





























Hadeeth Cards
Da'wa cards that highlight great meanings from the noble prophetic hadiths in a simple style and attractive display that helps the Muslim to have a deeper understanding of his religion in an easy way
All
Daga Dan Abbass cikin fadin Allah inda yake cewa: kuma suka ce kada ku kuskura ku bar Allolinku kuma kada ku bar Waddan da Suwa'an da kuma Yagusa da ya'uka da kuma Nasra, sai ya ce wadan nan sunayen na wasu Mutanen kikrki ne daga cikin Mutanen Annabi Nuh, yayai da suka Mutu sai shaidan yayi musu wahayi ga Mutanensu kan su kafa a wurarensu da suke zama gumaka, kuma su sa musu sunansu sai kuwa suka yi, kuma ba'a bauta musu ba sai bayan wadan nan sun Mutu kuma an manta da Ilimin sai aka rika bauta musu"
Buhari ne ya rawaito shiDan Abbas yana Fassara wannan Aya mai girma cewa wadan nanGumakan wadanda aka ambata a Alkurani cewa Mutanen Annabi Nuhu ne sunyi ta yiwa junansu wasiyya da ayi ta bauta musu bayan Annabinsu ya hanasu ga barin yin Shirka da Allah, kuma cewa ita a Asali sunaye ne na Mutanen kirki daga cikinsu, wanda suka wuce gona da Iri da yadda Shaidan ya kawata Musu har suka kafa gumakansu, sai kuma al'amarin wadan Hotunan ya koma Gumaka da ake bauta musu koma bayan Allah.
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Wanda ya saurarawa wanda yake cikin mawuyacin hali, ko ya sarayar masa (da bashinsa), Allah Zai inuwantar da shi a ranar Alƙiyama ƙarƙashin inuwarssa ranar da babu wata inuwa sai inuwarsa".
Tirmizi da Ahmad sun rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah - su tabbata agare shi - ya ba da labari cewa wanda ya saurarawa wanda ake bi bashi, ko ya sarayar masa daga bashinsa, to, sakamakonsa: shi ne Allah Zai inuwantar da shi ƙarƙashin al-Arshinsa a ranar Alƙiyama, wanda rana zata kusanto kawunan bayi a cikinta, kuma zafinta zai tsananta akansu. Babu wanda zai samu wata inuwa sai wanda Allah Ya inuwantar da shi.
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Wanda Allah Yake nufinsa da alheri zai shafeshi da rashin lafiya (zai jarrabeshi)".
Bukhari ne ya rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana ba da labarin cewa idan Allah Ya yi nufin wani alheri ga bayinsa muminai sai ya jarrabesu a kawunansu da dukiyoyinsu, don abin da zai faru ga mumini na komawa zuwa ga Allah - Maɗaukakin sarki - da addu'a, da kankare munanan ayyuka, da ɗaukaka darajoji.
