





























Hadeeth Cards
Da'wa cards that highlight great meanings from the noble prophetic hadiths in a simple style and attractive display that helps the Muslim to have a deeper understanding of his religion in an easy way
All
Daga Abdullah bn Masoud - Allah ya yarda da shi - tare da rahoto: "Za a shigar da Jahannama a wannan rana a kansa saboda iyayengiji dubu saba'in, tare da kowace sarauta ta sarakuna dubu saba'in da suke jan ta."
Muslim ne ya rawaito shiRanar tashin kiyama za'a kawo mata wuta da igiya dubu saba'in, wanda zata jagoranta, kuma a kowace igiya sarakuna dubu saba'in zasu mata jagora da ita.
Daga Anas ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Ba'a dawo da addu'a tsakanin kiran sallah da iƙama".
Abu Dawud da Tirmizi da Nasa'i ne Suka Rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana falalar addu'a tsakanin kiran sallah da iƙama, kuma cewa ba'a dawo da ita kuma ta cancanci amsawa, to ku roƙi Allah a cikinsa.
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana cewa: ’’ Ya Allah Ka gyara mini Addini na wanda shi ne ƙashin bayan al’amari na, kuma Ka gyara mini duniya ta wacce na ke rayuwa a cikinta, Ka kuma gyara mini lahira ta wacce a cikinta ne makoma ta take, Ka sanya rayuwa (ta zamo) ƙarin duk wani alheri gareni, kuma Ka sanya mutuwa ta zamo hutu ce a gare ni daga dukkan wani sharri’’.
Muslim ne ya rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - Ya yi addu'a da wata addu'a wacce ya haɗo a cikinta tushen manyan ɗabi'u waɗanda aka aiko shi dan cikasu; su ne gyara Addini, da duniya, da lahira, sai ya nemi shayarwar gyaran waɗannan abubuwan masu tattarowa guda uku a cikin wannan taƙaitaccen lafazin, sai ya fara da gyaran Addini da shi ne (za'a samu) gayaran halin gidaje biyun (duniya da lahira) sai ya ce: (Ya Allah Ka gyara mini Addini na) shi ne Ka datar dani da tsayuwa da ladubbansa ta cikakkiyar fuska mafi cika. (Wanda shi ne kashin bayan al'amarina) mai kiyayewa ga dukkan al'amurana, idan Addinina ya ɓaci to al'amurana sun ɓaci, na taɓe na yi asara, kuma cewa gyaruwar Addini abin nema baya cika sai da gyaruwar duniya , sai ya ce: (Ka gyara mini duniyata) ta hanyar lafiyar jiki da aminci, da arziƙi, da mata ta gari, da zuriya kyakkyawa da abinda nake buƙatuwa zuwa gare shi, kuma ya zama na halal, mai taimako akan yi maKa biyayya, sannan ya ambaci uzuri a cikin tambayarsa gyaranta; shi ne ya ce: (Wacce a cikinta rayuwata ta ke) da wurin rayuwata da zamanin rayuwata. (Kuma ka gyara min lahirata wacce a cikinta ne makomata take) da komawata zuwa haɗuwa da Kai, hakan da gyaruwar ayyuka, da datarwar Allah ga bawa akan ibada da ikhalasi, da kyakkyawar cikawa. Kuma tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya jeranta lahira bayan duniya; domin ta farko ita ce tsanin gyaran ta biyu, wanda ya daidaita a duniyarsa daidai da abinda Allah yake so, to lahirarsa ta daidaita kuma ya azirta a cikinta. (Ka sanya rayuwa) da tsawon rayuwa (ƙari gareni a kowane alheri) da zan yawaita ayyuka na gari a cikinta. (Ka sanya mutuwa) da gaggautota (hutu gareni daga kowane sharri) da fitina da jarraba da ibtila'i da saɓo da rafkana, da kuma kuɓuta daga wahalar duniya da baƙin cikinta, da samun hutu.
