





























Hadeeth Cards
Da'wa cards that highlight great meanings from the noble prophetic hadiths in a simple style and attractive display that helps the Muslim to have a deeper understanding of his religion in an easy way
All
Daga Sauban - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Mafificin dinaren (kudi) da mutum zai ciyar da shi: Dinarin da ya ciyar da shi ga iyalansa, da dinaren da mutum yake ciyar da shi ga dabbarsa a tafarkin Allah, da dinaren da yake ciyar da shi ga abokansa a tafarkin Allah" Abu Kilaba ya ce: "Sai ya fara da iyali, sannan Abu Kilaba ya ce: Kuma wanne mutum ne mafi girman lada kamar mutumin da yake ciyar da iyali ƙanana don ya rufa musu asiri ko Allah Ya anfanar da su da shi, kuma ya wadata su".
Muslim ne ya rawaito shi(Annabi) tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi ya bayyana wasu Nau’uka a cikin ciyarwa, ya kuma jerantasu idan fuskokin ciyarwar sun gagara gwargwadan mafi wajabci akanka, sai ya fara da mafi muhimmanci sai mafi muhimmanci; sai ya sanar da cewa mafi yawan dukiya a lada ita ce wadda musulmi yake ciyar da ita ga wanda ciyarwarsa ta wajaba akan shi; kamar mata da ɗa, sannan ciyarwa ga abin hawa wanda aka tanada dan yaƙi a tafarkin Allah, sannan ciyarwa ga abokansa da ayarinsa a halin kasancewarsu mayaƙa a tafarkin Allah.
Daga Abu Sa'id Khudri - Allah Ya yarda da shi - cewa shi ya ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: "Idan ɗayanku ya ga wani abu a mafarkinsa da yake son sa to shi daga Allah ne, sai ya godewa Allah a kansa kuma ya bada labarin shi, idan kuma ya ga wanin hakan daga abinda yake ƙi, to kawai shi daga Shaiɗan ne, to sai ya nemi tsari daga sharrinsa, kuma kada ya fadawa kowa, to shi (mafarkin) ba zai cutar da shi ba".
Bukhari ne ya rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa kyakkyawan mafarki mai faranta rai a cikin mafarki to daga Allah ne, kuma ya nunar da cewa ya godewa Allah akansa, ya kuma bada labarinsa, idan kuma ya ga abinda yake ƙinsa yake baƙanta masa rai to shi kawai daga Shaiɗan ne; to ya nemi tsarin Allah daga sharrinsa, kada ya faɗawa kowa; (to mafarkin) ba zai cutar da shi ba , inda Allah Ya sanya abinda aka ambata sababi na kuɓuta daga abinda yake na mugun mafarkin .
Daga Suhaib - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce -: ’’Lamarin mumini da ban mamaki yake, dukkannin al’amuransa alheri ne, kuma hakan ba ya kasancewa ga kowa sai ga mumini ,idan abin farinciki ne ya same shi sai ya gode wa Allah sai, sai ya zamar masa alheri, idan kuma na sharri ne ya same shi sai ya yi haƙuri, shi ma sai ya zamar masa alheri’’.
Muslim ne ya rawaito shi(Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi yana mamaki daga sha'anin mumini da halayensa ta ɓangaren kyautatawa; hakan domin halayensa dukkansu alheri ne, kuma hakan ba ya kasancewa ga wani sai ga mumini; Idan farin ciki ya same shi sai ya godewa Allah; sai ya samu lada saboda godiyarsa. Idan kuma cuta ta same shi sai ya yi haƙuri ya nemi lada a wurin Allah, sai ya samu lada saboda haƙuri, shi a kowanne hali yana cikin lada.
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance idan zai yi atishawa, yana sanya hannunsa - ko tufafinsa - a bakinsa, kuma ya runtse - ko matse - muryarsa da shi.
Abu Daud ne ya ruwaito shi da Kuma Tirmizi da Ahmad(Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata aagre shi ya kasance idan zai yi atishawa: Da farko: Yana ɗora hannunsa, ko tufafinsa akan bakinsa; dan kada wani abu da zai cutar da abokin zamansa ya fita daga bakinsa ko hancinsa. Na biyu: Yana ƙanƙar da muryarsa ba ya ɗaga ta.
