





























Hadeeth Cards
Da'wa cards that highlight great meanings from the noble prophetic hadiths in a simple style and attractive display that helps the Muslim to have a deeper understanding of his religion in an easy way
All
Daga Anas -Allah ya yarda da shi ya ce: Manzon Allah SAW ya ce: "Haqiqa an tsorata ni a tafarkin Allah irin tsoratawar da ba'a yiwa kowa ba, kuma Haqiqa an cutar da ni irin cutarwar da ba'a yiwa kowa ba, Nayi kwana Talatin tsakanin Dare da Rana bani da Abincin abincin da zan ci ni da bilal sai Xan wani abu da zai kare cibiyar Bila"
Ibnu Majah ne ya Rawaito shi - Al-Tirmithi Ya Rawaito shi - Ahmad ne ya rawaito shiManzon Allah SAW ya faxa cewa a cewa shi kaxai ne a farkon bayyanar Addinin sai Kafirai suka bashi tsoro saboda hakan kuma suka cutar da shi, kuma babu wani tare da shi da zai kare masa cutarwar sai taimakon Allah da kariyarsa da kuma datarwarsa sannan yayi bayanin cewa duk da haka ga qarancin kuxi da Abinci da rashin tanadi, yadda zai kwana Talatin bashi da Abinci sai xan kaxan da Bilal zai iya voyeshi a qasan Hammatarsa, kuma ko tukunyar da zasu saka abincin babu, wannan shi ne lokacin da ya futa SAW yana mai guduwa daga Makka.
Daga Anas -Allah ya yarda da shi- Cewa Wata mata tana da wata damuwa a hankalinta, sai ta ce ya manzon Allah lallai ni ina da wata buqata a wajenka, sai ya ce: " Babar Wane, kalli ko wane hanyoyi kika so, har in biya miki bukatarki sai ya keve da ita a Hanya har ta gama gaya Masa buqatarta
Muslim ne ya rawaito shiCewa Wata mata tana da wata damuwa a hankalinta, sai ta ce ya manzon Allah lallai ni ina da wata buqata a wajenka, sai ya ce: " Babar Wane, kalli ko wane hanyoyi kika so, har in biya miki bukatarki sai ya keve da ita a Hanya har ta gama gaya Masa buqatarta, kuma wannan bai kasance cikin kevancewa da Muharrama ba, saboda Wannan akan hanya ne da Mutane suke wucewa kuma ana ganinsu, sai dai ba'a jin Maganarsu, kuma wannan yana nuna irin Tawaru'unsa da jin Qansa ga Al-ummarsa SAW
Daga Nana Aisha -Allah ya yarda da ita ta ce: "Bana kishin Mutuwar wani da Mutuwa da tafi bani tsoro da tsanani kamar Mutuwar Manzon Allah SAW"
Al-Tirmithi Ya Rawaito shiNana Aisha tana cewa: lallai cewa ita ba zatayi farin ciki da sauqin Mutuwar wani ba, kuma ba zata yi fatan ta zama mai sauqi ba, bayan abun da ta gani ga Manzon Allah SAW haqiqa tasan cewa tsananin Mutuwa ba ita ce take nuna Mummunan qarshe ga mamaci ba, kuma ba saqinta ba ne yake nuna Karama ba, kuma inda haka ne da Manzon Allah SAW ya kasance Mafi cancantar Mutane da shi, to don haka kada kuji tsoron tsananin Mutuwa, kuma kada kuyi farin cikin don wani ya Mutu ba tare da tsanani ba.
