





























Hadeeth Cards
Da'wa cards that highlight great meanings from the noble prophetic hadiths in a simple style and attractive display that helps the Muslim to have a deeper understanding of his religion in an easy way
All
Daga Jabir Dan Abdullahi - Allah Ya yarda da su - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Kada ku nemi ilimi dan ku yi wa malamai alfahari da shi, ko ku yi musu da wawaye da shi, kuma kada ku nufi bijiro da shi a zababbun majalisai, wanda ya aikata haka to wuta wuta".
Ibnu Majah ne ya ruwaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya gargadar da wanda ya nemi ilimi dan yi wa malamai alfahari, da bayyanar da cewa ni malami ne irinku, ko dan su yi magana da jayayya da wawaye masu karancin hankali, ko a nemi ilimi dan a bijiro a majalisai, a gabatar da shi akan waninsa a cikinsu. Wanda ya aikata haka; to cewa shi ya cancanci wuta da riyarsa da rashin tsarkake niyyarsa a cikin neman ilimi saboda Allah.
Daga Nawwas Dan Sam'an Al’Ansary - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Allah Ya buga wani misali hanya ce madaidaiciya, a gefunan hanyar biyu akwai ganuwowi biyu, a cikinsu akwai budaddun kofofi, akan kofofin akwai sakakkun labulaye, a kofar hanyar akwai wani mai kira yana cewa; Yaku mutane, ku shigo hanyar gaba daya, kada ku karkace, da wani mai kiran kuma yana kira a birbishin hanyar, idan ya yi nufin ya bude wani abu daga wadancan kofofin, zai ce: Kaicanka kada ka bude shi , domin cewa kai idan ka bude shi zaka shige shi. Tafarkin shi ne Musulunci, ganuwowin biyu kuma: Su ne iyakokin Allah, budaddun kofofin kuma: Su ne abubuwan da Allah Ya haramta, wannan mai kiran kuma akan tafarkin: Shi ne littafin Allah, mai kiran kuma a birbishin tafarkin: Mai wa'azin Allah ne (Ajiyoyin Allah) a cikin zuciyar kowane musulmi".
Tirmizi da Ahmad sun rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa; Allah Ya buga wani misali ga Musulunci da hanya madaidaiciya mikakkiya babu karkata a cikinta, agefan wannan hanyar akwai ganuwowi biyu, to bangwaye da suke kewaye da ita ta fuskarsa su ne iyakokin Allah, wasu budaddun kofofi suna shiga wadannan ganuwowi biyun su ne Abubuwan da Allah Ya haramta, akan wadannan kofofin akwai labulayen da basa bayyanar da wanda yake cikinsu ga mai wucewa akan hanyar, afarkon hanyar akwai wani mai kira yake fuskantar da mutane kuma yake shiryar da su yana ce musu: Ku tafi akansa ba tare da kun karkace zuwa wani bangaren ba, wannan mai kiran duk lokacin da mai tafiya akan tafarkin ya yi niyyar ya bude wani gwargwado mai sauki daga labulayen kofofin sai ya tsawatar masa ya ce da shi: Kaicanka kada ka bude shi! domin cewa kai idan ka bude shi zaka shigeshi kuma ba zaka sami damar kare kanka ba daga shiga, wannan mai kiran shi ne mai wa'azin Allah a cikin zuciyar kowane Musulmi.
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce : Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Shin dayanku yana son idan ya koma zuwa iyalansa ya samu manyan taguwowi masu ciki masu giba?" muka ce: Eh. Ya ce; "To ayoyi uku dayanku zai karantasu a cikin sallarsa sun fiye masa alheri daga taguwowi uku manya masu ciki".
Muslim ne ya rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bayyana cewa ladan karanta ayoyi uku a cikin sallah; shi ne mafi alheri daga mutum ya sami taguwowi uku masu ciki manya a cikin gidansa.
Daga Uqubah Dan Amir Al-Juhani - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Mai bayyanar da Alkur’ani kamar mai bayyanar da sadaka ne, mai boye Alkur’ani kamar mai boye sadaka ne".
Abu Dawud da Tirmizi da Nasa'i ne Suka Rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa mai bayyanar da karatun Alkur’ani kamar mai bayyanar da bayar da sadaka ne, mai boye karatun Alkur’ani kamar mai boye bayar da sadaka ne.
Daga Aliyu Allah ya yarda da shi ya ce: Ni na kasance mutum ne idan na ji wani hadisi daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - Allah Zai anfanar da ni daga abinda Ya so daga gare shi, Ya anfanar da ni da shi, idan wani mutum daga sahabbansa ya zantar da ni zan sa shi ya rantse, idan ya rantse mini sai in gasgata shi, cewa Abubakar Allah ya yarda da shi ya zantar da ni, kuma Abubakar ya yi gaskiya, ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: "Babu wani mutum da zai aikata laifi, sannan ya tashi ya yi alwala, sannan ya yi sallah, sannan ya nemi gafarar Allah, sai Allah Ya gafarta masa", sannan ya karanta wannan ayar: {Sune wadanda idan sun aikata wata alfasha ko sun zalinci kansu sai su tuna Allah sai su nemi gafarar zunubansu ga (Allah)}. [Aal-Imran: 135].
