





























Hadeeth Cards
Da'wa cards that highlight great meanings from the noble prophetic hadiths in a simple style and attractive display that helps the Muslim to have a deeper understanding of his religion in an easy way
All
Daga Abu Zarr - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ce: Ya Manzon Allah menene kofunan tafki? (Sai) ya ce: "Na rantse da wanda ran Muhammad yake a hannunSa, kofunansa sun fi yawan adadin taurarin sama ku saurara a cikin duhun daren da babu hazo, kofunan Aljanna wanda ya sha daga garesu ba zai yi kishirwa ba har karshen al’amarinsa (na kishirwa), indararo biyu ne suke zuba a cikinsa daga Aljanna, wanda ya sha daga gareshi Ba zai yi kishirwa ba, fadinsa tamkar tsawonsa ne, tsakanin Amman zuwa Ailata, ruwansa ya fi nono tsananin fari, kuma ya fi zuma zaki".
Muslim ne ya rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi rantsuwa akan cewa kofunan tafkinsa a ranar Alkiyama sun fi yawan adadin taurarin sama, Wannan yana bayyana a cikin dare mai duhun da babu wata a cikinsa; domin kuwa dare mai wata taurari ba sa kasancewa a bayyane a cikinsa dan boyuwarsu da hasken wata, kuma wacce babu hazo a cikinta; domin samun hazo yana hana ganin taurari, Kuma cewa kofunan Aljanna, wanda ya sha daga abin shan dake cikin su ba zai yi kishirwa ba har abada, kuma wannan yana kasancewa karshen abinda yake samun mai shan na kishirwa. Kuma cewa tafkinsa indararo biyu daga Aljanna suna zuba a cikinsa, kuma fadinsa tamkar tsawonsa ne; Tafkin madaidaicin rukunai ne, tsawonsa yana kasancewa gwargwadan tazarar dake tsakanin Amman -ita wani gari ne a Balka'a daga Sham-, zuwa Ailata, wani birni ne sananne a gefen Sham. Ruwan tafkin ya fi nono fari, kuma dandanonsa ya fi zuma zaki.
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wutarku wani yankine daga yanki saba'in daga wutar Jahannama", (Sai) aka ce: Ya Manzon Allah, ta kasance ta isa (dan azabtarwa), ya ce: "An fifita ta a kansu da yanki sittin da tara, kowannen su tamkar zafinta yake”.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa wutar duniya wani yanki ne daga yanki saba'in daga wutar Jahannama, Wutar lahira karfin zafinta yana karuwa akan zafin wutar duniya da yanki sittin da tara, kowanne yanki daga gareta yana daidai da zafin wutar duniya. Sai aka ce : Ya Manzon Allah lallai cewa wutar duniya ta isa dan azabtar da masu shigarta. Sai ya ce: An fifita wutar Jahannama akan wutar duniya da yanki sittin da tara, kuma dukkaninsu tamkarta ne a cikin tsananin zafi.
Daga Abdullahi Dan Mas'ud - Allah Ya yarda da shi -: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya zantar damu alhali shi mai gaskiya ne abin gasgatawa: "Lallai cewa halittar dayanku ana tarota a cikin mahaifiyarsa yini arba'in da dare arba'in. Sannan ya zama gudan jini tamkarsa, sannan ya zama gudan tsoka tamkarsa, sannan a aiko masa da Mala'ika, a yi masa izini da kalmomi hudu, sai ya rubuta arzikinsa da ajalinsa da aikinsa, dan wuta ne ko dan Aljanna ne, sannan ya busa rai a cikinsa. Lallai dayanku zai yi aiki da aikin 'yan Aljanna har ya zama tsakaninsa da ita bai zamo ba sai zira'i, sai littafi ya rigaya agare shi sai ya yi aiki da aikin 'yan wuta sai yashiga wutar. Kuma cewa dayanku zai yi aiki da aikin 'yan wuta har ya kasance tsakaninsa da ita bai zamo ba sai zira'i, sai littafi ya rigaya akansa, sai ya aikata aikin 'yan aljanna sai ya shigeta".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDan Mas'ud ya ce:: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya zantar damu alhali shi mai gaskiyane a zancensa, kuma abin gasgatawa yayin da Allah - Madaukakin sarki - Ya gasgata shi. Ya ce: Lallai cewa dayanku ana taro halittarsa, cewa mutum idan ya zo wa iyalansa to tarwatsettsen maniyyinsa ana taroshi a cikin mace kwana arba'in yana maniyyi. Sannan ya zama gudan jini ita ce gudan jini mai kauri sandararre, wannan a arba'in ta biyu ne, Sannan ya zama gudan tsoka ita ce yanki na nama gwargwadan abinda ake taunawa, wannan a arba'in ta uku ce, Sannan sai Allah Ya aiko masa da Mala'ika, sai ya busa rai a cikinsa bayan karewar arba'in ta uku, Sai a umarci Mala'ikan da ya rubuta kalmomi hudu su ne: Arzikinsa, shi ne gwargwadan abin da zai samu daga ni'imomi a rayuwarsa, Da ajalinsa, shi ne gwargwadan wanzuwarsa a duniya, Da aikinsa, menene shi? dan wutan ne ko dan Aljanna ne. Sannan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi rantsuwa cewa; mutum zai yi aiki da aikin 'yan Aljanna kuma aikinsa zai zama na gari, wato a abinda yake bayyana ga mutane, kuma ba zai gushe a haka ba har ya kasance tsakaninsa da ita bai zama ba sai zira'i daya, wato: Babu abinda zai wanzu tsakaninsa da tsakanin saduwa da ita aljannar sai kamar wanda zai zama tsakaninsa da tsakanin wani wuri na kasa zira'i daya ne, sai littafi ya rinjaya akansa da abinda aka kaddara akansa to a wannan lokacin zai yi aiki da aikin 'yan wuta sai a cika masa da shi sai ya shiga wutar; Domin cewa sharadin karbar aikinsa shi ne ya tabbata akansa ta yadda ba zai canjaba, wani dayan kuma daga mutane zai yi ayyukan 'yan wuta har sai ya kusanci shigarta, kuma gwargwadan zira'i ne na kasa zai kasance tsakakninsa da wutar, sai littafi ya rinjaya akansa da abinda aka kaddara akansa, sai ya yi aikin 'yan Aljanna kuma ya shiga Aljannar.
