da bawa ne ya shugabance ku, domin cewa wanda ya rayu daga cikinku zai ga saɓani mai yawa, to na horeku da sunnata da kuma sunnar halifofina shiryayyu masu shiryarwa Ku riƙeta da turaman haƙoranku, na haneku daga fararrun al'amura; domin dukkanin bidi'a ɓata ce».
Abu Dawud da Tirmizi ne Suka Rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi wa sahabbansa wa'azi wa'azi isasshe zukata sun ji tsoro daga gare shi, kuma idanuwa sun zubar da hawaye daga gare shi, Sai suka ce : Ya Manzon Allah ! kai ka ce wannan wa'azin bankwana ne, saboda abinda suka gani ya kai matukarsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a wa'azi, sai suka nemi wata wasiyyar dan su yi riko da ita a bayansa, Ya ce: Ina yi muku wasicci da tsoron Allah - Mai girma da daukaka -, hakan da aikata wajibai da barin abubuwan da aka haramta, da ji da bi, wato: Ga shugabanni, koda bawa ne ya shugabanceku ko ya yi rinjaye a kanku, wato ya zama mafi kaskantar halitta sarki akanku kada ku hanu daga hakan, ku bi shi dan tsoron tada fitintinu, domin shi wanda ya rayu daga cikinku zai ga sabani mai yawa. Sannan ya bayyana musu mafita daga wannan sabanin, hakan dayin riko da sunnarsa da sunnar Halifofi shiryayyu a bayansa, Abu bakar Al-Siddik, da Umar Dan Al-khaddab, da Usman Dan Affan, da Aliyu Dan Abu Dalib - Allah Ya yarda su baki daya -, da riketa da turamen hakora wato - turamen hakora na karshe -: Yana nufi da hakan kokari a lazimtar sunna da yin riko da ita, ya kuma gargadesu daga fararrun al'amura kirkirarru a Addini, domin cewa kowacce bidi'a bata ce.
Daga Abdullahi Dan Amr - Allah Ya yarda da su - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Ku isar game da ni koda aya daya ce, kuma ku zantar game da Banu Isra'ial babu laifi, duk wanda ya yi mini karya da gangan to ya tanadi mazauninsa a wuta".
Bukhari ne ya rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana umarni da isar da ilimi daga gare shi na littafi ne ko Sunnah, koda abin ya zama kadan ne kamar aya daya daga Alkur’ani ko hadisi, da sharadin ya zama masani da abinda zai isarda shi kuma ya yi kira zuwa gare shi. Sannan tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya bayyana cewa babu laifi da akan bayanai daga Banu Isra'il da abinda ya afku gare su na al'amura da abinda ba ya karo tare da shari'a. Sannan ya yi gargadi daga yi masa karya, kuma cewa duk wanda ya yi masa karya da gangan to yariki masauki a wuta.
Daga Mikdam dan Maadikarib - Allah Ya yarda da shi - ya ce : Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbbata agare shi - ya ce "Ku saurara, kada wani mutum Hadisi ya je masa daga gareni alhali shi yana kishingide akan mazauninsa sai ya ce: Tsakanin mu da ku littafin Allah, abinda muka samu na halal a cikinsa mu halattashi, abinda muka samu a cikinsa na haram mu haramtashi, kuma lallai abinda Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya haramta to kamar abinda Allah Ya haramtane".
Abu Dawud da Tirmizi da Ibn Majah ne Suka Rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agar shi - ya bada labarin cewa hakika wani lokaci ya kusa , wani sinfi na mutane zasu zamo acikinsa a zaune, dayansu yana kishingide akan shinfidarsa, Hadisi zai isar masa daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai ya ce: Abinda zai raba tsakaninmu da ku a cikin al'amura shi ne Alkur’ani Mai girma shi ya ishemu, abinda muka samu a cikinsa na halal mu yi aiki da shi, abinda muka samu a cikinsa na haram mu nisance shi. Sannan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa duk abinda ya haramtashi ko ya yi hani gareshi a cikin sunnarsa to shi a hukunci kamar abinda Allah Ya haramtashi ne a cikin littafinSa; domin cewa shi ne mai isarwa daga Ubangijinsa.
