





























Hadeeth Cards
Da'wa cards that highlight great meanings from the noble prophetic hadiths in a simple style and attractive display that helps the Muslim to have a deeper understanding of his religion in an easy way
All
An rawaito daga Anas Bn Malik -Allah ya yarda da shi daga Manzon Allah: "Lallai kowace Alumma tana da Amintaccen ta, kuma lallai amintaccen wannan Al-umma shi ne Abu Ubaidah Bn Al-Jarrah"
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiA cikin kowace Al-umma daga cikin Al-ummai wani Mutum da ya shahara da Amana sama da kowa, kuma mafi Shaharar wannan Al-ummar da Amana shi Abu Ubaidah Amir Bn Al-jarrah -Allah ya yarda da shi- saboda shi koda yake amanar ta kasance sifa ce da kowa daga cikin sahabbai yayi tarayya da shi a cikinta -Amincin Allah ya tabbata a gare su- sai sigar Hadisin tana nuna cewa ya xaresu a cikinta
Daga Ali -Allah ya yarda da shi- ya ce: "Ban taba ganin wani mutum da ya Manzon Allah SAW ya fansheshi ba bayan Sa'ad naji shi yana cewa: Ka harba fansarka da Mahaifana"
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiAli -Allah ya yarda da shi- yana bada labari cewa shi bai tava ganin Manzon Allah SAW yana fansar wani Mutum ba bauan Sa'ad Bn Abi Waqqae -Allah ya yarda da shi- lokacin da Manzon Allah SAW yaji shi yana cewa da shi a lokacin Yaqin Uhud, ka jefi kafirai da Mashi ina fansarka da Mahaifana, ai ina gabatar da Mahaifana don su zamo fansa a gareka kai ka tsira, kuma ya tabbata a cikin Ingantaccen hadisi cewa Manzon Allah SAW ya fanshi Zubai -Allah ya yarda da shi- da Iyayensa a Yaqin Khandaq, Kuma ana iya haxa tsakaninsu da cewa Ali -Allah ya yarda da shi- bai san hakan ba, ko kuma nufinsa yana taqaicewa ne kawai a Yaqin Uhud
Daga Aisha -Allah ya yarda da ita- cewa manzon Allah SAW ya kasance yana cewa: "Lallai Al-amarinku yana cikin abunda yake damuna bayana, babu mai iya haquri da ku sai mai haquri" ya ce: sannan Aisha tace, to Allah ya shayar da Mahaifinka Salsabilan Al-janna, tana nufin Abdulraman Bn Auf, kuma haqiqa ya Kasance yaci gaba da kula da matan Annabi SAW da Kuxi ana cewa: an siyar da ita da Dubu Arabain
Al-Tirmithi Ya Rawaito shi - Ahmad ne ya rawaito shiAn rawaito daga Abu salama Bn Abdulrahman Bn Auf -Allah ya yarda da shi- cewa uwar Muminai Aisha -Allah ya yarda da ita- ta ce:Lallai Manzon Allah SAW ya nemi Auren Matansa yana mai cewa lallai ni yana baqantamun sha'aninku da rayuwarku yadda zata kasance bayan Mutuwa ta, saboda ban bar muku gado ba, kuma cewa babu mai iya haqurin ciyar da ku sai Masu haquri sannan Aisha ta ce da Abu salama Allah ya shayar da Mahaifinka Abdulrahman Bn Auf da ruwan Al-jannah wacce ake kira Salsabil kuma haqiqa yayi sadaka ha Matan Manzon Allah SAW da wata gona wacce aka sayar da iya kan kuxi da ya kai Dinare Dubu Arba'in
