





























Hadeeth Cards
Da'wa cards that highlight great meanings from the noble prophetic hadiths in a simple style and attractive display that helps the Muslim to have a deeper understanding of his religion in an easy way
All
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Bala'i ba zai gushe ga mumini da mumina ba a kansa da ɗansa da dukiyarsa har sai ya gamu da Allah ba shi da wani laifi".
Tirmizi da Ahmad sun rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa bala'i da jarraba ba zasu gushe ba ga bawa mumini da mumina, a kansa da lafiyarsa da jikinsa, da 'ya'yansa na rashin lafiya ko mutuwa ko sabawa ko wanin haka, haka a dukiyarsa na bukatuwa da tafiya kasuwanci da sata, da tawayar rayuwa da kunci a cikin arziki, har Allah Ya kankare masa dukkanin zunubansa da kurarkuransa da wannan bala'in har idan ya gamu da Allah zai zama ya tsarkaka daga dukkan zunubai da kurakuran da ya aikata.
Allah madaukaki yana cewa: {Don haka kada ku sanya wa Allah kima, duk da cewa kun sani.} Ibn Abbas ya fada a cikin ayar cewa: "Aboki: shirka ne, wanda aka boye daga tururuwa da ke dauke da bakar leda a cikin duhun dare." Ya kamata a ce: Na rantse da Allah da rayuwarku, Ya-da-haka, da rayuwata, sai ta ce: Ba don wannan bala'in ba, da barayi sun zo mana, kuma ba don agwagi a cikin gida ba barayi sun zo gare mu, kuma maganar mutumin ga abokin nasa: Abin da Allah yake so da abin da yake so, da kuma maganar mutumin: Ba don Allah da haka-da-haka ba, kuma kada a sanya hakan. Wannan duk shirka ne. "Dan Abbas Allah ya kara yarda a gare su ya ce: cikin ayar: Al'Andadu: shine shirka, ita tafi daga tafiyar tururuwa akan fan dutse cikin duhun dare, kuma shine kace: na rantse da Allah da rayuwarka wane da rayuwata! kuma kace: ba dan karen nan ba da Barayi sun zo mana, ko kuma ba dan agwagin cikin gidan ba, da Barayi sun zo mana, da fadin Mutum ga abokin sa: Allah ya so kuma kaima ka so, da fadin Mutum: ba don Allah da wane ba,kada ka sanya kowa acikin ta,wan nan baki dayan sa akwai shirka acikin sa.Dan Abi Hatim ne ya rawaito shi.
Abu Hatim ya rawaito shiAllah - Albarkace da daukaka - ya ce: {Don haka kada ku sanya daidai da Allah, duk da cewa kun sani.Saboda haka ya hana mutane daukar karin magana da sahihancin ra'ayi a gare shi a matsayin wani abu na bautarsa. Sun san cewa Allah shi kaɗai ne Mahalicci kuma Mai azurtawa. Kuma cewa wadannan takwarorin ba su da karfi, matalauta ne, kuma ba su da komai game da lamarin, kuma Ibn Abbas - Allah ya yarda da shi - ya san takwarorinsu tare da abokan tarayya, kuma ya ambaci misalai don daukar su, kuma ya buya daga boyewar tururuwa a kan dutsen sumul mai santsi a cikin duhun dare, sannan ya ambata misalan hakan: wanda ake rantsuwa da shi Da wani abu ba Allah ba, kuma mafi girma shi ne a daidaita Allah da shi sai a ce: Na rantse da Allah da raina, ko kuma in kalli abin ba tare da dalili ba, kuma al'amarin ba zai koma ga Allah ba, sai ta ce: Idan ba don kare ba, wannan da ya tsare mu, da barayi sun zo mana, ko ya ce: Idan ba don agwagwar da ke cikin gidan ba, zai yi mana gargaɗi idan wani ya shigo gidan Barayi, kuma daga shirka: maganar mutum ga mai shi: Abin da Allah yake so da abin da yake so, da kuma fadin mutum: Idan ba don Allah da haka-da-haka ba, kada a sanya haka-da-haka a ciki, to ya nanata cewa duk wannan karamar shirka ce, kuma idan wanda ya ce ya yi imani cewa mutumin ko agwagwar ko kare ne mai tasiri a kansa maimakon Allah to Babban lalata.