Daga Dawus cewa shi ya ce: Na riski wasu mutane daga sahabban Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - suna cewa kowane abu (yana kasancewa) da kaddara ne, ya ce: Na ji Abdullahi Ibnu Umar - Allah Ya yarda da su, yana cewa: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: "Kowanne abu da kaddara ne, har gajiya da dabara, ko kuma wayo da gajiya ".
Muslim ne ya rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa kowanne abu da kaddara ne; Har kasawa: ita ce: Barin abinda yake wajibi ne aikata shi, da cewa zai yi ta jinkirta shi daga lokacinsa, da al'amuran duniya da lahira. Har dabara ita ce: Nishadi da kwarewa da al'amuran duniya da lahira. Kuma cewa Allah - Mai girma da daukaka - hakika Ya kaddara gajiyawa da wayo da kowane abu, ba zai afku a kasantacce ba sai hakika sanin Allah Ya rigaya da shi da mashi'arSa.
Daga Madar Dan Ukamis - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: "Idan Allah Ya kaddarawa bawa cewa zai mutu a wata kasa sai Ya sanya masa wata bukata zuwa gareta".
Tirmizi ne ya ruwaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa Allah idan Ya hukunta Ya kuma kaddarawa bawa cewa zai mutu a wata kasa alhali shi ba ya cikin kasar; sai a sanya masa wata bukata gareta sai ya tafi kasar, sai a karbi ransa a cikinta.
Daga Anas Ibnu Malik - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Muna zaune tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a cikin masallaci sai wani mutum ya shigo akan wani rakumi, sai ya dirkusar da shi a cikin masallaci sannan ya daure shi, sannan ya ce da su: Waye Muhammad a cikinku? alhali Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana kishingide a tsakaninsu, sai muka ce : Wannan farin mutumin wanda ke kishingide. Sai mutumin ya ce da shi: Ya kai Dan Abdul Mudallib sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce da shi: "Hakika na amsa maka". Sai mutumin ya cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: Ni mai tambayarka ne mai tsananta maka a tambaya, kada ka ji haushi na a ranka? sai ya ce: "Ka tambayi abinda ya bayyana gareka" sai ya ce: Ina tambayarka dan Ubangijinka da Ubangijin wadanda suka gabaceka, shin Allah ne Ya aikoka zuwa ga mutane gaba dayansu? sai ya ce: "Eh ya Allah". Ya ce: Ina maka magiya da Allah, shin Allah ne Ya umarceka da mu yi salloli biayr a yini da dare? ya ce: "Eh ya Allah ne.” ya ce Ina maka magiya da Allah shin Allah ne Ya umarceka da mu yi azumin wannan watan a shekara? ya ce: "Eh ya Allah". Ya ce; Ina maka magiya da Allah, shin Allah ne Ya umarceka da ka karbi wannan sadakar daga mawadatanmu sai ka rabata ga talakawan mu? sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Eh ya Allah". sai mutumin ya ce; na yi imani da abinda ka zo da shi, kuma ni manzo ne na wadanda ke bayana cikin mutane na, Ni ne Dimam dan Sa'alabata dan uwan Banu Sa'ad dan Bakar.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiAnas dan Malik - Allah Ya yarda da shi - yana bada labarin cewa: Lokacin da sahabbai suna zaune tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a cikin masallaci yayin da wani mutum ya shigo akan wani rakumi, sai ya durkusar da rakumin sannan ya daure shi. Sannan ya tambayesu: Waye Muhammd a cikinku? Alhali Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana kishingide tsakanin mutanen, sai muka ce : Wannan farin mutumin. Sai mutumin ya ce da shi: Yakai Dan Abdul Muddalib. Sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce da shi: Na ji ka yi tambaya in amsa maka. Sai mutumin ya cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: Ni mai tambayarka ne kuma mai tsananta maka a tambaya, kada ka ji wani abu game dani a ranka. Wato: Kada ka yi fushi da ni kuma kada kunci ya sameka. Sai ya ce: Ka tambayi abinda kake so. Sai ya ce: Ina ina hada ka da Ubangijinka kuma Ubangijin wadanda suka gabace ka, shin Allah ne Ya aikoka zuwa ga mutane? Sai ya ce: Eh ya Allah, dan karfafa gaskiyarsa. Sai Mutumin ya ce: Ina