Daga Abdulrahman Bin Abi Umairah kuma ya kasance daga cikin sahabban Manzon Allah SAW daga Annabi SAW cewa shi ya ce da Mu'awiya: "Ya Ubangiji kasanya shi Shiyayye kuma maishiryarwa kuma ka shiryar da shi"
Al-Tirmithi Ya Rawaito shi - Ahmad ne ya rawaito shiManzon Allah SAW yayi Addu'a ga Mu'awiya Bn Abu Sufyan cewa Allah ya sanya shi Mai nuni zuwa Alkairi kuma ya sanya shi shiryayye akankin kansa, kuma Mutane su shiryu da shi
An rawaito daga Asma'a Bint Abubakar -Allah ya yarda da ita- ta ce: Manzon Allah SAW ya yi Wa'azin fitintinu waxanda Mutum zai gamu da su a cikin Qabarinsa, yayin da ya faxi haka sai Musulmai sai sukai kuwwa da ta hanani na fahimci abunda manzon Allah SAW yake nufi, yayin da kururuwar ta su ta ragu sai nace da wani Mutum da yake kusa da ni: Mai Manzon Allah yace Allah yayi maka Al-barka a qarshen maganarsa? sai ya ce: "Haqiqa anyi mun Wahayi cewa ku za'a Jarrabeku a cikin Qabarinku kusan Fitinar Dujal"
Buhari ne ya rawaito shi - Al-Nasa'i Ya Rawaito shiAsma'u tana bada labarin cewa Manzon Allah SAW ya yi Wa'azin fitintinu waxanda Mutum zai gamu da su a cikin Qabarinsa,da tsoronsa, kuma ya faxi Fitinar Qabari, kuma abunda ake nufi da ita shi ne tamabayar Mala'iku biyu Munkarun da Nakiri, zasu tambayi bawa game da Ubangijinsa da Annabinsa da Addininsa, kuma ya faxi wannan fitina ce Maigirma, kuma duk wanda ya dace a wannan to ya rabauta, kuma duk wanda ya kasa to ya halaka, yayin da ya faxi haka sai Musulmai sai sukai kuwwa da ta hanani na fahimci abunda manzon Allah SAW yake nufi, yayin da kururuwar ta su ta ragu sai nace da wani Mutum da yake kusa da ni: Mai Manzon Allah yace Allah yayi maka Al-barka a qarshen maganarsa? sai ya ce: Haqiqa anyi mun Wahayi cewa ku za'a Jarrabeku a cikin Qabarinku kusan Fitinar Dujal, Saboda Fitinar Duja Mai tsanani ce kuma mai wuya haka ma Azabar Qabari.
Daga Abdullahi Ibnu Amr Ibnul Aas - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Duk wanda ya gamu da Allah ba ya hada wani abu da shi to kuskurensa ba zai cutur da shi tare da shi ba, wanda kuwa ya mutu alhali yana yin shirka da shi wani kyakkyawan aikinsa ba zai amfane shi tare da shi da komai ba"
Ahmad ne ya rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa wanda ya mutu kuma ya gamu da Allah yana mai kaɗaita Allah ba ya hada wani da abu da shi to shi yana daga cikin 'yan aljanna, ko da an yi masa uƙuba da zunubinsa a cikin wuta. Wanda ya mutu alhali yana hada wani abu da shi to wani kyakkyawan aiki ba zai yi amfani tare da shirkarsa ba; kuma aljanna haramun ce gare shi .
Daga Abu Musa - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya tsaya a cikinmu da wasu kalmomi biyar, sai ya ce: «Lallai Allah - Mai girma da ɗaukaka - ba Ya bacci, kuma ba ya kamata gareShi Ya yi bacci, Yana ƙasa da ma'auni kuma Yana ɗaga shi, ana ɗaga aikin dare kafin aikin rana zuwa gare Shi, da aikin rana kafin aikin dare, shamakinSa shi ne haske, da ace zai yaye shi da hasken fuskarSa ya ƙona inda ganinsa ya tiƙe daga halittarSa».