Abu Dawud da Tirmizi da Nasa'i cikin alkubra da Ibnu Majah haka kuma AhmadAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa babu wani bawa da zai yi zunubi, sai ya kyautata alwala, sannan ya tashi ya yi sallah raka'a biyu da niyyar tuba daga zunubinsa wannan, sannan ya nemi gafar Allah, sai Allah Ya gafarta masa. Sannan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya karanta fadinsa - Madaukakin sarki -: {Kuma waɗanda suke idan suka aikata wata alfãsha ko suka zãlunci kansu sai su tunã da Allah, sabõda su nẽmi gãfarar zunubansu ga Allah. Kuma wãne ne ke gãfara ga zunubai, fãce Allah? Kuma ba su dõge a kan abin da suka aikata ba, alhãli kuwa suna sane}. [Aal- Imran: 135].
Daga Abu Umama al-Bahili - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Wani mutum ya zo gurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ya ce: Shin kana ganin mutum ya yi yaƙi yana neman lada da yabo, me gare shi? sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Ba shi da komai". Sai ya maimaita masa sau uku, tsira da amincin Allah su tabbata agare shi yana ce masa: "Ba shi da komai" sannan ya ce: "Lallai Allah ba Ya karɓar aiki sai wanda ya zama abin tsarkakewa, kuma aka nufi fuskar Allah da shi".
Nasa'i ne Ya Rawaito shiWani mutum ya zo gurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: dan ya tambaye shi ya nemi fatawarsa game da hukuncin mutumin da yake fita yaƙi yana neman lada daga Allah da kuma kwaɗayin yabo da godiyar mutane, shin zai samu lada? sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya bashi amsa: Da cewa bashi da komai na lada; dan abinda ya yi wa Allah tarayya da shi a cikin niyyarsa, sai mutumin ya maimaita tambayarsa sau uku ga Annabi - tsira da amincin Allaah su tabbata agare shi -, kuma tsira da amincin Allah su tabbata agare shi yana amsa masa wannan amsar; da cewa bashi da lada, sannan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bashi labarin cewa ka'idar karbar aiki a wurin Allah: Lallai cewa Allah ba Ya karbar aiki sai in ya zama dukkansa saboda Allah ne batare da tarayya da wani a cikinsa ba, kuma ya zama dan zatin Allah ne - tsarki ya tabbatar maSa -.
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Yana daga kyan Musuluncin mutum yabar abin da babu ruwansa».
Tirmizi da Ahmad ne sun rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa daga cikar kyawun Musuluncin musulmi da kuma cikar imaninsa, ya nisanci abin da bai shafe shi ba, kuma bai keɓance shi ba, bai da alaƙa da shi da kuma abin da ba zai amfane shi ba na maganganu da ayyuka, ko kuma abin da baruwansa da shi na al'amuran Addini da duniya, shagaltuwa da abin da bai shafi mutum ba wataƙila zai shagaltar da shi daga abin da akwai ruwansa a ciki, ko ya kai shi zuwa ga bin da nisantarsa yake wajaba akansa; domin kuwa mutum abin tambaya ne game da ayyukansa a ranar lahira.
Daga Abdullahi ɗan Mas’ud - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Mumini ba mai yawan suka bane ko mai yawan tsinuwa ba ko mai yawan alfasha ba ko mai zancen banza ba".
Tirmizi ne ya ruwaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa bai zamo daga sha'anin mumimi mai cikakken imani ya zama mai yawan aibata mutane a cikin dangantakar su ba, kuma ba mai yawan zagi da tsinuwa bane, kuma ba mai yawan alfasha ne da aiki ko magana wacce babu kunya a cikinta ba.
Daga Abu Huraira Allah - Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Wanda ya ce: (Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Shi kaɗai Ya ke ba shi da abokin tarayya, mulki naSa ne, godiya taSa ce, kuma Shi Mai iko ne a kan dukkan komai) sau ɗari a cikin yini, yana da abinda ya yi daidai da wuyaye goma, kuma za'a rubuta masa kyakkyawa ɗari, kuma za'a shafe masa mummuna ɗari, kuma za ta kasance tsari daga Shaiɗan a wannan yinin nasa, har sai ya kai maraice, kuma ba wanda zai zo da abin da ya fi wanda ya zo da shi, saidai wanda ya aikata sama da hakan».
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa wanda ya ce: (Babu abin bautawa da gaskiya) babu wani abin bauta da cancanta (sai Allah, Shi kaɗai Yake) a cikin UluhiyyarSa da RububiyyarSa da sunayenSa da kuma siffofinSa, (mulki naSa ne) da tasarrufi da kuma jujjuya al'amura gaba ɗayansa, (godiya taSa ce) akan dukkan abinda Ya halicce shi kuma Ya ƙaddara shi, (Shi Mai iko ne akan dukkan komai) ba tare da wani mai hanawa ko mai karewa ba, abinda bai so ba zai kasance ba. Wanda ya faɗi wannan zikirin sau ɗari a yini kuma ya maimaita shi, za'a rubuta masa lada a wurin Allah kamar ya 'yanta wuyaye goma ne, kuma za'a rubuta masa kyakkyawa ɗari da daraja ɗari a cikin aljanna, kuma za'a shafe masa za'a sarayar masa da mummuna ɗari, kuma zasu zame masa tsari da kiyayewa da katanga da hani daga Shaiɗan da halakarwarsa da kuma rinjayensa a wannan yinin nasa har sai ya shiga yammaci ta hanyar faɗauwar rana, kuma wani ba zai zo da mafificin abinda ya zo dashi ba sai dai wanda ya aikata hakan kuma ya ƙari a kansa.