





























Hadeeth Cards
Da'wa cards that highlight great meanings from the noble prophetic hadiths in a simple style and attractive display that helps the Muslim to have a deeper understanding of his religion in an easy way
All
Daga Aliyu - Allah Ya yarda da shi -: Cewa Faɗima - Allah Ya yarda da ita - ta zo wajen Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - tana kawo ƙarar abinda take gamuwa da shi a hannunta na daka, kuma labari ya isar mata cewa wani bawa ya zo masa, bata same shi ba, sai ta ambaci hakan ga A'isha, lokacin da ya dawo sai A'isha ta ba shi labari, (Aliyu) ya ce: Sai ya zo mana alhali mun kwanta, sai muka tafi muka tashi, sai ya ce: "Ku zauna a wurinku" sai ya zo sai ya zauna tsakani na da ita, sai naji sanyin diga-digansa akan cikina, sai ya ce: "Shin bana shiryar daku ga mafi alheri daga abinda kuka tambaya ba? idan kun kwanta - ko kunzo shinfiɗarku - to ku yi tasbihi sau talatin da uku, ku yi hamdala sau talatin da uku, ku yi kabbara sau talatin da da hudu, to shi ne mafi alheri gareku daga dan aiki".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiFaɗima - Allah Ya yarda da ita - 'yar manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - takai koken abinda take fama dashi na gurbin kayan niƙan da take niƙawa, lokacin da ribatattu suka zo wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai ta tafi zuwa gare shi zata tambaye shi ɗan aiki daga waɗannan ribatattun; dan ya tsaya a matsayinta akan ayyukan gida, sai dai cewa bata sameshi a gidansa ba, sai ta samu A'isha - Allah Ya yarda da ita -, sai ta bata labarin hakan, Lokacin da tsira da amincin Allah su tabbata agare shi dawo sai Nana A'isha ta ba shi labarin zuwan Faɗima wurin shi dan ta tambaye shi ɗan aiki ne, sai Annbi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya zo wurin Nana Faɗima da Aliyu - Allah Ya yarda da su - a gidansu alhali su suna kan shinfiɗa suna shirin barci, sai ya zauna tskaninsu har Aliyu - Allah Ya yarda da shi - ya ji sanyin diga-digan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - akan cikinsa, sai ya ce: Shin bana sanar daku mafi alheri daga abinda kuka tanbayeni ba akan na baku ɗan aiki? Suka ce: Eh, sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Idan kun kwanta dan yin bacci da daddare, to ku yi kabbara sau talatin da huɗu, da faɗin: Allahu Akbar, ku yi tasbihi sau talatin da uku, da faɗin: Subhanallahi, ku yi hamdala sau talatin da uku, da faɗin: Alhamdulillah; to wannan zikirin shi ne mafi alheri gareku daga ɗan aiki.
Daga Abdullah dan Khubaib - Allah Ya yarda da shi - cewa shi ya ce: Mun fita cikin dare da akai ruwa da duhu mai tsanani, muna neman Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi mana sallah, ya ce: Sai na riske shi, sai ya ce: "Ka ce", ban cekomai ba, sannan ya ce: "Ka ce", ban ce komai ba, sai ya ce: "Ka ce" sai na ce: Me zan ce? Ya ce: Ka ce: "{Ka ce Shi ne Allah Shi kadai} da falaki da Nasi (Wato ka karanta Qul huwa da Falaki da Nasi) lokacin da ka wayi gari da kuma lokacin da ka yi maraice sau uku sun isheka komai".
Abu Dawud da Tirmizi da Nasa'i ne Suka Rawaito shiSahabi mai girma Abdullah dan Khubaib - Allah Ya yarda da shi - yana bada labarin: Cewa sun fita a dare mai yawan ruwa, kuma duhu ya kasance mai tsanani dan neman Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -; Domin ya yi musu sallah, sai suka same shi, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce masa: "Ka ce" wato ka karanta, bai karanta komai ba, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya sake fada masa, sai Abdullahi ya ce: Mezan karanta ya Manzon Allah? sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Ka karanta Surat Al-Ikhlas {Ka ce Shi ne Allah Shi kadai}, da Falaki da Nasi {Ka ce ina neman tsari da Ubangijin safiya}, da {Ka ce ina nemn tsari da Ubangijin mutane}, a lokacin yammaci, da lokacin safiya, sau uku za su kiyayeka daga kowanne sharri, kuma zasu kareka daga kowanne mummunan abu.