Daga Abu Musa - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - cewa shi ya kasance yana addu'a da wannan addu'ar. "Ya Ubangiji Ka gafarta mini kuskurena da wautata, da wuce gona da irina a cikin dukkan al'amarina, da abinda Kaine Mafi sani da shi daga gareni, ya Allah Ka gafarta mini kurakuraina, da gangancina da jahilcina da kakacina, dukkan hakan daga garenin ne, ya Allah Ka gafarta mini abinda na gabatar da abinda na jinkirtar, da abinda na ɓoye da abinda na bayyana, kaine Mai gabatarwa kuma Kaine Mai jinkirtarwa, kuma kaine Mai iko akan dukkan komai".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiYa kasance daga addu'o'in Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - mai tattarowa faɗinsa: "Ya Ubangiji Ka gafarta mini kurakuraina" da zunubina, "da jahilcina' da abinda ya afku daga gareni ba tare da sani ba. "Da wuce gona da iri na a dukkan al'amarina" da kasawata da wuce gona da iri na. "Da abinda Kaine Mafi sani da shi daga gareni" Ka san shi Allah ni kuma na manta shi. "Ya Allah Ka gafarta mini kurakuraina da gangancina" da abinda ya bijiro na ganganci daga gareni da ilimi daga gareni da zunubai. "Da (aiki) da gaske daga gareni da kakaci na" da abinda ya bijiro daga kakaci, da abinda ya afku daga gareni a hali biyun. "Dukkanin wannan daga gareni ne" inda na tattara abinda aka ambata daga zunubai da aibuka. "Ya Allah Ka gafarta mini abinda na gabatar" da abinda ya shuɗe, "da abinda na jinkirtar" a abinda zai zo . "Da abinda na ɓoye" na ɓoye, "da abinda na bayyana" na bayyanar. "Kai ne mai gabatarwa kuma Kaine Mai jinkirtarwa" Kana gabatar da wanda kake so daga halittarKa zuwa rahamarKa da dacewarKa da abinda Ka yarda da shi, kuma Kaine Mai jninkirtarwa Kana jinkirtar da wanda Kake so daga hakan da taɓarwarKa gare shi , bamai gabatar da abinda Ka jinkirtar, kuma ba mai jinkirtar da abinda Ka gabatar daga al'amura. "Kai ne Mai iko akan dukkan komai" Mai cikakken iko Mai cikakken nufi, Mai aikata abinda Ka so.
Daga Ɗan Umar - Allah Ya yarda da su- ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - bai kasance yana barin waɗannan addu'o'i ba lokacin da ya yi yammaci ko ya wayi gari: "Ya Allah lallai ni ina roƙonKa lafiya a duniya da lahira, ya Allah lallai ni ina roƙonKa rangwami da lafiya a Addini na da duniya ta da iyalaina da dukiyata, ya Allah Ka suturta al'aurata - ko: al'aurorina Ka amintar da tsorona, ya Allah Ka kiyayeni ta gabana, da bayana, da damana, da haguna, da samana, ina nemn tsarinKa kada a yaudareni da kisa ta ƙarƙashina".
Abu Daud da Nasa'i da Ibnu Majah da Ahmad ne suka Rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - bai kasance ba yana barin waɗannan addu'o'in ba lokacin da Ya yi yammaci da lokacin da ya wayi gari: (Ya Allah lallai ni ina roƙonKa lafiya), da kuɓuta daga masassara da masifu da tsanance-tsanance na duniya, da sha'awowi da fitintinu cikin Addini (a duniya da lahira) magaggauciya da majinkirciya. (Ya Allah lallai ni ina roƙonKa rangwame) da shafe zunubai da ƙetare su. (da lafiya) da kuɓuta daga aibuka, (a Addini na) daga shirka da bidi'o'i da saɓo, (da duniya ta) daga masifu da cuta da sharruka, (da iyalaina) matana da 'ya'ya na da 'yan uwana, (da dukiya ta) dukiyoyi na da aiki na. (Ya Allah Ka suturta al'aurori na) da abinda ke cikina na aibuka da ɓaci da taƙaitawa Ka shafe zunubai na, (Ka amintar da tsorace -tsorace na) razani na da tsoro na. (Ya Allah Ka kiyaye ni) Ka tunkuɗe bala'i daga gare ni daga abubuwa masu cutarwa da masifu, (ta gaba na da baya na, da dama na, da hagu na, da sama na) inda ya roƙi Allah Ya kiyaye shi ta kowane bangare: domin cewa masifu da aibuka kaɗai suna samun mutum ne kuma suna fuskantar sa daga ɗaya daga waɗannan ɓangarorin. (Ina neman tsarinKa kada a kashe shi ni) shi ne a kamani bagtatan, in mutu ba tare da na sani ba (ta ƙarƙa shi na) sh ne in halaka ta kisfewa.