yi maka magiya da Allah, wato; Ina tambayarka sabo da Allah, shin Allah ne Ya umarceka da ka yi salloli biyar a yini da dare? Su ne salloli wadanda aka faralanta ?., Ya ce: Eh ya Allah, Ya ce: Ina maka magiya da Allah, shin Allah ne Ya umarceka da mu azimci wannan watan daga shekara? wato: Watan Ramadan, Ya ce: Eh ya Allah, Ya ce: Ina maka magiya da Allah, shin Allah ne Ya umarceka daka karbi wannan sadakar daga mawadatanmu sai ka rabata ga talakawanmu? ita ce zakka. Sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: Eh ya Allah, Sai Dimam ya musulunta, kuma ya ba Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - labarin cewa shi zai kira mutanensa zuwa Musulunci. Sannan ya yi bayanin kansa cewa shi ne Dimam dan Sa'alabata daga Banu Sa'ad Ibnu Bakar.
Daga Ziyad Dan Labid - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ambaci wani abu, sai ya ce: "Wannan a lokacin tafiyar ilimi kenan" Na ce: Ya Manzon Allah, ta yaya ilimi zai tafi, alhali mu muna karanta Alkur’ani kuma, muna karantar da 'ya'yanmu shi, kuma 'ya'yanmu suna karantar da 'ya'yansu har zuwa ranar Alkiyama ? Ya ce: "Mahaifiyarka ta yi wabinka Ziyad, na kasance ina ganinka daga mafi fahimtar mutane a Madina, shin wadannan Yahudawan da Nasaran ba sa karanta Attaura da Injila, ba sa aiki da wani abinda ke cikinsu?!".
Ibnu Majah ne ya ruwaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agar shi - ya kasance a zaune tsakanin sahabbansa, sai ya ce:: Wannan lokacin da za'a dauke a zare ilimi ne daga mutane. Sai Ziyad Dan Labid Al-Ansary - Allah Ya yarda da shi - ya yi mamaki kuma ya tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, Sai ya ce; Ta yaya za'a dauke ilimi a sarayar da shi daga garemu?! Alhali mun karanta Alkur’ani mun haddaceshi; na rantse da Allah sai mun karantashi, kuma mun karantar da matanmu da 'ya'yanmu shi, da 'ya'yan 'ya'yanmu, Sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce yana mai mamaki: Mahaifiyarka ta rasaka ya Ziyad! na kasance ina lissafaka daga malaman mutanen Madina! Sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya bayyana masa: Cewa rasa ilimi bai zamo da rasa Alkur’ani ba; saidai rasa ilimi (yana kasancewa ne) da rashin aiki da shi, Wannan Attaurar da Injilar dake wajen Yahudawa da Nasara; a tare da haka ba ta anfanesu ba, kuma ba su anfana da manufarsu ba; shi ne aiki da abinda suka sani.
Daga Dan Abbas - Allah Ya yarda da su - ya ce: An saukarwa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - alhali shi yana da shekara arba'in, ya zauna a Makka shekara goma sha uku, sannan aka umarce shi da yin hijira, sai ya yi hijira zuwa Madina, ya zauna a cikinta shekara goma, sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya rasu.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDan Abbas - Allah Ya yarda da su - yana bada labarin cewa: An saukar da wahayi ga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - kuma an aiko shi alhali shekarunsa arba'in, sai ya zauna a Makka shekara goma sha uku bayan wahayi, sannan aka umarce shi da hijira zuwa Madina, ya zauna a cikinta shekara goma, sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya rasu shekarunsa sittin da uku.
Daga Katada - Allah Ya yi masa rahama - ya ce: Anas Dan Malik - Allah Ya yarda da shi - ya zantar damu cewa wani mutum ya ce: Ya Annabin Allah ya za’a tashi kafiri akan fuskarsa? Ya ce: " Shin wanda ya tafiyar da shi akan kafafuwa biyu a duniya bai zama yana da iko akan ya tafiyar da shi akan fuskarsa ranar Alkiyama ba?"Katada ya ce: Eh na rantse da buwayar Ubangijinmu.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiAn tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: Ya za'a tashi kafiri akan fuskarsa a ranar Alkiyama ?! sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce; Shin yanzu wanda ya tafiyar da shi akan kafafuwa biyu a duniya bai zama mai iko akan ya tafiyar da shi akan fuskarsa a ranar Alkiyama ba?! Allah Mai ikone akan dukkan komai.