





























Hadeeth Cards
Da'wa cards that highlight great meanings from the noble prophetic hadiths in a simple style and attractive display that helps the Muslim to have a deeper understanding of his religion in an easy way
All
Daga Buraidah - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce -: "Lallai alƙawarin da ke tsakanin mu da su (shi ne) sallah, wanda ya barta, to, haƙiƙa ya kafirta".
Tirmizi da Nasa'i da Ibnu Majah da Ahmad ne Suka rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bayyana cewa alƙawari tsakanin musulmai da wasunsu daga kafirai da munafikai (shi ne) sallah, wanda ya barta to haƙiƙa ya kafirta.
Daga Umar Dan Khaɗɗab - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da a mincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Lallai Allah - mai girma da daukaka - yana hanaku ku rantse da iyayenku", Umar ya ce: Na rantse da Allah ban yi rantsuwa da su ba tunda na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana hani daga garesu da gangan ko ina mai ciratowa (daga wanina).
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa Allah - Madaukakin sarki - Yana hani daga rantsuwa da iyaye, duk mai nufin yin rantsuwa kada ya rantse da kowa sai da Allah, kada ya rantse da waninsa. Sannan Umar Dan Khaddab - Allah Ya yarda da shi - ya ambaci cewa shi bai sake rantsuwa da su ba tunda ya ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana hani game da hakan, bada gangan ba, ba kuma yana mai cirato rantsuwa da wanin Allah daga waninsa ba.
Daga Abdullahi Dan Mas’ud - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Farkon abinda za’a yi huknci a tsakanin mutane a ranar Alkiyama akan jini ne".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ambaci cewa farkon abinda za’a yi hukunci a tsakanin mutane a zalincin junansu a ranar Alkiyama: A jinane ne, kamar kisa da raunuka.
Daga Dan Abbas - Allah Ya yarda da su - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya wuce wasu kaburbura biyu, sai ya ce: "Lallai su ana musu azaba, kuma ba’a yi musu azaba dan wani babban laifi ba, amma dayansu ya kasance ba ya suturta daga fitsari, amma dayan ya kasance yana tafiya da annamimanci" Sannan ya dauki wani danyan itacan dabino, sai ya raba shi biyu, sai ya kafa daya a kowanne kabari, suka ce: Ya Manzon Allah, meyasa ka aikata hakan, sai ya ce: "Watakila a saukaka musu muddin dai basu bushe ba".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya wuce wasu kaburbura biyu sai ya ce: Lallai masu kaburburan nan biyu ana musu azaba; kuma ba'a yi musu azaba dan wani babban laifi ku a ganinku ba, duk da yake mai girma ne a wurin Allah, amma dayansu ya kasance ba ya himmantuwa da kiyaye jikinsa da tufafinsa daga fitsari har sai ya biya bukatarsa, dayan kuma ya kasance yana tafiya da annamimanci a tsakanin mutane, sai ya dakko zancen wani da nufin cutarwa da sanya sabani da fitina a tsakanin mutane.
Daga Anas - Allah Ya yarda da shi -: Cewa wani mutum ya tambayi Annabi - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - daga alkiyama, sai ya ce: Yaushe ne alkiyama? Ya ce: "Mai ka tanadar mata?" Ya ce: Babu komai, sai dai ni ina son Allah da ManzonSa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai ya ce; "Kai kana tare da wanda ka so" Anas ya ce: Bamu taba farin ciki da wani abu ba, irin farin cikinmu da faɗin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: "Kai kana tare da wanda ka so" Anas ya ce: Ni ina son Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da Abubakar, da Umar, kuma ina kaunar in kasance tare da su dan son da nake musu, koda ban yi aiki irin aikinsu ba.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiWani mutumin karkara irin waɗanda suke zama a sahara ya tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: game da lokacin tashin alkiyama? Sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi Ya ce masa: Meka tanadar mata na aiki na gari? Sai mai tambayar ya ce: Ban tanadi wani aiki mai yawa ba sai dai ni ina son Allah da ManzonSa, bai ambaci wanin hakan ba daga ayyuaka na zuciya da jiki da dukiya; domin su dukkaninsu rassa ne ga soyayya masu jerantuwa ne akanta, kuma domin soyayya ta gaskiya tana zaburar da kokarin yin aiki na gari. Sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi Ya ce masa: Lallai kai kana tare da wanda ka so a aljanna. Sai sahabban Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - suka yi farin ciki mai girma da wannan busharar. Sannan Anas ya bada labarin cewa shi yana son Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da Abubakar, da Umar, kuma yana kaunar ya kasance tare da su, koda aikinsa bai zama irin aikinsu ba.