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Ku barni a abinda na bar muku, kaɗai waɗanda ke gabaninku sun halaka ne da tambayarsu da kuma saɓawarsu ga annabawansu, idan na haneku daga wani abu to ku nuisance shi, idan na umarceku da wani abu to ku zo da shi daidai ikonku".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ambaci cewa hukunce-hukuncen shari'a sun rabu gida uku: Abinda aka yi shiru akan sa, da abubuwan da aka hana, da abubuwan da aka yi umarni. Amma na farko: Shi ne wanda shari'a ta yi shiru akansa, ta yadda babu wani hukunci, sai kuma cewa asali a abubuwa rashin wajabci; amma a zamaninsa - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - to barin tambaya ga wani abu da bai afku ba yana wajaba dan tsoron kada a wajabta ko haramci ya sauka a kan shi, domin Allah Ya bar su ne dan rahama ga bayi. Amma bayan rasuwarsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - idan tambayar ta kasance ta fuskar neman fatawa ce ko koyarwa ga abinda ake buƙatuwa a gare shi na al'amarin addini to ya halatta, kai an yi umarni da shi ma, idan kuma ta fuskar ta'annututi ce da ɗorawa kai to shi ne abinda ake nufi da barin tambaya daga gare shi a cikin wannan Hadisin; hakan domin cewa shi zai iya kaiwa zuwa kwatankwacin abinda ya afku ga Banu Isra'ila, dan an umarce su su yanka saniya da sun yanka kowacce irin saniya da sun aikata umarni, sai dai su sun tsananta sai aka tsananta musu. Na biyu: Abubuwan da aka hana; su ne: Abinda ake bawa wanda ya bar shi lada, kuma ana yi wa wanda ya aikata shi uƙuba, to nisantarsu yana wajaba. Na uku: Abubuwan da aka umarta; shi ne abinda ake bawa wanda ya aikata shi lada, kuma ana yi wa wanda ya bar shi uƙuba, to yana wajaba ya aikata shi gwargwadan iko.
Daga Ibnu Abbas - Allah Ya yarda da su - Daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - a cikin abin da yake ruwaitowa daga Ubangijinsa - Mai girma da ɗaukaka - ya ce: Ya ce: "Lallai Allah Ya rubuta kyawawa (lada) da munana (alhaki), sannan Ya bayyana hakan, wanda ya yi nufin kyakkyawa bai aikatata ba, to, Allah zai rubuta masa kykkyawa cikakkiya, idan ya yi nufinsa sai ya aikatata, to, Allah Zai rubuta masa kyawawa goma a wurinsa zuwa ninki ɗari bakwai, zuwa ninki da yawa, wanda ya yi nufin mummuna bai aikatashi ba, to, Allah Zai rubuta kykkyawa cikakke, idan ya yi nufinsa sai ya aikatashi Allah Zai rubuta masa mummuna ɗaya".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiManzo - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bayyana cewa Allah Ya ƙaddara kyawawa da munana, sannan Ya bayyanawa Mala'iku biyu yaya zasu rubuta su: Wanda ya yi nufin ya aikata kykkyawa za'a rubuta masa kyakkyawa ɗaya ko da bai aikatashi ba, idan ya aikatashi, to, za a ninkashi da tamkarsa goma zuwa ninki ɗari bakwai, zuwa ninki da yawa, ƙarin yana kasancewa ne da gwargwadan abin da ke cikin zuciya na ikhlasi da ƙetarewar amfani da makamancin hakan. Wanda ya yi nufin aikata mummuna sannan ya barshi saboda Allah, za a rubuta masa kykkyawa, idan ya barshi don shagaltuwa da barinsa, tare da rashin aikata sabubbanta ba za a rubuta masa komai ba, idan ya barshi don gajiyawa daga gareshi za a rubuta masa niyyarsa, idan ya aikatata za a rubuta masa mummuna ɗaya.
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Allah ba Ya duba zuwa surorinku da dukiyoyinku, sai dai Yana duba zuwa zukatanku da ayyukanku".
Muslim ne ya rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bayyana cewa Allah - Tsarki ya tabbatar masa Ya ɗaukaka - ba Ya duba zuwa surorin bayi da jikkunasu, shin su kyawawa ne ko munana ne? shin su manya ne ko kananu ne? lafiyayyu ne ko marasa lafiya ne? Kuma ba Ya duba zuwa dukiyoyinsu, shin masu yawa ne ko kaɗan ne? Allah - Mai girma da daukaka - ba Ya kama bayinsa kuma ba Ya yi musu hisabi a kan waɗannan al'amuran da fifikon da ya ke cikinsu, sai dai Yana duba zuwa zukatansu da abin da ke cikinsu na tsoron Allah da sakankancewa, da gaskiya da ikhlasi, ko nufin riya da jiyarwa, yana duba zuwa ayyukansu ta bangaren gyaransu da ɓacinsu; sai Ya bayar da lada, kuma Ya yi sakayya a kansu.