Daga (Nana) A'isha Uwar muminai - Allah Ya yarda da ita - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya koya mata wannan addu'ar: "Ya Allah ina roƙon Ka dukkan alheri, magaggaucinsa da majinkircinsa, abin da na sani daga gare shi da abin da ban sani ba, kuma ina neman tsarinKa daga dukkan sharri magaggaucinsa da majinkircinsa, abin da na sani daga gare shi da abin da ban sani ba. Ya Allah ina roƙonKa mafi alherin abin da bawanKa kuma AnnabinKa ya roƙeKa, kuma ina neman tsarinKa daga sharrin abin da bawanKa kuma AnnabinKa ya nemi tsarin Ka da shi, ya Allah ina roƙonKa aljanna da abin da yake kusantota na magana ko aiki, kuma ina neman tsarinKa daga wuta, da abin da yake kusantota na magana ko aiki, ina rokonKa Ka sanya dukkan hukuncin da Ka hukunta gare ni ya zama alheri".
Ibnu Majah da Ahmad ne suka rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya koyawa Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - dunkulallun addu'o'i su ne addu'o'i huɗu: Na farko: Addu'a mai game kowane alheri: (Ya Allah ina roƙonKa dukkan alheri) dukkansa, (magaggaucinsa) makusanci a lokacinsa, (da majinkircinsa) na nesa, (abinda na sani daga gare shi) daga abinda Ka sanar da ni, (da abinda ban sani ba), daga abinda yake kasancewa a cikin saninKa - tsarki ya tabbatar maKa -. A cikinsa akwai fawwala al'amari zuwa ga Allah Masani Mai bada labari Mai sawwaƙawa; sai tsarki ya tabbatar maSa Ya zaɓawa musulmi maffificinsa kuma mafi kyansa, (Ina neman tsarinKa) ina neman tsarinKa ina kiyayewa (da Kai daga sharri dukkansa magaggaucinsa da majinkircinsa, abinda na sani da abinda ban sani ba). Addu'a ta biyu: Ita ce kiyayewar musulmi daga ya yi shisshigi a cikin addu'a (Ya Allah lallai ni ina roƙonKa) ina nemanKa (daga mafificin abinda bawanKa kuma AnnabinKa ya roƙeKa) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi, (ina neman tsarin Ka) ina fakewa ina nenam tsari (da Kai daga sharrin abinda bawanKa kuma AnnabinKa ya nemi tsarin Ka) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi , wannan addu'a ce da nema daga Allah Ya bawa mai addu'ar daga abinda Annabi Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya roƙe shi kuma ya neme shi ga kansa, ba tare da ƙididdiga nau'ikan abinda tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da shi ya roka ba. Addu'a ta uku: Neman shiga aljanna da nisantar wuta, shi abin neman kowane musulmi ne kuma matuƙar aikinsa: (Ya Allah ina roƙon Ka aljanna) da rabauta da ita (da abinda ya kusantota na magana ko aiki) na gari wanda zai yardar da kai, (ina neman tsarinKa daga wuta) inda babu tsari daga munanan ayyuka sai da luɗufinKa, (da abinda ya kusanto zuwa gareta na magana ko aiki) daga saɓon da zai sa fushinKa. Addu'a ta huɗu: Addu'a da yarda da hukuncin Allah (ina roƙonKa Ka sanya kowane hukuncin da Ka hukunta mini ya zama alheri) dukkan al'amarin da Allah Ya hukunta shi gareni Ya sanya shi mafi alheri gare ni, wannan yana daga addu'a da yarda da hukuncin Allah.
Daga Abdullahi ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - ya ce: Ya kasance daga addu'ar Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi -: "Ya Allah ina neman tsarinKa daga gushewar ni'imarKa, da juyawar lafiyarKa, da shammatar azabarKa, da dukkan fushinKa".