An rawaito daga Nana Aisha -Allah ya yarda da ita- ta ce: "Yayin da Annabi SAW ya rasu sai suka ce: a ina za'a Binne shi? sai Abiubakar ya ce: a wurin da ya ra su a cikinsa"
Ibnu Sa'ad ne ya Rawaito shi - Al-Tirmithi Ya Rawaito shiyayin da Manzon Allah SAW yayi wafati Sahabbai sunyi savanin wurin da za'a binne shi a cikinsa, sai Abubakar ya ce: ku binne shi a wurin da ya rasu a cikinsa, a cikin wasu Riwayoyi: cewa Abubakar ya ji Manzon Allah SAW yana cewa: Babu wani Annabi daga cikin Annabawa sai a Mahallin da yake son a binneshi a cikinsa
Daga Nana Aisha -Allah ya yarda da ita- ce: "Cewa Abubakar ya shiga ga Annabi SAW bayan Wafatinsa, sai ya sanya bakinsa akan Idanunsa, ya sanya Hannayensa akan Mukamukinsa, kuma ya ce: "Ya Annabi, ya Badadi, ya zababbe"
Ahmad ne ya rawaito shiAbubakar ya shiga Wajen Manzon Allah SAW bayan Wafatinsa, sai ya sanya bakinsa a tsakanin Idanuwan Manzon ALlah SAW sai ya Sunbanceshi, kuma ya sanya Hannayensa a kan Muqamiqan Manzon ALlah SAW, su ne gefen Fuska daga Ido zuwa Kunne, kuma ya ce: "Muna rashin Annabinsa, Muna Rashin Masoyinsa, Muna rashin Zavavvensa" ai cewa shi ya kasance -Allah ya yarda da shi- yana jin ciwon Mutuwar Manzon Allah SAW kuma yana siffanta shi da cewa shi ya kasance yana fifitashi kan komai har kansa, kuma wannan shi ake kira Alhini, kuma idan bai kasance a cikinsa akwai futo na futo da Musiba da kuma raki ba, kuma idan ba'a xaga Murya ba, Kamar yadda Mata suke yi da Ihu da Kururuwa, to Wacan ya Halatta, Kuma shi ne abunda Abubakar yayi -Allah ya yarda da shi
Daga Anas Bin Malik -Allah ya yarda da shi- ta ce: "Yayin da Manzon Allah SAW ya shiga Madina a cikinta kowane abu ya haskaka, kuma Ranar da ya rasu a cikinta kowane abu a cikinta yayi duhu, kuma bamu watsa kasa kan Kabarin Manzon Allah SAW da Hannayenmu, kuma Mu wajen rufeshi har sai da muka tsani Zukatanmu"
Ibnu Majah ne ya Rawaito shi - Al-Tirmithi Ya Rawaito shi - Ahmad ne ya rawaito shiAnas Bin Malik yana bada Labari daga Manzon Allah SAW cewa shi yayin da ya shiga Madina Farkon Hijirasa daga Makka, komai ya haskaka, yayinda da kuma ya yi wafati komai yayi duhu kuma Duhun da Hasken da aka faxa a wannan Hadisin ana nufin na Ma'ana bana Zahiri ba, sannan ya ya bada labarin cewa yayin suka gama binneshi basu samu zukatansu kamar yadda suke ba a baya a lokacin Manzon Allah SAW yana raye, na hasken Imani da Tausayi da Haxin kai a tsakaninsu saboda yankewar Wahayi, da rashin Albarkar Zama da shi SAW.
An rawaito daga Nana Aisha -Allah ya yarda fa ita- ta ce: "Manzon Allah SAW bai bar Dinare da Dirhami ba ko Akuya ko Raqumi kuma bai yi Wasiyya da komai ba"
Muslim ne ya rawaito shiNana Aisha -Allah ya yarda da ita- tana bada labarin cewa Manzon ALlah SAW bai bar komai ba bayan Mutuwarsa kaxan ne ko mai yawa, kuma bai bar Akuya ba, ko kuma Raquma ko wanin hakan na dangogin Dukiya, Kuma bai yi wasiyya da wani abu ba, tana nufin Wasiyyar Kuxi na Musamman; Saboda Mutum yana iya yin Wasiyya ne idan za'a gajr shi, kuma shi SAW bai bar komai na Gadon ba da za'a gada ballantana yayi wasiyya a cikinsa, Kuma Haqiqa Manzon Allah SAW yayi wasiyya da wasu abubuwan daban, daga cikinsu akwai kula da Sallah, da kuma futar da Yahudawa da nasara daga Jazirar Larabawa