Daga Umar ɗan khaɗɗab - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Wata rana muna zaune a wurin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yayin da wani mutum ya ɓullo mana mai tsananin farin tufafi, mai tsananin baƙin gashi, ba’a ganin sawunsa, kuma wani daga cikinmu bai sanshi ba, har ya zauna zuwa ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, sai ya jingina gwiwoyinsa zuwa gwiwoyinsa, ya ɗora tafukansa a kan cinyoyinsa, sai ya ce: Ya Muhammad, ba ni labari game da musulunci, sai manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: "Muslulunci: shi ne ka shaida babu wani abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma cewa (Annabi) Muhammad manzon Allah ne, ka tsai da sallah, ka ba da zakka, ka azimci Ramadan, ka ziyarci ɗakin (Allah) idan kana da ikon tafiya zuwa gareshi" ya ce: ka yi gaskiya, ya ce: Sai muka yi mamakinsa, yana tambayarsa yana gasgatashi, ya ce: Ka ba ni labari game da imani, sai ya ce: "Ka ba da gaskiya da Allah, da mala'ikunsa, da littattafansa, da manzanninsa, da ranar lahira, ka ba da gaskiya da kaddara alherinta da sharrinta". Sai ya ce: ka yi gaskiya, ya ce: Ka ba ni labari game da kyautayi, ya ce: "Ka bautawa Allah kamar kai kana ganinsa, idan ka kasance ba ka ganinsa, to, shi yana ganinka" Ya ce: ka ba ni labari game da al-ƙiyama, ya ce: Wanda ake tambayar bai fi wanda yake tambayar sani ba". Ya ce: Ka ba ni labarin alamominta, ya ce: "Kuyanga za ta haifi uwargijiyarta, kuma za ka ga marasa takalma talakawa masu kiwon dabbobi suna gasar tsawaita gidaje", Ya ce: Sannan ya tafi, sai na zauna ɗan wani lokaci sannan ya ce da ni: "Ya Umar, shin ka san waye mai tambayar?" Na ce: Allah da Manzonsa ne mafi sani, ya ce: "To, lallai Jibrilu ne ya zo muku don ya sanar da ku addininku".
Muslim ne ya rawaito shiUmar ɗan Khaɗɗab - Allah Ya yarda da shi - yana ba da labari cewa Jibril - aminci ya tabbata a gare shi - ya fito wurin sahabbai - Allah Ya yarda da su - a surar wani mutum namiji ba a sanshi ba, daga siffofinsa, cewa tufafinsa masu tsananin fari ne, gashin kansa kuma mai tsananin baƙi ne, ba a ganin gurbin tafiya a gareshi na bayyanar gajiya, da ƙura, da rarrabewar gashi, da dattin tufafi, kuma wani ɗaya daga mahalartan bai sanshi ba, alhali su suna zaune a wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, sai ya zauna a gaban Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - irin zaman mai neman sani, sai ya tambayeshi game da musulunci, sai ya ba shi amsa da waɗannan rukunan, waɗanda suka ƙunshi iƙirari da shaida biyu, da kiyayewa a kan salloli biyar, da ba da zakka ga waɗanda suka cancanta, da azimin watan Ramadan, da ba da farillar Hajji a kan mai iko. Sai mai tambayar ya ce: Ka yi gaskiya, sai sahabbai suka yi mamaki daga tambayarsa mai nuni a kan rashin saninsa a cikin abin da yake bayyana da kuma gasgatashi. Sannan ya