Daga Irbad dan Sariya - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Wata rana Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya tsaya a cikinmu, sai ya yi mana wa'azi, wa'azi isasshe zukata suka ji tsoro daga gare shi, idanuwa suka zubar da hawaye daga gareshi, aka ce: Ya Manzon Allah ka yi mana wa'azin bankwana to ka yi mana alkawari. Sai ya ce: 'Na horeku da tsoron Allah, da ji da bi, koda bawa ne mutumin Habasha, za ku ga sabani mai tsanani a bayana, to na horeku da sunnata da sunnar Halifofina shiryayyu, ku rike su da turamen hakoranku, na haneku da fararrun al'amura, domin cewa kowacce bidi'a bata ce".
Abu Dawud da Tirmizi da Ibnu Majah da Ahmad ne Suka Rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi wa sahabbansa wa'azi wa'azi isasshe zukata sun ji tsoro daga gare shi, kuma idanuwa sun zubar da hawaye daga gare shi, Sai suka ce : Ya Manzon Allah ! kai ka ce wannan wa'azin bankwana ne, saboda abinda suka gani ya kai matukarsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a wa'azi, sai suka nemi wata wasiyyar dan su yi riko da ita a bayansa, Ya ce: Ina yi muku wasicci da tsoron Allah - Mai girma da daukaka -, hakan da aikata wajibai da barin abubuwan da aka haramta, da ji da bi, wato: Ga shugabanni, koda bawa ne ya shugabanceku ko ya yi rinjaye a kanku, wato ya zama mafi kaskantar halitta sarki akanku kada ku hanu daga hakan, ku bi shi dan tsoron tada fitintinu, domin shi wanda ya rayu daga cikinku zai ga sabani mai yawa. Sannan ya bayyana musu mafita daga wannan sabanin, hakan dayin riko da sunnarsa da sunnar Halifofi shiryayyu a bayansa, Abu bakar Al-Siddik, da Umar Dan Al-khaddab, da Usman Dan Affan, da Aliyu Dan Abu Dalib - Allah Ya yarda su baki daya -, da riketa da turamen hakora wato - turamen hakora na karshe -: Yana nufi da hakan kokari a lazimtar sunna da yin riko da ita, ya kuma gargadesu daga fararrun al'amura kirkirarru a Addini, domin cewa kowacce bidi'a bata ce.
Daga Samura ɗan Jundub da Mugira ɗan Shu'ubah - Allah Ya yarda da su - sun ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wanda ya zantar da wani Hadisi daga gareni yana ganin cewa shi ƙarya ne to shi yana ɗaya daga cikin maƙaryata".
Muslim ne ya rawaito shi a cikin Mukaddima din saAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa wanda ya riwaito wani Hadisi daga gare shi alhali shi yana sane ko yana zato ko yana rinjayar da zatansa cewa shi Hadisin ƙaryane a gare shi- tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -; to maruwaicinsa yana tarayya da mai ƙirƙirar wannan ƙaryar.
Daga Abu Sa'id Al-Khudri Cewa Manzon Allah SAW ya ce: "Kada ku rubuta komai daga gare ni, kuma duk wanda ya rubuta wani abu daga gare ni ba Qur'ani ba to ya goge shi, kuma ku zantar daga gare ni kada ku samu damuwa, kuma duk wanda yayi mun qarya yana sane to ya tanadi mazauninsa a Wuta"
Muslim ne ya rawaito shiDaga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Wanda ya yi mini karya da gangan to ya tanadi masaukinsa a wuta".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa wanda ya yi masa karya da gangan ta hanyar danganta masa magana ko aiki, to lallai cewa shi yana da mazauni a wuta; sakamako ne gare shi akan karyar da ya yi masa.
Daga Abu Huraira daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - lallai ya ce: "Za a samu wasu mutane a ƙarshen al'ummata suna zantar da ku abin da ku da iyayenku ba ku ji ba, to, kashedinku da su"
Muslim ne ya rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ba da labarin cewa wasu mutane a ƙarshen al'ummata za su bayyana suna ƙirƙirar ƙarya, kuma suna faɗin abin da wani kafinsu bai faɗa ba, suna ba da labarai da hadisan ƙarya abubuwan ƙirƙira, sai (Annabi) tsira da aminci su tabbata a gareshi ya umarcemu mu nisancesu kada mu zauna da su, kuma kada mu ji hadisansu; don kada ƙirƙirarran hadisin ya tabbata a cikin zukata, sai mu kasa kuɓuta daga su.