Daga Aban ɗan Usman ya ce: Na ji Usman ɗan Affan - Allah Ya yarda da shi - yana cewa: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: "Wanda ya ce: Da suna Allah wanda wani abu ba ya cutuwa tare da sunanSa a cikin ƙasa, ko cikin sama, Shi ne Mai yawan ji Masani”. sau uku, wani bala'i na fuj'a ba zai same shi ba har sai ya wayi gari, wanda ya faɗeta lokacin da ya wayi gari sau uku, wani bala'i na fuj'a ba zai same shi ba har sai shiga maraice", ya ce: Sai shanyewar ɓarin jiki ya samu Aban ɗan Usman, sai mutumin da ya ji hadisin daga gare shi ya fara kallonsa, sai ya ce masa: Me yasa meka kake kallona? Na rantse da Allah ban yi wa Usman ƙarya ba, kuma Usman bai yi wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ƙarya ba, sai dai ranar da abinda ya sameni ya sameni a cikinta na yi fushi sai na manta ban fadi addu'ar.
Abu Dawud da Tirmizi da Nasa'i cikin alkubra da Ibnu Majah haka kuma AhmadAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa wanda ya ce da safiyar kowace rana bayan ɓullowar alfijir, da yammacin kowane dare kafin faɗuwar rana sau uku: (Da sunan Allah) ina neman taimako ina neman kiyayewa daga dukkan abinda yake cutarwa (wanda ba ya cutarwa tare da) ambatan (sunanSa), ko (wane abu) duk irin girman da ya yi (a cikin ƙasa) da abinda yake fitowa daga gareta na bala'i (ko a cikin sama) mai saukowa daga gareta na bala'i (Shi Mai yawan ji ne) ga maganganun mu (Masani) da halayenmu. Wanda ya faɗeta lokacin da ya shiga maraice bala'i ba zai same shi ba bagtatan har sai ya wayi gari, wanda kuma ya faɗeta lokacin da ya wayi gari bala'i bagtatan ba zai sameshi ba har sai ya shiga maraice. Sai maruwaicin hadisin Aban ɗan Usman ya samu cutar shanyewar ɓarin jiki; shi ne shanyewar ɓarin jiki, sai mutumin da ya ji hadisin a wunsa ya fara kallon Aban yana mai mamaki! sai mutumin ya ce: Me ya sameka ne kake kallona?! Na rantse da Allah ban yi wa Usman ƙarya ba, kuma Usman bai yi wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ƙarya ba, saidai a ranar da abin ya sameni a cikinta Allah bai ƙaddara mini faɗinta ba, fushi ne ya sameni sai na manta in faɗi waɗannan kalmomin da aka ambata.
An rawaito daga Anas -Allah ya yarda da shi- ya ce "wani Mutum yace: Ya Manzon Allah wani Mutum daga cikin mu yakan gamu da Danuwansa ko Abokinsa shin ya durkusa masa, sai ya ce to ya rikeshi ya ya sunbance shi ? sai yace aa sai ya ce to ya kama hannunsa su gaisa? ya ce: Ey"
Al-Tirmithi Ya Rawaito shi - Ahmad ne ya rawaito shiDaga Sa'ad - Allah Ya yarda da su - ya ce: Wani balaraben kauye ya zo wurin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai ya ce: Ka sanar maganar da zan fada, ya ce: "Ka ce: Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah Shi kadai Yake ba Shi da abokin tarayya, Allah ne Mafi girma Mai girma, godiya ta tabbata ga Allah mai yawa, tsarki ya tabbata ga Allah Ubangijin talikai, babu dabara babu karfi sai ga Allah Mabuwayi Gwani" sai ya ce: Wadannan na Ubangijina ne, to ni me gareni? ya ce: "Ka ce: Ya Allah Ka gafarta mini Ka ji kaina Ka shiryar dani Ka azurtani".