Daga Huzaifa - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Kada ku ce : Allah Ya so wane ma ya so, saidai ku ce: Allah ne Ya so, sannan wane ma ya so".
Abu Dawud da Nasa'i cikin alkubra haka Ahmad suka ruwaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya hana musulmi ya ce a zancensa: Allah Ya so wane ma ya so", ko Allah Ya so da wane; hakan domin ganin damar Allah da nufinSa a wawaice suke, wani ba ya tarayya daShi a cikinsu, a cikin amfani da Waw (da) a adafi alamtarwa ne na hada wani tare da Allah da daidaitawa a tsakaninsu. Saidai ya ce: Allah ne Ya so, sannan wane ma ya so, Sai ya sanya ganin damar bawa mai bi ce ga ganin damar Allah ta hanyar fadin: "Sannan" canjin "da"; domin "sannan" tana fa'idantar da bibiya da kuma jinkiri.
Daga Abdullahi Dan Mas'ud -Allah yarda da shi ya ce: "a rantse da Allah ina mai karya shi ne mafi soyuwa a gareni da na rantse da waninsa
Ibnu Abi Hatim ya rawaito shi - Abdurrazak Ya Rawaito shiDan Mas'ud yana cewa Rantsuwa ta da Allah alhalin ina Mai karya cikin hakan asama hakan zai faru to hakan yafi mun soyuwa a gareni da in rantse da wanin Allah akan wani Abu kuma ina da gaskiya a kansa, kuma cewa ya rinjayar da rantsuwa da Allah yana mai karya kan rantsuwa da waninsa yana mai gaskiya; Domin Rantsuwa da Allah cikin hakan akwai a cikinsa wani yanayin aikin lada na kadaita Allah, kuma da laifin Karya a cikinsa, kuma Rantsuwa da waninsa yana mai gaskiya a cikinsa akwai ladan gaskiya kuma da laifin Shirka, kuma ladan kadaita Allah yafi girma kan ladan gaskiy, kuma laifin karya yafi sauki akan laifin shirka
Daga Abu Sa'id al-Khudri - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Lallai za ku bi hanyoyin waɗanda zo kafinku, taki da taki, zira'i da zira'i, har da ko sun shiga ramin damo ne sai kun bi su" Muka ce: Ya manzon Allah ! Yahudawa da Nasara? ya ce: "To su wa?".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi(Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi yana bada labarin abinda halin da sashin al'ummarsa zasu kasance akansa bayan zamaninsa, shi ne bin hanyar Yahudawa da Nasara a aƙidunsu da ayyukansu da al'adunsu bi na zirfafawa mai tsanani taki da taki, zira'i da zira'i, har da a ce su shiga ramin damo to da waɗannan zasu shige shi suna bayansu.
Daga Abu Huraira Allah - Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: "Wanda ya yi kira zuwa ga shiriya yana da lada kwatankwacin ladaddakin wadanda suka bi shi, ba za’a tauye komai daga ladansu ba, wanda ya yi kira zuwa ga bata yana da zunubi kwatankwacin zunuban wadanda suka bi shi, ba za’a tauye komai daga zunubansu ba".
Muslim ne ya rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bayyana cewa wanda ya shiryar ya kwadaitar da mutane kan hanyar da aciknta akwai gaskiya da alheri da fada ne ko aikatawa yana da ladan wanda ya bi shi ba tare da antauye komai daga ladan mai bin ba. Wanda ya kira mutane zuwa hanyar karya da sharri a cikinta akwai zunubi da kuskure ko wani al'amarin da ba ya halatta, na fadane ko aikatawa, ya kasance akwai zunubi akansa kwatankwacin zunubin wanda ya bi shi ba tare da an tauye komai daga zunubansu ba.
