Hadeeth Cards
Da'wa cards that highlight great meanings from the noble prophetic hadiths in a simple style and attractive display that helps the Muslim to have a deeper understanding of his religion in an easy way






























Da'wa cards that highlight great meanings from the noble prophetic hadiths in a simple style and attractive display that helps the Muslim to have a deeper understanding of his religion in an easy way
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana ba da labarin cewa wanda ya sallaci Asuba, to, zai kasance cikin kiyayewar Allah da gadinsa da tsarinsa, kuma Zai yi kariya gareshi, kuma zai yi ɗauki gareshi. Sannan (Annabi) tsira da aminci su tabbata a gareshi ya yi gargaɗi game da warware wannan alƙawarin da ɓatashi, ko dai da barin sallar Asuba, ko da bijirowa mai sallatarta da ta'addanci a kansa, to, duk wanda ya aikata haka to haƙiƙa ya keta wannan tsarin, kuma ya cancanci narko mai tsanani na cewa Allah Zai nemeshi saboda abin da ya yi sakaci na haƙƙinsa, wanda kuwa Allah Ya nemeshi Zai kamashi, sannan Ya jefashi a wuta ta fuskarsa.
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana bayyana cewa sadaka ba ta rage dukiya, kai! tana tunkuɗe masa illoli, kuma Allah Yana musanyawa mai ita da alheri mai girma, sai ta zama ƙari ba ragi ba. Kuma afuwa tare da iko a kan ramuwa ko kama (mai laifin), ba sa karawa mai yinsu komai sai ƙarfi da buwaya. Kuma wani ba zai ƙanƙan da kai, ya ƙasƙanta ga Allah ba, ba don tsoron wani ba, ba don yaudara (na nuna tausayi) gareshi ba, ba don neman wani abin amfani daga wajensa ba, sai sakamkonsa ya zama ɗaukaka ne da sharafi.
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana bayanin mafi cikar imani a cikin mutane shi ne wanda ɗabi’unsa suka kyautata, ta hanyar sakin fuska, da bayar da abu mai kyau, da kyakkyawar magana, da barin cutarwa. Mafi alherin muminai shi ne mafi alherinsu ga iyalansa, kamar matarsa da ‘ya'yansa mata, da ‘yan’uwansa mata, da danginsa mata, domin su ne suka fi kowa haƙƙin a kyautata musu.
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana bayanin cewa ita duniya da abin da ke cikinta wani abu ne da za a ji dadi da shi, na wani lokaci sannan ya wuce, to, mafificin jin daɗinta shi ne mace ta gari, wacce idan ya kallaceta za ta faranta masa, idan kuma ya umarceta za ta yi masa biyayya, idan ba ya nan za ta tsare shi a kanta da kuma dukiyarsa.
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana ba da labarin Allah maɗaukakin sarki Ya ce: Ya kai Ɗan Adam ka ciyar cikin ciyarwar wajibi da ta Mustahabbi zan yalwata maka, zan kuma ba ka makwafin abin da ka bayar, kuma in sanya maka albarka.
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana bayyana cewa mafi cancantar sharaɗin da za a cika shi ne wanda ya kasance dalili na halatta jin daɗi da mace, su ne sharuɗɗan da suke na halal ga mace ta nema a lokacin ɗaurin aure.
Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance yana HAILALA bayan ya sallame daga kowacce sallah ta farilla da wannan zikirin mai girma, Ma’anarsa ita ce: "Babu abin bautawa sai Allah"; Wato babu abin bauta da gaskiya sai Allah. "Shi kaɗai yake ba shi da abokin tarayya": Wato babu wanda yake tarayya da Shi a Allantaka [ cancantar bauta ] ko a rububiyya [ kasancewarSa Mahalicci, Mai azurtawa, Mai rayawa, Mai matarwa ] ko kuma a sunaye da siffofinSa. "Mulki na sa ne": Wato; Shi Ya ke da cikakken mulki wanda ya game komai, mulkin sammai da ƙassai da abin da ke tsakaninsu. "Godiya ta sa ce": Wato shi ne wanda ya siffantu da cikakkiyar cika, wanda ake yabonSa da cika saboda so da girmawa a kowanne lokaci, na farin ciki da na damuwa. "Shi mai iko ne a kan komai": IkonSa cikakken iko ne ta kowacce fuska, babu abin da yake gagararsa, babu wani al’amari da zai gagare shi. "Ba dabara ba ƙarfi sai da yin Allah": Wato babu canji daga wani hali zuwa wani halin, ko daga saɓon Allah zuwa ga baiyayyarSa, haka babu ƙarfi, sai da Allah wanda Shi ne Mai taimako, kuma Wanda ake dogara da Shi. "Babu abin bauta da gaskiya sai Allah, ba ma bautawa kowa sai Shi": karfafawa ce a kan ma’anar Allantaka da kuma kore shirka, da cewa babu wanda ya cancanci bauta in ba Shi ba. "Ni’ima ta Sa ce da falala": Shi ne wanda ya halicci ni’imomi kuma yake mallakarsu, yake kuma ba da su ga wanda Ya so cikin bayinSa. "Kyakkyawan yabo nasa ne": A bisa zatinSa da siffofinSa da ayyukanSa da Ni’imominSa a kowanne lokaci. "Babu abin bautawa da cancanta sai Allah, muna masu tsantsanta addini a gareShi": Wato, muna masu Tauhidi, babu riya, kuma babu jiyarwa a kan biyayya ga Allah. "Koda kafirai sun ƙi": Wato muna masu tabbatuwa a kan Tauhidi da bauta masa ko da kafirai sun ƙi.
Annabi tsira da amincin Allah su tabba a gare shi, yana bayyana ayyuka na ƙwarai a goman farko na watan and Zul Hijja (Watan babbar Sallah) ya fi a kan sauran kwanakin shekara. Sahabbai Allah ya yarda da su, suka tambayi Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi dangane da Jihadi a kwanakin da ba waɗannan goman ba, shin shi ne ya fi ko kuwa ayyuka na ƙwarai a waɗannan kwanakin? saboda abin da suka sani na Jihadi yana cikin mafificin ayyuka. Sai Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya amsa da cewa kyawawan ayyuka a waɗannan kwanakin sun fi Jihadi a wasu kwanakin, sai dai mutumin da ya fita yana mai Jihadi da kutsawa hatsari da ransa da dukiyarsa; Don ɗaukaka addinin Allah sai ya rasa dukiyar ta sa kuma ran shi ya fita domin ɗaukaka addinin Allah. To wannan shi ne ya fi a kan aiki na ƙwarai a cikin waɗannan kwanaki masu falala.
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya tsawatar a kan jinkirta sallar La’asar daga lokacinta da gangan, kuma duk wanda ya yi hakan, to, aikinsa ya lalace, ya tafi kawai a watse.