Muslim ne ya rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya nemi tsari daga abubuwa huɗu: Na farko: (Ya Allah ni ina neman tsarinKa daga gushewar ni'imarKa) ta Addini da duniya kuma in tabbata akan Musulunci, in nisanci faɗawa cikin saɓon da yake gusar da ni'imomi. Na biyu: (Da juyawar lafiyarKa) da canjata zuwa bala'i; to ina roƙonKa dawwamar lafiya, da kuɓuta daga radaɗi da cututtuka. Na uku: (Da shammatar azabarKa) daga bala'i ko saɓo, azaba da uƙuba idan suka zo fuj'a bagtatan, to babu wani lokaci a wannan dan tuba da riska, wanda aka shafa da su zai zama mafi girma kuma mafi tsanani. Na huɗu: (Da dukkan fushinKa) da sabubban da suke wajabta fushinKa; domin wanda Ka yi fushi da shi to haƙiƙa ya taɓe kuma ya yi asara. Haƙiƙa tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya zo da lafazin jam'i; dan ya ƙunshi sabubban fushinSa - tsarki ya tabbatar maSa Ya ɗaukaka - daga maganganu da ayyuka da ƙudirce-ƙudierce.
Daga Abdullahi ɗan Amr ɗan al-Aas - Allah Ya yarda da su - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana Addu’a da waɗannan kalomin: "Ya Allah ni ina neman tsarinKa daga rinjayar bashi, da rinjayar maƙiyi, da dariyar maƙiya".
Nasa'i ne ya ruwaito shi da AhmadAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya nemi tsari daga wasu al'amra: Na farko: (Ya Allah ni ina neman tsari) ina fakewa ina dogara (da Kai) bada wanin Ka ba, (daga rinjayar bashi) da rinjayarsa da baƙin cikinsa da takaicin sa, ina roƙonKa taimako akan biyansa da warware shi. Na biyu: (Rinjayar maƙiyi) da rinjayansa da ɗora shi akaina, ina roƙon Ka kame cutarsa, da nasararsa a kansa. Na uku: (Dariyar maƙiya) da farin cikin makiya akan abinda yake samun musulmai na bala'i da musiba.
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - Cewa shi ya kasance idan ya wayi gari yana cewa: "Ya Allah da (kiyayyewar) Ka ne muka wayi gari, kuma da (kiyayewar) Ka ne muka shiga maraice, da (al'amarin) Ka ne muka rayu, kuma da (al'amarin) Ka ne zamu mutu, kuma tashi (daga ƙabari) yana gareKa" Idan ya shiga maraice ya ce: "Da (kiyayewarka) Ka ne muka shiga maraice, kuma da (kiyayewar) Ka ne muka wayi gari, da (al'amarin) Ka zamu mutu, kuma tashi (daga ƙabari) yana gare Ka" ya ce: Wani lokaci kuma: "Makoma tana gare Ka".
Abu Dawud da Tirmizi da Nasa'i a cikin Alkubra da Ibnu Majah ne Suka Rawaito shi(Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya kasance idan ya wayi gari shi ne farkon yini tare da ɓullowar alfijir yana cewa: (Ya Allah da (kiyewar) Ka ne muka wayi gari) muna masu cakuɗuwa da kiyayewarKa ababen lulluɓewa da ni'imominKa, masu shagaltuwa da ambatanKa, masu neman taimako da sunanKa, masu tarowa da dacewarKa, masu motsawa da dabararKa da kuma ƙarfinKa, (da (kiyayewar) Ka ne muka shiga maraice, da (kiyayewar) Ka ne muka rayu, da (kiayewar) Ka ne zamu mutu) wato kamar lafazin da ya gabata tare da sanya shi a sama, sai ya ce: Ya Allah da Kai ne muka shiga maraice, kuma da sunanKa ne Mai rayawa muke rayuwa, da sunaKa ne Mai kashewa zamu mutu, (kuma gareKa ne tashi yake) da tashi bayan mutuwa, da rarrabuwa bayan haduwa, halinmu zai ci gaba akan haka a cikin dukkan lokuta, da ragowar halaye ba zan rabu ba daga gare shi kuma ba zan kaurace masa ba. Idan ya shiga maraice bayan la'asar ya ce: "Ya Allah da (kiyayewar) Ka ne muka shiga maraice, kuma da (kiyayewar) Ka ne muka wayi gari, da (umarnin) Ka ne muke rayuwa, kuma (da al'amarin) Ka ne zamu mutu, makoma tana gare Ka) makoma a duniya, da makoma a ƙarshe, Kaine Kake rayani kuma kaine zaKa kasheni.