Muslim ne ya rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya tsaya yana mai huɗuba a cikin sahabbansa da wasu jumloli biyar cikakku, su ne: Na farko: Allah - Mai girma da ɗaukaka - ba Ya bacci. Na biyu: Bacci ya koru a cikin haƙƙinSa; saboda cikar ƘayyumiyyarSa da kuma rayuwarSa. Na uku: Allah Yana ƙasa da ma'auni kuma Yana ɗaga shi da abin da ake auna ayyukan bayin da aka ɗaukakasu masu hawa zuwa gareShi, kuma ana aunawa daga arziƙansu masu sauka zuwa ƙasa, arziƙin da shine rabon kowanne abin halitta tsarki ya tabbatar maSa Yana ƙasƙantar da shi sai Ya ƙanƙanta shi, kuma Yana ɗaukaka shi sai Ya yalwata shi. Na huɗu: Ana ɗaga abin da bayi suka aikata da daddare kafin yinin da zai zo a bayansa, da kuma aikinsu da rana kafin daren dake bayansa; Mala'iku masu kiyaye ayyuka suna hawa sama da ayyukan dare bayan ƙarewarsa a farkon yini, kuma suna hawa da ayyukan rana bayan ƙarewarsa a cikin farkon dare. Na biyar: HijabinSa mai hana ganinSa shi ne cikakken haske ko wuta, da zai yaye shi da hasken fuskarSa ya ƙona inda ganinSa ya tiƙe a halittarSa; hasken fuskarSa shi ne haskenSa da kuma ɗaukakarSa da kwarjininSa. Abin ƙaddarawa: Da a ce Ya gusar Ya yaye abin da ke hana ganinSa shine hijabi, Ya yi tajalli ga halittarSa da hasken fuskarSa sun ƙona inda ganinSa ya tiƙe daga halittarSa; sune dukkanin halittu; domin cewa ganinSa - tsarki ya tabbatar maSa Ya ɗaukaka - mai kewaye sani ne da dukkanin kasantattu.
Daga Nana Aisha Uwar Muminai - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan zai umarce su da wasu ayyukan yana umartar su da abin da zasu iya, suka ce: Lallai mu bamu kasance kamar yanayinka ba ya Manzon Allah, lallai Allah Ya gafarta maka abin da ya gabata daga zunubinka da abin da ya jinkirta, sai ya yi fushi har sai da aka gane fushi a fuskarsa, sannan ya ce: «Lallai ni na fiku tsoron Allah kuma na fiku saninSa».
Bukhari ne ya rawaito shiUwar muminai Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - tana bada labarin cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan zai umarci mutane da wani aiki cikin ayyuka sai ya umarce su da abin da zai yi musu sauƙi banda wanda zai wahalar da su, dan jin tsoron kada su gajiya daga dawwama a kansa, sai ya yi aikin da shine kishiyar abin da yake umartarsu da shi daga sauƙaƙawa, sai dai cewa su sun nemi taklifin abin da zai wahalar da su daga gare shi, dan sun ƙudirce buƙatuwarsu zuwa kai matuƙa a cikin aikin dan ɗaukaka darajoji koma bayansa. Sai su ce: Lallai halinmu ba kamar halinka ba ne ya Manzon Allah, domin Allah haƙiƙa Ya gafarta maka abin da ya gabata daga zunubinka da abin da ya jinkirta, sai ya yi fushi har sai da aka gane fushi a fuskarsa, sannan ya ce: Lallai ni na fiku tsoron Allah kuma na fiku saninSa, dan haka ku aikata abin da nake umartarku da shi.
Daga ibnu Abbas - Allah Ya yarda da su - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Mune ƙarshen al'ummu, kuma waɗanda za'a fara yi wa hisabi, za’a ce: Ina al'ummar nan ba'uwa da kuma Annabinta? mune na ƙarshe kuma na farko».
Ibnu Majah ne ya ruwaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa al'ummarsa ita ce ƙarshen al'ummu a samuwa da kuma zamani, kuma ita ce farkon al'ummu da za’a yi wa hisabi a ranar alƙiyama, a ranar alƙiyama za'a ce: Ina al'ummar nan (ummiyya) ba'uwa da Annabinta? An dangantata ne zuwa ummiyarsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a cikin rashin iya karatu da kuma rubutu. Za'a kirasu dan yin hisabi a farko, dan haka mune na ƙarshe a zamani da kuma samuwa, kuma na farko a hisabi da kuma shiga aljanna a ranar alƙiyama.