Daga Usama ɗan Zaid - Allah Ya yarda da shi - ya ce: An ce masa: Shin ba zaka shiga gurin Usman ba ka yi masa magana? sai ya ce: Shin kuna ganin cewa ni ba za yi masa magana ba har sai na fada muku? wallahi hakika na yi masa magana tsakanina da shi, ba tare da na buɗe kofar wani al'amarin da bana son in zama na farkon wanda zai buɗeshi ba, kuma ba zan cewa wani dan ya zama sarkina (shugabana) ba: Cewa shi ne mafi alherin mutane bayan na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: "Za’a zo da mutum ranar Alkiyama, sai a jefa shi a cikin wuta, sai hanjin cikinsa su fita, sai ya kewaya da su kamar yadda jaki yake kewaye da dutsen nika, sai 'yan wuta su taru gare shi, sai su ce: Ya wane me ya sameka? shin baka kasance kana umarni da aikin alheri ba, kuma kana hani daga abin ki? sai ya ce: Eh, hakika na kasance ina horo da aikin alheri amma bana aikata shi, kuma ina hani daga abin ki (mummuna) kuma ina aikata shi".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiAn cewa Usama ɗan Zaid Allah - Ya yarda da su - Shin baka shiga wurin Usman ɗan Affan - Allah Ya yarda da shi - ba ka yi masa magana cikin abinda yake faruwa na fitina tsakanin mutane da kokari a kasheta gabaɗayanta, sai ya sananar da su cewa shi ya yi masa magana a sirri dan neman maslaha badan tada fitina ba, manufarsa cewa shi ba ya son bayyanar da inkari ga sarakuna a cikin jama'a, sai ya zama sababi na rena khalifa, kuma shi ne kofar fitina da sharri ba zan zama farkon wanda zai buɗeta ba. Sannan Usama - Allah Ya yarda da su - ya ce: Shi yana yi wa sarakuna nasiha a boye kuma ba ya yi wa wani mujamala koda sarki ne, kuma ba ya yi musu fadanci sai ya yabe su a gabansu da karya, hakan bayan ya ji daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - cewa shi za’a zo da wani mutum ranar alkiyama, sai a jefa shi a cikin wuta, sai hanjin (kayan) cikinsa su fito daga cikinsa da gaggawa saboda tsananin zafi da tsananin azaba, sai ya kewaya da 'ya'yan cikinsa yana wannan halin kamar kewayawar jaki a gefan dutsen nikansa, sai 'yan wuta su taru a gefansa kamar sarkar data kewaye shi, sai su tambaye shi : Ya wane, shin ba kaine ka kasance kana umartarmu da aikin alheri ba kuma kake hanamu abin ki ba?! Sai ya ce: Lallai ni na kasance ina horo da aikin alheri amma bana aikata shi, kuma ina hani daga abin ki kuma ina aikata shi.
Daga Anas ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wanda ya reni 'yan mata biyu har suka balaga zai zo ranar alƙiyama ni da shi" sai ya dunƙule yatsunsa.
Muslim ne ya rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa wanda aka azirta shi da 'yan mata biyu ko 'yan uwa mata biyu sai ya tsaya da ɗawainiya da tarbiyya da nusarwa ga alheri da gargaɗarwa daga sharri da makamancin hakan har suka girma suka balaga; zai zo ranar alƙiyama shi da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - kamar waɗannan biyun, kuma sai ya haɗa yatsunsa biyu manuniya da na tsakiya.
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Ba za ku shiga aljanna ba har sai kun yi imani, Ba za ku yi imani ba har sai kun so junanku, , shin ba na shiryar daku akan abinda idan kun aikata shi za ku so junanku ba? ku yada sallama a tsakaninku".
Muslim ne ya rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agar shi - ya bayyana cewa ba masu shiga aljanna sai muminai, kuma imani ba ya cika, sannan halin jama'ar musulmai ba ya gyaruwa har sai sashinsu yaso sa shi. Sannan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agar shi - ya shiryar zuwa mafificin al'amuran da su ne soyayya take gamewa, ita ce yada sallama tsakanin musulmai, wacce Allah Ya sanyata gaisuwa ga bayinSa.
Daga Abu Huraira - Allah ya yarda da shi - ya ce: Mun kasance tare da Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yayin da ya ji wata kara, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Shin kun san mene ne wannan?" ya ce: Muka ce: Allah da ManzonSa ne mafi sani, ya ce: "Wannan wani dutsene da aka jefa shi cikin wuta tun shekara saba'in, shi (dutsan) yana faɗawa cikin wuta a yanzu, har sai da ya kai karshanta".
Muslim ne ya rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ji wani sauti (kara) mai tsoratarwa kamar faɗuwar wani jiki daga jikkuna, sai ya tambayi waɗanda ke tare da shi cikin sahabbai - Allah Ya yarda da su - game da wannan karar, sai suka ce: Allah da Manzonsa ne mafi sani. Sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Lallai wanann karar da kuka ji ta ta wani dutse ce da aka yi jifa da shi daga gefen Jahannama tun shekara saba'in, shi yana sauka yana faɗawa a cikinta, har sai ya kai karshenta a yanzu lokacin da kuka ji sautin.
Daga Salamah Dan Akwa'a - Allah Ya yarda da shi -: Cewa wani mutum ya ci a wurin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - da hannun hagunsa, sai Ma’aikin Allah ce da shi: "Ka ci da hannun damanka ." Ya ce: Ba zan iya ba. Ya ce: "Ba za ko ka iya ba", ba abin da ya hana shi sai girman kai, ya ce: Bai kara daga shi zuwa bakinsa ba.
Muslim ne ya rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ga wani mutum yana ci da hannunsa na hagu, sai ya umarce shi da ya ci da hannunsa na dama, sai mutumin ya amsa masa dan girman kai da karya da cewa shi ba zai iya ba! sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi mummunan addu'a akansa da haramta masa ci da dama, sai Allah Ya amsa addu'arsa da shanyewar hannunsa na dama, bai kara daga shi zuwa bakinsa ba bayan hakan da abinci ko abin sha.