Daga Dan Abbas -Allah ya yarda dasu-ya ga wani mutum ya firgita yayin da yaji wani hadisi game da Annabi -tsira da aminci su tabbata a gare shi- game da sifofin Allah-don nuna rashin yardarsa da haka- sai yace: Meye banbancin wadannan?zuciyarsu na yin taushi in suka ji ayoyi bayyanannu,su kuma rikice in suka ji ayoyi masu rikitarwa".
Ibnu Abi Asim ya rawaito shi - Abdurrazak Ya Rawaito shiIbn Abbas -Allah ya yarda dasu- ya tsani duk mai tsorata a dalilin ya ji hadisai da suke magana akan siffofinAllah har ma su razana don kin abin,ba sa imani da abin da ya zo daga manzon Allah -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- wanda suka san ma'anarsa daga Alkur'ani wanda shi ne gaskiya, mumini ba ya kokwanto a cikinsa, wasa kuma sai suke daukarsa ba a ma'anarsa da Allah yake nufi ba sai su halaka a dalilinhaka
Daga Abdullahi Dan Mas’ud - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agar shi - ya ce: "Canfi shirka ne, canfi shirka ne, canfi shirka ne, - sau uku -", babu wani a cikinmu saidai, saidai cewa Allah - Mai girma da daukaka - Yana tafiyar da shi da dogara (ga Allah).
Abu Dawud da Tirmizi da Ibnu Majah da Ahmad ne Suka Rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi gargadi daga canfi shi ne canfi daga kowanne abu, abin ji ne ko abin gani, daga tsuntsayene ko dabbobi ko masu larurori ko lambobi ko kwanuka ko makamancin hakan, kadai ya ambaci canfi ne domin cewa shi ne ya fi shahara a lokacin Jahiliyya, asalinsa shi ne sakin tsuntsu a lokacin fara wani aiki na tafiya ne ko kasuwanci ko makamancin hakan, idan ya tashi a bangaren dama sai ya yi yunkuri ya ci gaba da abinda yake nufi, idan ya tashi bangaren hagu sai ya canfa ya kame daga abinda yake nufi. Ya bada labarin cewa hakan shirka ce, kadai canfi ya zama shirka; domin ba mai zuwa da alheri sai Allah, kuma ba mai tunkude sharri sai Allah Shi kadai ba shi da abokin tarayya. Dan Mas'ud - Allah Ya yarda da shi - ya ambaci cewa wani abu na canfi zai iya darsuwa a zuciyar musulmi, saidai ya wajaba akansa ya tunkude shi da dogaro ga Allah, tare da aikata sabubba.
Daga Abdullahi Dan Shikkhir - Allah Ya yarda dashi - ya ce: Na tafi a cikin jama'ar Banu Amir zuwa ga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, Sai muka ce: Kai ne shugabanmu, sai ya ce: "Shugaba Shi ne Allah", muka ce: Mafificinmu a fifiko, kuma mafi girmanmu a kyauta, sai ya ce: "Ku fadi maganarku, ko wani bangare na maganarku, kada Shaidan ya yi amfani daku".
Abu Dawud ne ya Rawaito shi da Kuma AhmadWasu jama'a suka zo wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, lokacin da suka iso wurinsa sai suka fadi - suna masu yabonsa - wasu daga cikin kalmomin da tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ki su, sai suka ce ; "Kai ne shugabanmu", sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: "Shugaba (Shi ne) Allah" Cikakken shugabanci nasa ne akan halittarSa su bayinSa ne. Suka ce : Kai ne "Mafificinmu a fifiko" kuma mafi daukakarmu a daraja da daukaka. kuma kaine "Mafi girmanmu a kyauta" mafi yawaitawarmu a kyauta da daukaka da daraja. Sannan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya nuna musu su fadi maganarsu ta al'ada kada su kallafawa kansu lafazai, kuma kada Shaidan ya Ja su zuwa wuce gona da iri da kanbawar da zata afkar cikin abinda aka haramta na shirka da hanyoyinta.