Muslim ne ya rawaito shiWani mutum daga mazauna kauye ya tambayi Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya sanar da shi wani zikirin da zai fade shi, Sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Ka ce: "Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah Shi kadai yake ba da abokin tarayya" ya fara da shahada ta tauhidi, ma'anarta babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, "Allah ne Mafi girma Mai girma" Wato: Allah ne Mafi girma daga kowanne abu kuma Mafi girma, "Godiya ta tabbata ga Allah mai yawa" Wato: Godiya ta tabbata ga Allah mai yawa, ga siffofinSa da ayyukanSa da ni'imominSa wadanda ba'a iya lissafe su, "Tsarki ya tabbata ga Allah Ubangijin talikai" Wato: Ya tsarkaka Ya tsarkaka daga tawaya, "Babu dabara babu karfi sai ga Allah Ubangiji Mabuwayi Gwani" Wato: Babu dabara ta canza wa daga wani hali zuwa wani halin sai ga Allah da taimakonSa da gamkatar dinSa, sai mutumin ya ce: Wadannan kalmomin sun tabbata ga Ubanigijina dan ambatonSa da girmamaShi, to ni meye gareni na addu'a ga kaina? Sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Ka ce: "Ya Allah Ka gafarta mini" Da shafe munanan ayyuka da suturta su, "Ka jikaina" Ta hanyar sadar da abubuwan amfani da maslahohi na Addini da duniya gareni, "Ka shiryr da ni" ga mafi kyawun halaye kuma zuwa ga hanya mikakkiya, "Ka azirtani" Dukiya ta halal da lafiya da dukkanin alheri da lafiya.
An rawaito daga Shakl Bn Humaid -Allah ya yarda da shi- Na ce: Ya Manzon Allah ka koyamun wata Addu'a ya ce kace: "Ya Ubangiji ina neman tsarinka daga sharrin jina, da kuma sharrin Ganina, da kuma Sharrin Harshena, da kuma Sharrin Zuciyata, da kuma Sharrin farjina"
Al-Tirmithi Ya Rawaito shi - Al-Nasa'i Ya Rawaito shi - Abu Daud Ya Rawaito shi - Ahmad ne ya rawaito shiAn rawaito daga Abhu Huraira -Allah ya yarda da shi- daga Annabi ya ce: "Allah baiyi izini ga Annabi da wani Abu ba kamar yadda yayi izini da ya kawata Muryasa da Qur'ani"
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiAn rawaito daga Abu Huraira -Allah ya yarda da shi- cewa Manzon Allah ya ce:"Duk wanda aka yambaye shi wani ilimi sai ya boye shi to za'a yi masa linzami da shi na wuta a Ranar Alkiyama"
Ibnu Majah ne ya Rawaito shi - Al-Tirmithi Ya Rawaito shi - Abu Daud Ya Rawaito shi - Ahmad ne ya rawaito shiDaga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wanda ya rantse sai ya ce a cikin rantsuwarsa: Na rantse da Lata da Uzza, to ya ce: Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, wanda ya ce wa abokinsa: Zo mu yi caca tare, to ya yi sadaka".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana gargaɗi akan rantsuwa da wanin Allah; inda mumini ba ya rantsuwa sai da Allah kadai, kuma yana bada labarin cewa wanda ya yi rantsuwa da wanin Allah; kamar wanda ya yi rantsuwa ga misali da: Lata da Uzza - su biyun gumaka ne da ake bauta musu a lokacin Jahiliyya kafin Musulunci - to ya wajaba akansa ya ce yana mai riskar abin da ya fada da kansa: Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, dan kuɓuta daga shirka, da kaffara daga wannan rantsuwar tasa. Sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya bada labarin cewa wanda ya ce wa abokinsa: Zo mu yi wasan caca, - ita ce mutum ko sama da haka su yi rinjayeyeniya akan wata dukiyar da wani zai ɗauka a tsakaninsu, kuma kowanne daya daga cikinsu ba ya zama haka kodai yaci riba a cikinta ko kuma ya faɗi -; to an so ya yi sadaka da wani abu dan kaffara daga abinda ya yi kira zuwa gare shi.