tambaye shi gami da imani, sai ya amsa masa da waɗannan rukunan guda shida masu ƙunshe da imani da samuwar Allah - Maɗaukakin sarki - da siffofinsa, da kaɗaitashi da ayyukansa kamar halitta, da kaɗaita shi da ibada, kuma cewa mala'iku waɗanda Allah Ya haliccesu daga haske bayi ne ababen girmamawa ba sa saɓawa Allah - Maɗaukakin sarki - kuma suna aiki da umarninsa, da yin imani da littattafan da aka saukar ga manzanni daga Allah - maɗaukakin sarki -, kamar Alƙur'ani da At-Taura da Linjila da wasunsu, da kuma (imani) da manzanni masu isar da Addinin Allah, daga cikinsu akwai (annabi) Nuhu, da Ibrahim, da Musa, da Isa, da na ƙarshensu (annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata a gare su -, da wasunsu daga cikin Annabawa da manzanni, da imani da ranar lahira, abin da ke bayan mutuwa yana shiga cikinsu na kabari da rayuwar barzahu, kuma cewa mutum za a tasheshi bayan mutuwa kuma za a yi masa hisabi, kuma makomarsa za ta zama ko dai zuwa aljanna ko zuwa wuta, da imani da cewa Allah Ya ƙaddara abubuwa gwargwadon yadda iliminsa ya rigaya da shi, kuma hikimarsa ta hukuntashi da rubutunsa ga hakan, da mashi'arsa gareshi, da afkuwarsu gwargwadon yadda ya ƙaddarasu, ya kuma haliccesu don haka. Sannan ya tambaye shi game da kyautatawa, sai ya ba shi labari da cewa kyautatawa ita ce ya bautawa Allah kamar shi yana ganinsa, idan bai samu damar kaiwa zuwa wannan matsayin ba, to, ya bautawa Allah - Maɗaukakin sarki - kamar Allah Yana ganinisa, na farko shi ne matsayin Mushahada, ita ce mafi ɗaukaka, na biyu shi ne matsayin Muraƙabah. Sannan ya tambaye shi yaushe ne alƙiyama? sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya bayyana cewa sanin al-ƙiyama yana daga abin da Allah Ya keɓanta da saninsa, babu wani daga halitta da ya sanshi, wanda ake tambayar da mai tambayar. Sannan ya tambaye shi gami da alamomin alƙiyama? Sai ya bayyana masa cewa daga cikin alamominta akwai yawan kuyangi (sa-ɗaka) da 'ya'yansu, ko yawan saɓawar 'ya'ya ga iyayensu, mata za su dinga yi musu mu'amala irirn mu'amalar bayi, kuma cewa makiyaya dabbobi da talakawa za a shinfiɗa musu duniya a ƙarshen zamani, sai su dinga alfahari a ƙawata gine-gine da ɗaukakasu. Sannan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ba da labari da cewa mai tambayar shi ne Jibrilu ya zo don sanar da sahabbai wannan addinin miƙaƙƙe.
Daga Nana Aisha - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wanda ya farar da (wani abu) daga cikin al'amarinmu wannan abinda ba ya ciknsa to an mayar masa". Daga Muslim: "Wanda ya aikata wani aiki wanda ba ya kan al'amarinmu to shi abin an mayar masa".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bayyana cewa wanda ya yi kirkira a Addini ko ya aikata wani aikin da wani dalili bai yi nuni akansa ba na Alkur’ani ko hadisi, to shi abin juyarwane akan mai shi ba abin karba ba ne a wurin Allah.