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Shin bana ba ku labari ba game da Jujal, wanda babu wani annabi da ya zantar da mutanensa shi ? lallai shi mai ido ɗaya ne, kuma shi zai zo a tare da shi akwai kwatankwacin aljanna da wuta, wacce zai ce ita ce aljanna to ita ce wuta, lallai ni ina gargaɗarku kamar yadda (Annabi) Nuhu ya gargaɗi al'ummarsa da shi".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana ba wa sahabbansa labari game da Dajjal da siffofinsa da almominsa da abinda wani annabi a gabaninsa bai zantar da shi ba, daga hakan: Cewa shi mai ido ɗaya ne. Kuma Allah - Maɗaukakin sarki - Ya sanya masa kwatankwacin aljanna da wuta, gwargwdan ganin ido. Sai dai aljannarsa wuta ce, kuma wutarsa aljanna ce, wanda ya bi shi zai shigar da shi wannan aljannar a abinda mutane suke gani, sai dai cewa ita wuta ce mai ƙuna, wanda ya saɓa masa zai shigar da shi wutar a abinda mutane suke ganinsa, sai dai ita aljanna ce mai daɗi. Sannan annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi gargaɗi daga fitinarsa kamar yadda (Annabi) Nuhu ya gargaɗar da mutanensa shi.
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Mutum yana kan Addinin abokinsa, saboda haka dayanku ya duba wanda zai yi abokantaka (da shi)".
Abu Daud ne ya ruwaito shi da Kuma Tirmizi da AhmadAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa mutum yana kamanceceniya da abokinsa amintacce a rayuwarsa da kuma al'adarsa, kuma abokantaka tana tasiri a ɗabi'u da yanayi da tasarrufi, saboda haka ne ya nunar zuwa kyakkyawan zabin aboki; domin aboki yana shiryar da abokinsa akan imani da shiriya da alheri, kuma yana kasancewa taimako ga abokinsa.
Daga Abu Huraira Allah - Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: "Ku yi gaggawa da ayyuka (na alheri), wasu fitinu kamar yankin dare ne mai duhu, mutum zai wayi gari yana mumini ya kai yammaci yana kafiri, ko ya yammanta yana mumini ya wayi gari yana kafiri, zai sayar da addininsa da wata haja ta duniya".
Muslim ne ya rawaito shiAnnabi - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - yana kwaɗaitar da mumini akan gaggawa da yawaita ayyuka na gari kafin wuyatarsu da shagaltuwa daga gare su da zuwan fitinu da shubuhohin da zasu hana aikata su, kuma zasu toshe su, masu duhu ne kamar yankin dare, yana cakuɗe gaskiya da ƙarya a cikinsu, sai banbancewa tsakaninsu ta yi wuya a wurin mutane, saboda tsananinsu mutum zai dinga kaikawo har cewa shi zai wayi gari yana mumini ya yanmanta yana kafiri, kuma ya yanmanta yana mumini ya wayi gari yana kafiri, zai bar addininsa da wani ɗan jin daɗi na duniya mai gushewa.
Daga Zainab 'yar Jahsh - Allah Ya yarda da ita - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya shiga gurinta a firgice yana cewa; "Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, azaba ta tabbata ga larabawa daga sharrin da ya kusanto, a yau an buɗe katangar Yajuju da Majuju kwatankwacin hakan" sai ya kewaye ɗan yatsansa babba da wanda yake biye da shi. Zainab 'yar Jahsh ta ce : Sai na ce ya Manzon Allah: Shin zamu halaka alhali a cikinmu akwai salihai? ya ce: "Eh, idan barna ta yi yawa".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya shiga gurin Zainab 'yar Jahsh - Allah Ya yarda da ita - a firgice a tsorace, alhali shi yana cewa: Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, dan sanarwa da tinanin afkuwar wani al'amari abin ki da zai faru, kuma babu tsira daga gare shi sai fakewa ga Allah - tsarki ya tabbatar maSa -, sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: Kaico ya tabbata ga Larabawa daga wani sharrin da afkuwarsa ya kusanto, yau an buɗe katangar Yajuju da Majuju, shi ne katangar da Zulkarnaini ya ginata, misalin wannan; sai ya kewaye ɗan yatsansa babba da wanda ke biye da shi. Sai Zainab - Allah Ya yarda da ita - ta ce : Yaya Allah Zai halakar da mu alhali a cikinmu akwai muminai na gari? Sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce mata: Idan barna ta yi yawa da fasikanci da fajirci da sabo, da zina, da giya, da wasunsu, to halaka zata game kowa da kowa.