An rawaito daga Nana Aisha -Allah ya yarda da ita- ta ce: Manzon Allah SAw ya kasance yana cewa a halin yana cikin lafiyarsa: "Lallai ba'a karvar ran wani Annabi face sai an nuna masa Masaukinsa a Al-janna, sannan a bashi zavi" to yayin da Mutuwa ta sauka gare shi, Kansa yana kan cinyata sai ya suma, sannan ya farka sai idonsa ya kafe yana kallon rufin xakin, sannan ya ce: "Ya Ubangiji kusanci Mafi xaukaka"
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiNana Aisha -Allah ya yarda da ita- tana cewa: Manzon Allah ya kasance a lokacin yanada lafiya yana cewa kafin yayi rashin lafiyar Mutuwarsa: cewa babu wani Annabi da zai Mutu daga cikin Annabawa har sai Allah ya nuna masa Mahallinsa a Aljanna, sannan ya bashi zavin zama a Duniya ko kuma ya xaukeshi zuwa Masaukinsa a Aljanna, Aisha ta ce: yayin da manzon Allah SAW yayi rashin lafiyar Mutuwarsa, kansa yana kan cinya ta, sai ya suma sannan ya farka, sai ya xaga kansa zuwa rufin xakin sannan ya ce: "Ya Ubangiji zuwa Makwabtaka Maxaukakiya" ai ya zavi kusanci su ne Jama'ar Annabawa waxanda suke zaune a sama sama, Nana Aisha ta ce idan Allah ya bashi zavin tsakanin Duniya da Lahira to shi zai zavi Lahira ne, ba zai zave mu ba, kuma nasan cewa wannan zavin shi ne zancen da yake gaya mana lokacin yana lafiya, Aisha ta ce: Qarshen kalmar da ya faxa SAW ita ce: "Ya Ubangiji zuwa Makwabtaka Maxaukakiya"
Daga urwa Bn Zubair ya ce: "Na tambayi Abdullahi Bin Amr game da mafi tsananin abunda Mushirikai ga Manzon Allah SAW sai ya ce: Naga Uqubuta Bin Abi Muaix Manzon Allah SAW kuma yana Sallah, sai ya sanya Mayafinsa a wuyansa sai ya shaqeshi shaqa mai tsanani, sai Abubakar ya zo har ya ture shi, sai ya ce: "Yanzu zaku kashe Mutum don yace Allah ne Ubangijinsa, kuma bayan ya zo muku da Ayoyi Mabayyana daga Ubangijinku" { Ghafir: 28)
Buhari ne ya rawaito shiUrwa Bn Zubair ya ce: "Na tambayi Abdullahi Bin Amr game da mafi tsananin abunda Mushirikai ga Manzon Allah SAW sai ya ce: Naga Uqubuta Bin Abi Muaix Manzon Allah SAW kuma yana Sallah, sai ya sanya Mayafinsa a wuyansa sai ya shaqeshi shaqa mai tsanani, sai Abubakar ya zo har ya ture shi, sai ya ce: "Yanzu zaku kashe Mutum don yace Allah ne Ubangijinsa, kuma bayan ya zo muku da Ayoyi Mabayyana daga Ubangijinku" {Ghafir: 28) wannan ita ce shaidar mafi munin Abunda Abdullahi ya gani -Allah ya yarda da shi- kuma Urwa ya tsaya kan wannan shi ne ma tsananin abunda ya gani tunda Urwa ya bada labarin cewa Nana Aisha -Allah ya yarda da ita ta bashi labarin sa cewa ta ce da Manzon Allah SAW shi ka tava samun wata rana mafi tsanani a gareka kamar ranar Uhud? sai ya ce: "Na gamu abunda na gamu da shi daga Mutanenki kuma mafi tsananinsu ya kasance a ranar Aqaba lokacin da na gabatar da kaina ga Ibn Abd ya lail Bn Abd Kulal, bai amsa mun ba abunda na so, sai na tafi ina cikin vacin rai a fuskata, ban farka ba sai ina Qarn tha'alib sai na xaga kaina, sai ga girgije ya lulluveni, sai na duba sai Jibril a cikinsa, sai ya irani sai ya ce Allah yaji Maganar Mutanenka gareka, kuma da abunda suka mayar maka, haqiqa ya aiko Maka Mala'ika Duwatsu ka umarceshi da abunda ka so akan su, sai Mala'ikan Duwatsu ya kirani yayi mun Sallam sannan ya ce: ya Muhammad sai ya ce: Wancan sai abunda kaso in kaso in jeho shi akansu ? sai Manzon Allah SAW ya ce: aa ina son son a samu waxanda zasu futo daga ysatsonsu wanda zai bautawa shi kaxai, baya masa Shirka da komai" Buhari da Muslim suka rawaito shi