Daga Abu Zarr - Allah Ya yarda da shi - Daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - a abin da yake ruwatowa daga Allah - tsarki ya tabbatar masa Ya ɗaukaka - cewa Yace: "Ya bayina lallai ni Na haramta zalunci a kan kaina, kuma na sanyashi abin haramtawa, to, kada ku yi zalunci. Ya ku bayina dukkaninku ɓatattu ne sai wanda Na shiryar da shi, ku nemi shiriyata in shiryar da ku. Ya ku bayina, dukkaninku mayunwata ne sai wanda Na ciyar, ku nemi ciyarwata in ciyar da ku. Ya ku bayina dukkaninku matsiraita ne sai wanda na tufatar da shi, ku nemi tufatarwata zan tufatar da ku. Ya ku bayina lallai kuma yin laifi dare da rana, Ni kuma ina gafarta zunubai duka, ku nemi gafarata; Zan gafarta muku. Ya ku bayania haƙiƙa ba za ku iya cutar da ni ba, ballantana ku cuceni, ba za ku iya amfanata ba, ballantana ku anfanar da Ni. Ya ku bayina da a ce na farkonku da na ƙarshenku da muatnenku da aljanunku za su kasance a kan mafi taƙawar zuciyar mutum ɗaya daga cikinku hakan ba zai ƙara komai daga mulkina ba. Ya ku bayina da a ce na farkonku da na ƙarshenku da mutanenku da aljanunku za su kasance a kan zuciyar mafi fajircin mutum ɗaya daga cikinku hakan ba zai rage wani abu daga mulkina ba. Ya ku bayina da a ce na farkonku da na ƙarshenku da mutanenku da aljanunku za su tsaya a bigire ɗaya su tambayeni, sai in ba kowa tambayarsa hakan ba zai rage komai daga abin da ke wurina ba, sai dai abin da allura take tauyewa idan an shigar da ita kogi. Ya ku bayina kaɗai ayyukankun ne ina kiyayesu gareku, sannan in cika muku su, to, wanda ya sami alheri, to, ya godewa Allah wanda ya samu wanin haka, to, kada ya zargi kowa sai kansa".
Muslim ne ya rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bayyana cewa Allah - tsarki ya tabbatar masa Ya daukaka - Ya faɗi cewa: Ya haramta zalunci a kan kansa, kuma Ya sanya zalunci abin haramtawa a tsakanin bayinsa, kada wani ya zalunci wani. Kuma cewa halitta gaba ɗayansu ɓatattu ne daga hanyar gaskiya sai da shiriyar Allah da dacewarsa, wanda ya roketa zai datar dashi kuma ya shirye shi, kuma cewa halitta mabuƙata ne zuwa ga Allah masu buƙata ne gareshi a dukkanin buƙatunsu, wanda ya roƙi Allah zai biya buƙatarsa Ya kuma isar masa, kuma cewa suna yin zunubai dare da rana, kuma Allah - Maɗaukakin sarki - Yana suturtawa yana yafewa a yayin roƙon bawa gafara, kuma su ba za su iya cutar da Allah ba, ko su amfanar da Shi da komai ba, kuma da ace sun kasance a kan mafi taƙawar zuciyar mutum ɗaya, to, takawarsu ba za ta ƙara komai a mulkin Allah ba, da sun kasance a kan mafi fajircin zuciyar mutum ɗaya, to, fajircinsu ba zai tauye komai daga mulkinsa ba; domin cewa su raunana ne mabuƙata a gurin Allah, masu buƙatuwa zuwa gareshi a kowane hali da zamani da wuri, Shi ne Mawadaci - tsarki ya tabbatar masa -. kuma cewa da ace sun tsaya a bigire ɗaya mutanensu da aljanunsu, na farkonsu da na ƙarshensu suna roƙon Allah sai Ya ba wa kowane ɗaya daga cikinsu abin da ya roƙa, hakan ba zai tauye komai daga abinda ke wurin Allah ba, kamar allura ce da ake shigar da ita kogi sannan a fitar da ita, to, kogin ba zai ragu da komai ba, wannan don cikar wadatarsa tsarki ya tabbatar masa. Kuma Allah - tsarki ya tabbatar masa Yana kiyaye ayyuakan bayi, Yana tsaresu musu su, sannan Ya cika musu su a ranar alƙiyama, wanda ya samu sakamakon aikinsa alheri, to, ya godewa Allah a bisa dacewa da ya yi ga biyayya gareshi, wanda ya samu sakamakon aikinsa wani abu saɓanin hakan, to, kada ya zargi kowa sai zuciyarsa mai yawan umarni da mummuna wacce ta ja shi zuwa taɓewa.